Skip to main content

Zummunci

💦 *Talented writers forum*  💦


*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*

_domin samun littattafan mu shiga....

_To get access to talented novels check_

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na _Sunhera_

*dedicated to* _*Reefat yahya*_

*Wannan shafin naki ne my swt anty queenmermue u r so special I lyk evrtin abt u😘😘😘*

  *gaisuwa gareku Action baby, Mareeya Baba , Zainab idris makawa n baby Faty Afreen love u all ana tare sosai sosai*❤😘🤝🏻

*51&52*

A falo ya sameta kwance tana kallon wani American film zama yayi dab da ita yana mata wani irin kallo nan gabanta ya hau faduwa amma ta share ta cigaba da kallo haka suka xauna shiru , abinci ya d'auka yana ci a hankali har ya gama  sannan ya fitar da phn nasa ya kira ummansa suka gaisa inda ya mikawa Afreen ma sukayi magana daga karshe ya katse kiran bayan sunyi sallama.
      Shiru ne ya zuyarci falon gaba daya sun maida hankalin su gun kallon film d'in har wajen 11:30 Afreen ta fara hamma kamar jira yake yace " bacci koh, oya muje Ki kwanta" hararinsa tayi a cikin zuci kuwa cewa tayi da can kai kake sani baccin ne. Murmushi yayi yace " hararata kike koh" kwafa yayi nan batayi aune ne ya d'aga ta cak ! Ya wuce bedroom da ita. Bisa gado ya shimfideta nan ya shiga bayi brush yayi ya fito tana kwance inda ya barta , a hankali ya rike mata hannu ya fara murzawa yana wasa da yatsun ta tare da jefa mata wani shu'umin kallo yace " kin shirya? " cikin gatse tace " na me fah? " murmushi yayi yace " OK bari na nuna miki" aikuwa nan take ya fara aiko mata da sakonnin kiss gaba daya ya kashe mata jiki bata taba shiga irin wannan yanayi bah tunda take a rayuwar ta . Shuraim kam jikinsa sai rawa yake dag nan labarin ya fara canzawa Sunhera ta kashe musu wuta tare da Ja musu kofa domin Reefat ta hanata bin kwakwafi..lol

A takaice de a wannan dare Shuraim ya bareta cikin leda budurwa carr da ita godiya ya dinga xuba mata tare da jero mata aduoi iri iri , da safe ita ta shirya kanta idanunta a kumbure don tsabar kuka Shuraim kuwa sai lallaba ta yake. daga wannan rana Afreen ta fara samun wani irin kulawa ta musamman a gun angon nata sai riritata yake ya shagwaba ta gaskiya Shuraim ya iya soyayya gaba daya ya gama tafiyar da Afreen tuni ta fada tarkon sonsa bata sani bah, yawo sosai sukayi cikin birnin Lagos ya kaita wuraren shakatawa daban daban ya kai ta beach da parks kala kala haka ma shopping . sati biyu sukayi sannan ya shirya musu ticket d'in jirgi na komawa Adamawa bayan kwana biyu kuwa suka wuce airport sai land of beauty.

******
Bayan dawowar su ya koma gun Salina ta sauke girman kai ta mishi tarba me kyau abunka da mata da miji har ya manta fushin da yake da ita, Afreen kam tayi missing nashi ba Kadan bah haka ta yini tamkar Mara laka a jiki. Bayan kwana biyu ya dawo bangaren ta suka cigaba da soyewa a nan ta samu ta lallaba shi zancen komawa makaranta dakyar ya amince washe garin kuwa ta fara xuwa, kawayenta sai murna suke kowa na cewa ta kara kyau da haske.

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya an raba modibbo estate mutanen gari kowa na mamaki domin kuwa dayan gate d'in an maidashi Bukar kojoli estate yan gulma sai maganganu suke modibbo kam ranar har kuka sanda yayi don tsabar bakin cikin rabuwa da kanin nasa . Afreen ta share wata biyu a gidan Shuraim cikin wata biyun kuwa sau d'aya taje gidan su gara ma gidan modibbo donhaka yau ta lallaba mutumin nata dakyar ya barta ta tafi.
     Dama ranar girkin Salina ne donhaka Shuraim na falon ta ta xuba mai abincin rana lokacin karfe 4:15 ne bai dawo da wuri bah shiyasa sai ynxu yake cin abincin lunch nasa, yana sauri don zaije daukar Afreen daga gidansu a gurguje yake cin abincin yana duba lokaci. Salina kuwa sai kallon sa take tana murmushi ko meyasa oho! wani zobo ta xuba masa a cup mai sanyi yasa hannu ya d'auka sau biyu ya kurba yana lumshe ido don tsabar dad'i
" wow gaskiya zobon nan yayi dad'i my wife "
  Murmushi tayi tace " Allah koh" "sosai ma kuwa I like it" dariya tayi sannan ya cigaba da shan zobon, bayan ya gama cin abinci ne ya kwanta bisa 3 seater nan Salina ta fara jansa da hira tuni ya mance da wata Afreen.
     5:30 Afreen ta kira wayarsa saki ya Ja sannan ya d'aga ko me ta gaya masa oho sai naji yana cewa " Ki kwana kawai sai gobe " daga nan ya kashe wayar, Salina kam murna fal a cikin zuciyar ta tabbas maganin ya fara aiki haka ta cigaba da Jan hankalin Shuraim har Xuwa magrib sannan suka tashi don gabatar da salla .

