*ANCUCI🤦🏼♀HIJJABI*
*TRUE LIFE STORY*
✏ _Writen by_
*fayeeeeex m usman*
💦💦 *Talented writers forum* 💦💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
_To get access to talented novels check_
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💙❤💚 *sanku in ance dani na saida yai tsad~a danko yai girma har yai yabanya yai hud~a* _yasan muhallins~a tamkarruwa acikin rand~a ashe_ *batun ciniki akansa wannanm~a zancan shirmene* ❤💙💚 _saiku masoyana ana mugun tare🤝_
*Kuyi hqr da mistk dazakuga inayi*
*pg1⃣2⃣*
_azaune take abakin katafaren mirow wanda d'auke yake da nau'in kayan kwalliya da turarurruka iri daban daban ya cika yayi maqil samanshi da cikin duruwowinshi,wata budurwa na hango tsaleliya mai kyan gaske wacce idan ba hausa tai makaba to ba shakka zaka iya rantsewa da alqur'ani ba bahaushi yabace domin wani ma kyan wllhy saika matso kusa da ita, farace tar kamar jinsin balarabiya ga wani dogon hanci da maisama ya bata kamar wata ba indiya doguwace mai tsukakken jiki ga wani ido da Allah yabata kamar mage gasu farare tar,daga wanka ta fito na yacce naganta d'aure cikin towel,sai faman goga wancan take tana shafa waccan kamar wacce zata sauyawa kanta halitta na yacce naga tazage sai durje fatarta take da nau'in sosunan pawder kala_ _kala,fuskarnan tata d'auke da fara'a rantama fayau,jinai anbud'e qofar d'akin nata ,wanda yasa nai saurin juyawa dan ganin waya shigo,sai aloqacin na tabbatar d'akin tane,danni nazata a Hotel take na yacce d'akin ya gaji wurin had'uwa kamar a Dubai,wata tadtijuwace wacce ba zatawuce shekara arba'inba da wani abu,sanye take cikin wani tsalelan boyal less,lite pink ne taci kwalliya kamar wata budurwa tana kama da budurwar dake cikin d'akin,Murmushi naga Hassina ta sakarwa mom d'in tata,itama shi ta sakarmata afili kuma tace,"my daugther har yanzu baki gama shirya wabane?.baki ta d'an cono kafin tace,"Mom nagama shiryawa kaya kad'ai zansa,saidai tun d'azu ina ta_ _trying d'in non big bros anma ban sameshiba.taqarashe maganarne kamar zata fashe da kuka,kusa da ita taqarasa tare da rungumota kafin tace,"rabu dashi my daugther kinsan halinshi meby so yake yace bazai bimu villege d'inba...."nikuma mom banga laifiba kan mutum yaje mahaifarshiba idanma baije ba yanzu aewataran dolenshi yaje,idan na mai mgn wai saiya runga cewa aeshi ba acan akahaifeshi ba wai abirni akahaifeshi.dariya ceta su66u cewa Mom ta na yacce Hassina take mgn cike da shagwa6a,"to inban da abin Son ae acan akahaifi Dadynshi dan haka dole yaje komai dad'ewa,yanzu kedai kisauri kishirya kar ran dadynku ya6aci kinji..."ok Mom...ficewa Mom tai daga d'akin tanufi_ _kichin inda ta tarar da Hajjo mai aeki tana zuba abinci a place cike da kulawa Mom tace,"Hajjo kenan bakya gajiya da aeki ko?.tafid'i mgnarne tana sakar mata murmushi cike da girmamawa Hajjo tace,"Allah sarki Hjy bakya gajiya dawasa ae dole nayi aeki sabo dashine aekina agidannan kinga ni dafa abincinnan da kikema wllhy dan ba yacce zanyi dakene da sauran aeyukan da kike.dry Mom tayi kafin tace,"Hajjo kenan karfa kimanta nan gidan_ _miji nane d'auke fa spoon idan nayi allah lada zaibani kinga ko aebabban kuskurene inzauna ince sai wanine zaimun kuma aeni tuni na d'aukeki y'ar uwa dan haka dan allah ki daina wahalar dakanki da yawan aeki agidannan..."allah sarki allah yabaki abun da kike naima Hjy duniya da lahira wllhy samun mace kamarki azamanin yanzu abune mai wuya kina d'aya daga cikin mutanan da dukiya bata_ _rud'arsu tasa sushagala harma wani loqacin sumanta da mutuwa.murmushi Mom tayi loqacin da take da takar6i aekin da Hajjo take tana murmushi kafin tace,"kai Hajjo kedai kullum acikin fasamin kai kike ko.ja dabaya Hajjo tai tabar mata aekin dan tasan indai mom tashigo Kiching to saidai tabarmata aekin,azuciyarta kuma tana mamakin kyaun halin Hjy Nafisat da d'abi'unta baruwanta da girman kai mutumce wacce tasan daraja da kima na y'an Adam bataruwanta da girman kai balle wulaqanci gata da girmama nagaba da ita koda koshine shugaban y'an talauci..._
