💞 *Nadamar Soyayya*💞
( a true life story)
🖊by *_Reefat Yahya_*💞
*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_
*Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_
*Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_
*Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_
*Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_
*Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_
*Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_
*Kadan kenan daga cikin hirar da mukayi da wacce abin ya faru da ita readers muje Xuwa, ni kaina ina son sanin meya faru cikin tarihin rayuwar nata*
💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻
_To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com
_dedicated to *Zaleedah S Nalado*_my kwalliyas😘😘
Page *1&2*
Tsaye take a gaban mirror d'in dakin nasu sai faman kwalliya takeyi ta shafa wancan ta goge wancan, Kanwarta islam dake zaune a bakin gado sai faman jiranta take tun dazu taja dan karamin tsoki "mtswe! Mutum da kyanshi ko kwalliyar me zai tsaya yi kuma dallah batasan ma idan batayi wannan haukan ba tafi yin kyau.." Da sauri yarinyar da ke kwalliya a gaban mirror din ta juyo tace "me kike cewa Islam? Cikin tsoro Islam ta zaro ido waje tace " lah bance komai ba fa Yaya.. Kawai cewa nayi "please kiyi sauri kada muyi late tun ranar fara zuwanmu islamiyya din" kallon kin ma rainani yarinyar ta bita da shi cikin bacin rai tace "yimin shiru munafuka kin dauka banji abinda kikace bane ba.. So kike kowa ma ya zama kamarki ne ko bagidajiya yanda baki gayu nima haka kikeson ganina firi-firi kamar wata village girl? Wait wai Ko dai bakinciki kikemin ma dai dan kinga inada farinjinin samari da yawa har layin manya manyan motoci ake a kaina..?" "A'a yaya khairat ni fa banma isa kula wasu samari ba" da sauri islam ta bata amsa tana matsawa nesa dan gudun kada taci duka dan ba karamin aikin yayar tata bane ba tayi mata dukan tsiya idan ta mayar mata da amsa.
Hakalinta kwance ta cigaba da yin kwalliyar da takeyi har sai da ta gama tsaf ta tabbatar da tayi kyau sosai sannan ta wuce ta gefen Islam dake a takure ta dauki hijab dinta na islamiyya ta saka ta wuce wajen rataya jikkunansu ta dakko wata hadaddiyar sidebag dinta ta zuba litattafanta a ciki sannan ta ratayata a kan hijabin ana iya hango rigar uniform dinta da ta wuce guiwa da kadan da wandonta da ta mayar da shi kamar pencil.. Gaban modobi ta koma taje ta tsaya tana karewa kanta kallo ta hau juyi taga ko'ina yayi very neat kamar yanda takeso. Murmushi tayi ganin yanda tayi kyau duk da ita kanta tasan dama ita din mai kyau ce "sai dai gaskiyar bahaushe da yace idan kanada kyau ka kara da wanka" tace a ranta.
Baki islam ta saki tana kallon ikon Allah duk da tasan halin yayar tata toh amma abun nata kulllum sai gaba yakeyi ma sai kace mai aljannun kwalliya.. Kunkunai ta kamayi a ciki ciki tace "Mtswe! Kuma sai ance anason mutum yaji haushi yace an rainasa ma shi ga mai class amma dubi wannan irin kwalliya da tayi da sunan zuwa islamiyya.." Cakk! Khairat ta tsaya da neman takalmin da zata saka da take ta taso tazo gaban islam "inajinki dan ubanki.. Allah ko islam ki fita daga harkata idan kuwa ba haka ba duk abinda nayi maki ke kika siya da kanki.." Tace tana zubawa islam din rankwashi a kai "ashhh! Wayyo Allah yaya da zafi fa.." Islam tace tayi rau-rau da ido kamar zatayi kuka.
"Ai dama dan kiji zafin nayi maki mai shegen sa idon tsiya kawai.." "Yayi kyau sarauniyar yan' gayun Nigeria.." Akace daga bakin kofar dakin..
Wani matashin saurayi ne dake tsaye a bakin kofa tun fara maganarsu shine ya katse khairat daga maganar da take.. Yana karasa shigowa cikin dakin ya kama kunnen khairat da karfi ya murde.. "Wayyo kunne nah! yaya da zafi".. Khairat tace. Cikin dariya ya bata amsa da " ai dama dan kiji zafin nayi maki sarauniyar yan gayun Nigeria.." Yace yana mai kwaikwayarta.
Su dukka suka saka dariya har islam duk da tana jin tsoron masifar khairat amma ganin yayan nasu na a kusa yasa itama tayi dariyarta mai isarta.
