*💦Talented writers forum💦*
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkarda dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
To get access to talented novels check
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💐💐💐💐💐?
💐💐💐💐
💐💐💐
*ZAMAN AMANA KO CIN AMANA*
*Story & Written By📚✍*
*Maryam Lawal Wada*
Page 81---85
*Wannan shafin naki ne maman Mufeeda na gode da nuna kulawarki agareni ina k'aunarki har cikin raina Allah yaraya mana baby mufeeda bisa tafarkin shiriya rabbi ya jib'anci lamuranki ya inganta maku lafiya ana june irin baza,arabu ba🤝*
Salma tacigaba tace "maryam haka rayuwar mu tacigaba da tafiya, cikin tattali da k'aunar junnah" ranar wata juma,a da yamma muna falo nida imran ina kwance ajikinshi kamar yadda nasaba, saboda gaba d'aya jikina babu kwari.
Nace a hankali cikin murya mai dad'in sauraro "dear ya kamata ka koma wajen aiki tunda jikana yayi sauk'i sosai"
Imran yayi murmushi yace "salma nayi tunani haka sai dai kinsan miye" na gilgiza kai nace "a,a" imran yace "Salma banaso in tafi inbarki cikin damuwa" nace "karkadamu dear na warkefa".
Imran yace "kin tabbata har cikin zuciyarki haka ne" nayi murmushi nace "yes" imran yace "pls Salma ki kular mani da kanki da babynah idan wani abu yasameku bazan tab'a yafema kainaba, kinji dear" nace "inshaa Allah" imran yace "zuwa lahadi zan tafi abuja" nace Allah ya kaimu.
Salma tace " maryam da haka mukaita hira har aka kira sallar magariba tare muka tashi muka nufi bed room muka shiga toilet mukuyi alwala shi ya tafi massalaci nikuma na tada sallah, bayan nagama nayi addu,o,i.
Salma tace "maryam take hawaye ya cigaba dabi mani fuska 😭 kiran sallar isha,i danaji shi ya tadani domin gabatar da sallah dama imran baya dawowa in ya tafi sallah magriba har sai yayi isha,i bayan nagama na haye gado nayi kwanciyata, bani so imran yagane nayi kuka.
Lokacin da imran yadawo bacci har yayi gaba dani haka ya zauna ya dunga mamatsa mani k'afafuwana kullum haka yakeyi mani da yake k'afafun ciwo sukeyi mani, imran yace "sanu dear baby yana baki wahala Allah yabaki lafiya yasa ki haiho mana babyn mu cikin k'oshi lafiya" ya rungumuni jikinshi ya subaceni, da haka bacci yayi gaba dashi.
Kiran sallar asuba da imran yaji shi yatada shi daga baccin da yakeyi, alwala yayo ya gabatar da raka,atanil fijir yana zaune yana addu,o,i har akayi kiran assalatu da zai tafi massalaci ya tadani yace " dear ki tashi kiyi sallah".
Murmushi nayi mashi nace "to" haka na tashi nayo alwala nazo nagabatar da sallah daga nan bacci ya k'ara gaba dani ko tashi banyiba, daga inda nayi sallah.
Imran da yadawo daga massalaci ya d'aukan, yayi saman gado dani ya shiga gyaran gida da yake tunda ya dawo shi yake komi k'arfe 9:00 am imran ya tadani yace dear "kitashi ki d'anci wani abu baby yunwa yakeji" murmushi nayi na juya na gyara kwanciyata, da sauri imran ya rungumoni yace "pls dear mama takawo maki wainar filawa" da sauri na bud'e idona alamar dagaske imran yace "yes".
Da sauri na tashi imran ya ruk'oni yace " yi ahankali dear babyn mu" murmushi nayi na fad'a toilet lokacin dana shiga na iske komi na jirana, imran ya had'a mani hada ruwan wanka, nan ma bansan lokacin dana fara kukaba 😭 nace "ya Allah kaine gatan bawa ka fitar dani daga bala,in danake ciki haka nayi wanka jikina babu kuzari nayi burosh nafito ban iske imran ba hakan yabani dama saurin shirya.
Salma tace "maryam bawata kwaliya nayiba powder nashafa sai man Baki dana murza nasaka green d'in less dogowar nayi kyau sai dai ramar danayi tayi yawa, gaba d'aya hankali yana wajen wainar filawar da zanci shi yasa nayi komi a tak'aitacen lokaci falo nayo da sauri wanda hakan yayi dai-dai da fitowar imran daga bed room d'inshi.
Imaran ya bud'e mani hannushi alamar inzo gareshi kafad'a na mak'e na kali kular waina yace "haba Salma kizo gareni" take tausayinshi ya kamani nayi wajen mijina ya sanyani a fafad'an k'ijinshi ya rungumeni yace "(tabarakallahu ahassanul kalik'in) dear kullum sai kyau kike k'arawa kinga yadda ki kayi kyau" nace nadoge kaima kayi kyau".
Imran yace "tnx dear sai dai kin fini kyau" murmushi nayi ni dai fatana ya sakeni inci waina imran da kanshi ya zauna ya bud'e kular waina ya bud'e mani robar tashi yace "dear bissimillah amma banda shan tashi" aikuwa ba bata lokaci na dunga cin waina inajin nice d'inta kafin wani d'an lokaci naci rabin kula imran ya tsiyaya mani ruwa nasha nace "alhamdulillah" imran yace "kin k'oshi" nace "eh sai zuwa anjima".