A can bangaren Afreen kuwa mami ce ta kura mata ido tace " baby kin tabbata shi yace Ki kwana? "
Cikin sanyin murya ta amsa da " ehh ..mami ynxu muka gama waya nima bansan xan kwana da can.." Sai kuma tayi shiru, mami tace " da can me? Kodai akwai abinda kike boye min"? Kai ta girgiza tare da cewa
" da can munyi akan shi zai dawo da yamma ya d'auke ni , toh shine naga after 5 baizo ba shiyasa na kira sai yace na kwana sai gobe " shiru mami tayi tana nazarin maganar har Abba ya dawo daga masallaci yana kallon Afreen yace

" me kike jira baki koma gidan Mijin Ki bah?" Shiru tayi ta sunkuyar da kai mami ce ta masa bayani Abba yace " aah ba zaayi haka ba Ki tashi yayan Ki ya maida Ki ynxu "
  Kayi hakuri Alhj ka bari Xuwa goben tunda shi ya fad'a " mami ce ta furta hakan .
  Abba bai ce komai ba ya wuce bangaren sa amma bahaka zuciyar sa ta so bah, mami tabi bayan sa dakyar Afreen ta Ja kafafunta ta koma d'akin barcinta na da tun kan tayi aure. Da dare ma ta jira kiran Shuraim amma shiru bai nemeta ba ta kira layinsa har sau 3 bai d'aga bah dakyar ta samu tayi bacci da tunani iri iri a cikin zuciyar ta.

******

Washe garin dayake Afreen tana da class by 7 am ta shirya sadiq ne ya sauke ta a makaranta , bayan sun gama lectures ne suka fito wai xata kira Shuraim kenan ta duba Jakarta babu alamar phn nata kash! Ashe ta manta da wayar a gida. Ta duba agogon dake daure a hannun ta karfe 9 ne da yan mintuna ga tsananin yunwar da take ji donhaka tayi sallama da frenz nata ta nemi keke napep ta wuce gida.

   A falo ta iske mami nan suka gaisa mami tace " na dauka daga can xaki wuce gidan naki" murmushi tai tare da cewa " wllhi sai da na fito class ne na duba phn dina xan kira ya Shuraim kenan ashe na mance da wayar a gida"
   "Kedai kina da aiki da wannan mantuwar taki, sai Ki hanzarta kiyi kari Ki kama hanya ba sai kin jirashi bah" nan ta xauna taci abinci tayi nak sannan ta sake daukan wanka tayi kyau sosai sai juyi take gaban mirror tasan dole Shuraim ya yaba wannan kwalliya, bayan ta gama shirinta ne tayi sallama da mami ta rakata har bakin gate sannan suka rabu daga nan ta shiga keke Xuwa gidanta dake can cikin estate nasu.

    Cikin kankanin lokaci mai keke ya sauketa kofar gidan ta biya kudin tare da shigewa , salina ce xaune a harabar gidan Afreen tayi mamakin ganinta a wannan lokacin tasa kai xata wuce kenan kamar daga sama taji muryar Salina ta kirata " Afreen! " da tayi niyyar yin banza da ita sai kuma ta tsaya bari ta saurareta, murmushi Salina take har ta karasa gaban Afreen wata farar takarda ta damka mata tare da cewa " sako ne daga Mijin Ki yace a baki, yayi tafiya tun da safe ina nan ina jiran dawowar ki "
Gaban Afreen ya Fadi Salina kuwa yar dariya tayi sannan ta koma bangaren ta.
    A hankali ta bud'e takardar..innalillah wa inna'ilaihi rajiun...abunda ta furta kenan nan take jiri ya fara diban ta dakyar ta dafe jikin bango hawaye ne ke fitowa sai kuma ta juya a guje tabar gidan, Salina ta sheke da dariya tace
" shegiya aje can a nemi wani Salina tafi karfin kishiya ".
Afreen kam guduwa take tamkar xautacciya batasan ya akayi ta fito bakin titi bah, abin hawa ta samu sai da suka fara tafiya sannan ya tambayeta inda zasu dakyar ta fada masa sannan suka dau hanya.

     Mami na falo tana nazarin wani littafi Afreen ta shigo kamar an jefota " subhanallah lafiya " mami ta fada a bukace , takardar Afreen ta mika mata hannu na rawa ta karba tare da budewa....

*ni Shuraim na saki matata Aisha Afreen saki d'aya ba tare da wani dalili ba* ...abunda aka rubuta a cikin takardar kenan tsaki mami ta Ja tace " toh sai me? Ynxu sakin ne ya birkitaki haka? Haba kamar ba mace bah? Ina juriya da hakurin da na sanki dashi? Dallah malama Ki share hawayenki, dama ni nasan irin hakan zai faru donhaka Ki kwantar da hankalin Ki Allah yasa hakan shine alheri "

Kuttumelesi readers kuna jin abinda ya faru?????

Hmmmm auren wata biyu...muje xuwa😘😘😘

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...