Khairat ce ta katse masu dariyar da suke hakanan tace "Allah yaya ka daina kirana da wannan sunan banaso" "ahh toh karya nayi ne ba yar gayun bace ba?" Yace yana mai kallon islam ita dai murmushi kawai islam take a ranta tace "kai yaya usman akwai ban dariya wlh wai yaya khairat ce sarauniyar yan gayun Nigeria. Opposite in meaning kenan.. Idan ba haka ba waye zai bawa yaya khairat wani sarauniyar yan gayun Nigeria bayan duk yan gayun dake dakwai mtswe!" Agogon hannusa ya duba yaga har hudu da rabi ta gota"oya ku wuce muje na kaiku islamiyyar.. Gayun ya isa hakanan." Yace yana kallon khairat da ta cika tayi fam kadan take jira.
"Toh" islam tace tana ficewa daga dakin. Ita kuma khairat ta wuce ta dauki takalman da zatasa tabi bayan islam rai a bace..
A falo ta iske islam tana bawa ummansu labarin abinda ya faru umman sai dariya takeyi..
Islam na hangota ta ja bakinta tayi shiru sai ma mikewa da tayi da sauri tana cewa "umma na tafi." "Toh auta Allah yasa a shiga a sa'a." Umman tace" islam ta bata amsa da "Ameen ummanah!" Ta fice zuwa wajen mota ta jira fitowarsu yaya usman dan shi zai kai su saboda yau ne farkon fara zuwansu islamiyyar.
"Umma kiyima yaya usman magana ya daina kirana da wannan sunan banaso" khairat tace tana kallon yaya usman da ke zaune a kan daya daga cikin kujerun falon. "Kai yayansu toh ka bar kiranta da sunan mana tunda batason sarautar" umma tace tana mai boye dariyarta. "Ke ba sai kin hadani da ummata ba suna ne daga ranar da kika rage wannan kwalliyar haukan zan daina kiranki da shi.." Yaya usman yace yana mikewa daga kan kujerar da yake ya nufi kofar fita daga fallon yana cilla keys din dake rike a hannunsa..
Har yakai bakin kofa ya juyo yaga khairat na nan zaune a inda ya barta zaune. "ke wallahi idan kikayi wasa zanyi tafiyata na barki sai dai ki taho a kasa kuma dole ne kizo yau din zanjiraki a makarantar komai dare." Yana gama magana yayi ficewarsa daga falon.
Da gudu khairat tabi bayansa tana "umma na tafi" toh khairat Allah ya kiyaye yasa a dawo lafiya" umma tace. Khairat batajita ba ma ita har ta fice daga fallon dan ko yau tayi niyyar zuwa makarantar nan idan ko yaya usman ya barta ya gama da ita wallahi dan bazataso ace duk wannan kwalliyar da tayi ya tashi a aikin banza ba..
Har ya tada mota kuwa mai gadi kadai yake jira ya karasa bude masu gate ta samu ta bude ta shige baya da sauri "washh" tace tana kwantar da kan akan kujera ta hau maida numfashin gudun da tayi.
Saita mirror din gaban motar yayi ta yadda zai iya hangen khairat yana ganin yadda take maida numfashi daya bayan daya..
Ya hau yin dariyar mugunta.. A lokaci guda kuma ya Jade fuska kamar ba shi ba yace "yaya dai yar gayunmu?" Banza tayi masa kamar ma bataji ba.
Ganin haka yasa shima yaja bakinsa yayi shiru kawai yasan yau yakai khairat karshe kuwa tunda har tayi shiru.. Kowa yayi shiru kamar babu mutane a motar hakan yasa shima ya mayar da hankalinsa a gun tukin da yake ya kama hanyar sabuwar islamiyyarsu khairat..
Suna isa maigadin gate din islamiyyar ya taso ya bude masu suka shiga daga ciki yaya usman ya samu guri yayi parking..
Suka firfito ya rage sauran khairat kadai a motar kamar bazata fito ba sai da ta dade dan har su yaya usman sunyi nisa sannan ta fito da kafafunta daga cikin motar bakinta dauke da ad'dua "ya Allah ka sadani da alkhairan dake a cikin makarantar nan.. Sharrinta kuma Ka nisanta ni daga gareshi." Sannan ta fito ta mayar da marfin motar ta rufe. Ta tsaya tana karewa harabar makarantar kallo a ranta tace "nan kuma ko wanne mai rabon shan wulakancin ne zai ce yanasonah..?" Tayi murmushi da ta tuna da dalilin barowarsu tsohuwar makantarsu dan wani malami yace yanasonta har yayi gangancin samun number wayarta shine tayi masa wulakanci..
Kafadarta ta daga ta tabe baki alamar she don't care. "Whatever, ai shi yajawa kansa." Khairat tace tana nufar hanyar da taga su yaya usman sunbi..
Wasu kanan yara ta hango da alama daga bathroom suke.
Tsayar da yaran tayi tace "please ina ne office din headmaster?" Juna suka kama kallo sai yar' babbar cikinsu ce tace "ko dai staff room din malamai kike nufi? Ai dukka malaman a hade suke." "Ok can toh zaku rakani" khairat tace.