_saifaman zarya yake yana kiran nombar Hydar fuskar nan tashi sam babu walwala,mom wacce ke zaune akan d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun palaun itama sai faman kiran nombarshi take amma gaba d'aya nombobin sa arufe,Hassina ma wacce ke zaune aqasa agefan mom itama sai nemanshi take ayanar gizo~gizo kamar_ *whatsApp Imo Facebook* _da sauransu amma duka baya online cikin 6acin rai Alhaji Yusuf yace,"ni Hydar zamaida mutumin banza agabanshi fa jiya nakira d'an uwana nace zan kawosu dan sugaisa amma shine zairufe wayarshi.yai maganarne asanda yake jan wata qwafa,Hassina wacce gaba d'aya ranta itama ya 6aci,"Dady kayi hqr ina tunanin inda yake ne babu network..."yimun shiru bana san rainin hankali bayasan da tafiyar tamuba amma yai tafiyarshi,kawai kutashi mutafi.jiki asa6ule Hassina ta nufi d'akin Hajjo inda ta ganta akan sujjada da alama sallar_ _Walaha ta'idar durqusuwa tai cike da girmamawa ta gaishe da'ita ta amsamata cike da kulawa,"nasan Mom tafad'amiki zamu qauye ko?..."eh tafad'a mun d'azuma take cemun nashirya kinga yanzuma nake qoqarin fitowa.rausayar dakai Hassina tayi kafin tace,"wllhy ya Hydar ne bazai samu damar zuwaba shine nace ko zaki zauna agida kinga idan muka tafi bamai dafamai abinci ba mai kula dashi shine nace dan allah ko...Hajjo ce taisaurin katseta tahanyar cewa,"haba Hasana maye kuma na roqona ae wajibinane nazauna bamatsala allah yadawo daku lpyh.wani murmushin jindad'i Hassina tai_ _. da rungume Hajjo inda yai daidai dashigowar mom murmushi tai nayacce taga tarungume Hajjo Sam Hassina bata da girman kai itama kamar iyayanta ta biyo su sak dan baruwanta da d'aga kai,wannan dai gaba d'aya ogan uban gaiyar aka laftawa dan girmankai awurin Hydar har mgn yake,dan wannan suna tun yana prmry akasamushi kuma ya bishi,"bazaku fito bane karfa mu makara.mom ce tafad'i haka asanda ta bud'e qofar d'akin,dasauri Hassina ta miqe tana cewa,"daman mom cewa nai Mama Hajjo ta zauna kinga ya Hydar yana gida idan muka tafi bashi da mai dafamai abin...tsawar da mom tai matane yasata yin shiru"banasan zancan banza wannan mara mutuncinne zaici abincin Hajjo dama dai wani ba bashiba.taqarashe mgnarne sanda tamai da ganinta kan Hajjo,"kitashi mutafi ya dunga zuwa Restaurant ae yafi gane haka wani loqacin..."aa Hjyh baza ae hakaba daman wllhu banajin dad'in jikina kawai kutafi mahad'u wani_ _jiqon..."kamarya baki da lfyh kawai dai kice zaki biyewa wannan shasha shar..."aa wllhy hjy bahaka bane kawai dai allah yadawomin daku lafiya..."ae hankalinki ya kwanta zaki iya fitowa mutafi ko...momce tafad'i haka tana zabgawa Hassina harara tare da barin d'akin,waigawa Hassina tai inda suka had'a ido da Hajjo murmushi tasakar mata tare dacewa,"Ilove you Ma Hajjo qaunarki a jinina take.tana fad'in haka tasakai tafice daga d'akin tana dry itama Hajjon murmushi take,farfajiyar gidan ta nufa tana gudu tana dry anan taci karo dasu mom suna qoqarin shiga mota,kallo Dady yabi y'ar tashi dashi na yacce tai shiga inda sabo yaci ace yasaba cike da haushi yace,"kiyi qoqari kiyana gyalan koda akan kafad'arki ne kinji.sai aloqacin tai saurin kallon shigar datai doguwar rigace material ta kamata ga shegen ta kalmin da tasa mai d'an karan tsini da sauri ta yafa gyalen da taruqo ahannu,tashiga gidan baya dan yau dady dakanshi zaija motar,anan baba Garba mao gadi yawage musu katafaran get d'in suka fita yana musu addu'ar allah yasauqesu lpyh,sai da suka tsaya a babbar Market alhaji Yusuf ya tsaya inda yaiwa su Khadijat dasu Ammi da Baba siyayya kamar zatai mgn sannan suka d'au hanya_
*****************************
_su Ammi ma yau gida ya kacame dan yau ana da manyan baqi,Alhaji Ibarahim dakanshi yaje kasuwar Mata inda yasuyo kaji kusan guda bakwai da naman Rago gskyh anhad'a_ musu tarba ta alfarma,su _Khadijat ko yau ko makarantar islamiyya basujeba dan boko daman Anba da hutu basujeba,Ummi wacce ke tafaman wanke wanke Ammi da Khadijat kuma suna gyara kajin da Abba yasuyo Baba kuma na yanka kayan miya,Abba ne yashigo da wata baqar leda Ammi ya miqawa tare da_ _cewa,"gashi ki ajiyemun kud'innan Malam Rabi'u ne yaban ajiya zuwa gobe zai kar6a dubu d'ari da hamsin ne dan allah kimusu ajiya me kyau kinji.kar6a tai tana murmushi,hannu yazura a aljihu ya qirgo wasu kud'in yabata ga wannan kud'in ki had'a duk ki ajemun,hannu tasa ta kar6a tare dacewa,"sufa nawane?..."dubu ishirin da biyarne..." to shikenan...d'aki tashiga dan adanasu kafin tafito suka ci gaba da aeki suna fira,Ummi ko nagama aekinta tamiqe ta sulale tanufi gidan su Amina qawarta..._
_kubiyoni_
✍🏼✍🏼✍🏼 *fayeeeeex m usman*
Comments
Post a Comment