Skip to main content

Kece kaddarata

*KECE KADDARATA*
     
          *2017*

*Story and written by:*
*Halieymerh Ameen💕*

       *T.W.F*

       *Page 16 to 20*

*KATSINA STATE*
       

         9:30PM
Habib da Abdul zaune a daki suna kallon wani Indian film, Umma ce ta bude kofar dakin suka maida kallonsu wajenta
"Kallo kukeyi be?" Ta tambaya
"Eh Umma" Abdul ya amsa
"To yayi kyau.........Habib ko Nazifa ta fada maka gobe zata dawo kuwa?" Tashi yayi daga kwanciyar da yayi
"A'a amma dazu da safe naga missed call dinta ko da na kira kuma baya tafiya"
"Ayya to dai gobe tana hanya seka kirata kaji karfe nawa jirginsu zai sauko"
"To shikenan Umma zan kira"
"Abdul ya akayi ne ?ina fata babu wata matsala kam" murmushi Abdul yayi
"Aaah ba komai Umma nagode sosai"
"Bakomai karkaji komai" ta fice tare da janyo musu kofar.

Washegari misalin marfe 4:00 na yamma Habib na zaune a mota yana chatting sega Abdul ya shigo da sauri tare da rufe kofan motan
"Muje ko" kallon zolaya Habib ya masa yace
"Dan renin sense saida ka gama jamin class zaka wani ce mu tafi"
"Kaide muje dan naga gaba daya ka kosa kaga Nazifa"
"Hmmm ba dole inkosa ba ita kadai fa gareni"
"Da gaskiyar ka dole kaji da ita na goyi bayanka"(mahaifiyarsa ya tuno lokacin da suke wannan maganar),motan Habib ya tayar suka fice daga harabar gidan,gudu yake sosai kafun mintuna 15 saigasu cikin airport din.
4:45PM jirginsu Nazifa ya sauka,daga nesa Habib ya hango kanwar tasa tana tafe tana murmushi da gudu tazo ta rungume yayanta,jin muryarsu ne ya dawo da Abdul daga dogon tunanin da yatafi dan fun zamansu wajen yayi shiru tunanin *KADDARARSA* yake bashi da burin da ya wuce ya ganshi tare da ita.

Kamarwacce akacewa juya tayi ido hudu da Abdul kwarjini yayi mata hankalinta ya koma kanshi Habib ne yace  mata "Nazifa ga abokina Abdul,Abdul ga Nazifa" murmushi Abdul yayi yace
"Sannu Nazifa ya hanya" dakyar ta iya amsa
"Lafiya".
  
Kayanta suka dauka suka nufi parking space, Abdul ne a gabansu yanajan trolley ba karamin burgeta yayi ba gashi shiru shiru tunani ta farayi ina yayanta ya samo wannan handsome guy din me cute smile,tanason tamabayan Habib amma tana tsoron kar yai mata fada sai tayi shiru kawai.
Suna tafiya a mota suna hira jifa jifa Abdul yake magana amma Nazifa se satan kallonsa take har suka iso gida. Umma tana jin tsayuwar mota ta fito da saurin dan tarban autanta ta aikuwa Nazifa na ganin Umma ta taho a guje ta rungumeta
"Oyoyo Ummana"
"Barka da zuwa autan Umma"
"Umma ya jikinki"
"Naji sauki sosai mu shiga daga ciki" kama hannun ta Umma tayi suka shiga ciki, daki suka wuce.
Nazifa da Allah Allah takeyi su shigo ciki ta tambayi Umma, ajiye gyalenta tayi a bakin gado ta zauna tace
"Yauwa Ummana nikam da wayene yaya yaje daukoni?" Murmushi Umma tayi tace
"Toh fa minene? Ko wani abun ya miki?"
"A'a kawai dai naga bansanshi bane Yaya yacemin abokinsa da mukazo kuma naga ya wuce dakin Yaya kansa tsaye" ta fada tana kwanciya
"Tashi maza ki shiga kiyi wanka kiyi sallah kizo muci abinci barinje kitchen inkarasa shirya abincinin"
Mikewa Nazifa tayi ta nufi toilet.


Bayan tayi sallah suka fito ita da Umma suna jiran su Habib, suna cikin zaune saiga Habib ya fito daga side dinsu Abdul na biye dashi black jeans ne a jikinsa da blue T-shirt fuskarsa dauke da murmushi. Nazifa tana daga kai sukayi ido daya da Abdul, kawar da kansa yayi ya karaso a tsanake ya zauna har nan ta kasa sauke idanunta a kansa kowa sake baki yayi yana kallonta shikuma Abdul kunya yaji saida Umma tai mata tsawa ta firgita ta fara kame kame, Hararanta Habib yayi ta sunkuyar da kai kallonta kawai Umma tayi a zuciyarta tana cewa
"Wannan yarinya me take nufi ne anya lafiyarta kuwa dazu ta tambayeni wayeshi yanzu kuma ta tsareshi da ido  hmmmmmm Allah ya kyauta".Umma da kanta tayi serving dinsu.





*🕯Halieymerh Ameen🕯*

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...