"Yaya khairat!!!" Taji muryar islam na kwala mata kira waigawa tayi ta hangota tsaye a bakin wata baranda da alama a nan wajen office din yake. Wucewarta tayi tabar yaran dake a gabanta tsaye ita ta ma manta da su..
Ganin har ta shigo tsakiyar makarantar yasa tayi saurin canja tafiyarta, dama khairat ba daga baya ba wajen yanga.. Ai kuwa ta samu yanda takeso din dan daliban da ke a bakin windows din classes duk sun shaida zuwanta sai kus-kus sukeyi ita kuwa sai kara canja tafiya take.. Kafin takai Islam har ta gaji da jira tayi komawarta office din..
Da sallama khairat ta shiga office din sannanta gaishe da malaman da ke a office din. Nan yaya usman ya hau yiwa headmastern bayani "yauwa ga dayar nan malam sai a gwada karatun ko waccensu a sakata a ajin da ya kamaceta".
Khairat aka fara mikawa kur'ani ta karanta surar da suke a makarantar da suka baro. Babu laifi tiryan-tiryan ta karanta har sai da ta kusan gamawa sannan headmastern yace " Dakyau ya isa haka. Khairat ko?" Ya bukaci sanin sunanta. Khairat ta basa amsa da" eh mallam"
"Zamu ajeki a aji 4 saboda surar da kike a ta gabanta yan aji hudunmu suke."
" toh" kawai khairat tace ta mayar da qur'aninta a jikkarta ta samu gefe ta tsaya. Islam ma surar da take a islamiyyar da suka baro ta karanta. Ita kuma aka ce aji ukku za'a kaita. "Toh yayi hakan babu damuwa malan" yaya usman yace yana mika masa kudin makarantarsu.
Wasu yanmata ukku ne da bazasu wuce sa'o'in khairat ba suka shigo office din da sallama. Khairat ta dawo da kallonta gurinsu taga wadannan yanmatan dake lekenta ne dazu suna kus-kus..
Daya daga cikinsu ce tace "malam baki mukayi ne?" ya bata amsa da "eh" "dan Allah malam a kaita ajinmu.." Daya daga cikinsu tace tana kama hannun khairat. "Kuje Ku rakata ajin naku kunyi sa'a can ajin naku aka kaita dai" "yeeeeh" daliban sukace cikin jin dadi suka ja khairat sukayi aji.
Suna shiga ajin khairat ta nemi sit ta zauna a can baya su kuwa sauran yanmatan malamin dake ajin ya tsayar da su yace"Ku dan kun rainamin wayau shan ruwan kenan ko?" Dariya ce ta kufcemasa ganin yanda sukayi tsuru-tsuru yace "kuje Ku zauna"
Da sauri biyu cikinsu suka zauna a sit din da khairat take suka sakata tsakiya ita kuma dayar ta zauna a sit din bayansu sannan malamin ya cigaba da karatun da yake.
Tun shigowarsu khairat ajin ta lura da malaminnan bakinsa baya iya rufuwa da ta kalleshi sai taga yana yimata dariya ko murmushi.. Sai yanzu khairat tayi magana da ta kusa da ita tace "hey! Amma dai wannan malamin naku yanada ciwon dariya ne ko?" "Me kikace " dalibar tace tana zare idanu ganin malamin idonsa na a kansu. Khairat ta dake ta kalli cikin idon malamin tace " nace ba wai shi wannan malamin naku yanada ciwon dariya ne? Naga tun da muka shigo yaketa dariya shi daya ko ba'ayi abun dariya ba.." Cikin tsoro da mamakin karfin halin rashin kunyar wannan bakuwar dalibar yarinyar tace "na'am me kikace" "ke cewa nayi yanada matsalar dariya ne?" Khairat tace da karfi ganin yanda malamin yake karayimata smile kamar bashida zuciya a jikinshi shi komai smile ita a rayuwarta ta tsani namiji marar aji...
A hankali yarinyar dake a bayansu ta rada mata a kunne "ke shi fa wannan bashida matsala ko kadan haka yake always smiling.. Ki bari idan Allah ya kaimu ranar litinin zakiga malam Al-ameen daga litinin yake zuw.. A ranar zakiga rashin mutunci da miskilanci da mugunta ko kadan bashida imani ko dan yana ganinsa mai kyau kamar wani balarabe.."
Baki da kunne khairat ta saki tana sauraron bayanin sabuwar qawar tata dan da ganinta zasuje da ita irin qawar da takeso ce itama tasha makeup dinta abun ba sauki..
"A nan makarantar ne za'a samu mai kama da larabawa?" Khairat tace tana mai kasa gasgata zancen yarinyar...
https://mynovels.com.ng/zaki-page-1-to-40/
ReplyDelete