Imran yace "dear tunda kin gama d'ako hijab d'inki muje muyi sayayyar kayan amfanin gida, daga chan muje ki gaida mom da mama" maryam take farin ciki ya ziyarceni rabona da fita tun kafin in fara rashi lafiya a tunanina idan na fita zan rage zafi da rad'ad'in da zuciyata keyi 'yar uwa ashe abun ba haka yakeba na rungume imran nace "tnx dear".
Shi kanshi imran yasan fitar tasani jin dad'i yadda yaga fuskata cikin happy da sauri na mik'e imran ya rik'o hannuna yace "pls salma nagaya maki bani son gudun nan da kikeyi" nace "I'm sorry dear na daina" haka imran ya ruk'e mani hannuna har bed room d'ina, da kanshi ya d'auko hijabi yasaka mani.
Muka shiga d'akinshi ya d'auko key d'in mota har lokacin hannunshi rik'e danawa a haka duk yarufe mana k'ofofi muka nufi wajen mota ya zagaya ya bud'e mani nashiga ya rufe shima ya zagaya ya shiga yayima mota key mukabar gida.
sha,aban super market imran ya nufa ya gyara parking yace "dear zaki shiga?" kai kawai na gilgiza alamar a,a a lokacin har nafara jin bacci, imran ya shiga yajibgo mana kayan amfanin gida bai wani dadeba ya fito ya bud'e but a kacigaba da zuba mana kaya k'arar rufe marfin motar shi ya tadani daga baccin danake.
Imran yace "I'm sorry dear bacci ko? mu koma gida ki kwanta idan kin tashi sai muje" nace "nagama baccin mutafi" haka muka tafi ba dan ranshi yasoba.
A k'ofar gidan mu imran ya gyara parking nan ma da sauri na yunk'ura zan tashi imran ya ruk'o hannuna sai a lokacin na tunah nace "dear afuwan"👏🏻 yayi murmushi tare muka shiga har falon mom "maryam in bazaki mantaba, keki ka rugo ki ka rungumeni dai-dai nan mom tafito daga kicin tace "maryam bakiga 'yar uwartaki ba lafiya garetaba, mom tace "imran sununku da zuwa" imran yace "yawa mom ina wuni" bayan duk an gaisa mom tace "salma ya jikin".
Nace "mom jiki yayi sauk'i sai dai rashin k'arfin jiki" mom tace dama sai a hankali Allah ya saukeki lafiya" imran ya amsa da ameen, daga nan yayi mana ban kwana yace "dear k'arfe 4:00 zan dawo" nace "to Allah ya tsare".
Bed room d'in mom nashiga tare da sallama mom tayi mani izinin shiga na zauna gefen gado mom tace " salma ina imran d'in?" nace "ya tafi sai anjima zai dawo" mom tace " yaron kirki salma Allah yayima rayuwarku albarka salma kirik'e mijinki amana kada ki cutar da mijinki kanji" kai kad'ai na,iya dagawa saboda kukan 😭da yazo mani a hankali na kali agogo naga k'arfe d'aya na tashi na d'oro alwala na gabatar da sallah azahar daga nan bacci yayi gaba dani "Maryam gaba d'aya sai da nazama kamar mai ciwon bacci".
K'arfe 3:30 mom ta tadani in shirya na gabatar da sallah sana na gyara jikina mom ta kawo mani d'an wake da mai da yaji nai murna naci na k'oshi mom ta k'ara yi mani nasiha mai ratsa jiki, nace "mom dady baishigoba?" mom tace "ya shigo kina bacci yace kada a tadaki kiyi fama da ciwon kai zaizo har gida ku gaisa.
Da haka imran ya dawo mukayi ban kwana muka d'auki hanyar gidan mama chan mukasha fira sai dare muka tafi da muka fito, imran yace "mama namanta gobe inshaa Allah zan tafi wajen aiki" mama tace "Allah yayarda Allah ya tsare ya taimake ku aduk abunda ku kasa agaba" imran yace "ameen ya rabbi".
A gajiye muka koma gida na yi kwanciyata imran yacigaba da had'a kaya sai da yagama sanan yayi kwanciyarshi yau ma kamar kullum ya tashi yayi duk abunda yasaba gabatarwa, ya shirya ya tabbatar na cika cikina da misalin k'arfe 10:am yace "dear nafito zan tafi ga amanar babynah ki kular mani da ita" nace "to" nayi mashi rakiya ina daga ✋🏻mashi hannu ina hawaye nace "Allah ya tsare ya saukeka lafiya" imran yace "ameen ya rabbi" ya shiga mota yayi mata key yabar gidan.
Da gudu na tafi bed room d'ina na haye gado nasha kuka sai da naji kukan babu dad'i sana na hak'ura daga nan bacci yayi gaba dani kiran sallah azahar ya tasheni bayan na gabatar da sallah na duba wayata naga message d'in imran sun kai goma nayi mashi reply.
K'wan-k'wasa k'ofa naji a zatonama fahat ne, ina bud'e k'ofa naga nazir nace "a,uzubillahi mina shaid'ani rajim" na maida k'ofa zan rife, nazir yace "pls salma ki sauraran" nace "nazir mizan saurara daga gareka bayan ka cutar dani nazir kasani Allah bazai barkaba, kuka 😭 ya kwacema salma itama maryam kukan take.
Shi kuwa imran abun ya zarce tunanin mai karatu.
*Kucigaba da kasancewa tare L Wada*
I love you all 🙋🏻💝🙋🏻
Comments
Post a Comment