Skip to main content

Feenert

💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
             { ~*Diyar sarki ce*~}

   *Talented  writers forum*
 
      *(T. W. F)*

      *By*
 
*pherteenjeey*

  *Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*


            
              06

    Tunda garin Allah ya waye feenert take kuka, inna tayi lallashi har ta gaji, da kyar aka samu tayi shiru, sannan ta tashi ta fara hada kayanta.

  qarfe daya dot ta gama komai sannan ta dauki Ghana most go dinta da akwatin qarfen ta wanda malam ya siyo mata ta fito dasu waje domin qarfe daya da rabi zasu tafi, fitowar ta keda wuya ta ga inna tana ta kuka, ai batasan lokacin da ta jefar a akwatin ba taje ta rungume inna suna ta kuka, nima kaina sai da na tayasu kuka saboda tausayin da suka bani.

    Larai, baba, lami, mejidda ne suka fito tsakar gida domin jin kukan da yake tashi.

Baba ce tace gwara ki daina kuka dan bakima farayi ba, sai randa kika dawo gidannan na koraki domin nemo iyayen ki, shegiya kawai wanda bata da iyaye, larai ce ta amshe da yo ke baba ai itama karuwan cin zata tafi, kin taba ganin an tura yarinya birni wai da zummar yin  karatu ? ina fa larai saura kema idan kinyo cikin shegen kika Haifa saura ki jefar  kamar karuwar  uwarki, duk maganar da sukeyi babu wanda feenert ta gane a ciki gabaki daya Kanta yayi mata nauyi,  yanxu waye zai Amsa mata wadannan tambayoyin wanda baba da mama larai suke yi mata.

Tabbas inna da baba ne kawai suke da amsoshin wadannan tambayoyin nata, ita dai batasan wasu iyayen ba bayan inna da baba tabbas su zan tambaya, duk a zuciya take magana.

Durkushewa tayi a qasa tana zubarda hawaye masu zafi, Dan Allah inna ina son na tambayeku amma inason kimin alqawarin cewa zaki fadamin gaskiyar abinda yake faruwa, Ehh insha Allah zan fada miki gaskiya mamana,  innata shin kune iyayena ko ba ku bane ba?

Ras gaban inna ya fadi, data sani bata yiwa diyarta ta alqawari ba amma ya za'ai dole ta fada mata gaskiyar abinda ya faru. duk a zuciya take magana batare da kowa ya sani ba.

Malam ne ya shigo gidan da sallamar shi, domin kawowa feenert tsarabar da malam habu ya bayar a kawo mata, durqushe ya ganta a qasa tanata sharbar kuka hadda majina, qarasowa yayi da sassarfar sa, shikenan malam yau larai da baba Sunsa yau dole sai mun tone abinda muka binne tsawon shekara goma sha biyar baya, inna ce take magana tana qarasowa inda yake fuskar nan tasha kuka.

Meya farune ku fadamin mana, kwashe labari tayi kaf ta fada masa kuma hadda alqawarin da tayiwa feenert na fada mata gaskiya.

zubewa yayi a qasa alamun ya suma,  da sauri feenert da inna sukai kansa, innace take cewa feenert maza debo ruwa a zuba masa.

Da sauri kuwa ta debo ruwa ta kawowa inna, da sauri ta watsa masa a fuska, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke wani zafafan hawaye ne sukebin fuskar malam iro rufe ido yayi yace da inna wallahi yau hakuri na ya qare a gidannan yau sai ran wanda ya batawa yarinyar nan rai ya baci, agidannan.

Lami kije na sakeki Saki biu sannan ki tafi da wadannan yaran naki wanda kika batawa tarbiyyar gidanku, sannan baba duk abinda yake faruwa a gidannan nasan kece kike kullawa wata qwallace take fitowa a idanun sa.

wata uwar ihu ta qwalla tace wallahi zulai baki isa ki kwacemin iro a hannuna ba kinyi kadan shegiya,  gayyar matsiya ta.

*Tohh faaa anan ake yinta shin larai tana barin gidannan kuwa? Sannan feenert tana tafiya birni karatu kuwa? Shin idan taje birni tana samun iyayen ta kuwa?*

*Duk amsoshin tambayar nan sai kun biyoni zakuji cigaban labarin FEENERT*














fatimaauwal1999@gmail.com

Pherteenjeey✍🏻

Kuyi hakuri da typing kadan wallahi na gajine shiyasa luv u my fans😘

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...