💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
04
Albarka ta dinga shi masa tace dashi bikin bazai wuce nan da wata 1 ba, ba komai iro yace ya koma ya kwanta.
Baba kuma ta fita daga dakin domin ta kimtsa taje ta sanar da qanwar tata, tana isa gidan ta zayyane mata komai murna ce ta cikata. Ta dinga yiwa yayar tata godiya.
Rana bata qarya sai dai uwar diya taji kunya, a yaune ake daura auren larai er qanwar baba da iro Dan kishiyar ta. Bakin baba kamar ya yage don murna saboda burinta ya kusa cika.
Da daddare aka shirya amarya larai aka kaita gidan mijinta, inda acikin gidan ya gyara wani guri inda zai zauna da iyalansa.
Tun bayan Biki da sati uku larai ta fara nunawa iro ainihin halayen ta, ko sau daya baba bata taba yiwa larai fada ba.
Idan ma iro yakai qarar ta sai baba ta daura laifi akansa tun daga lokacin ya daina gaya mata komai Nasa.
Ahaka larai ta sami ciki har ta haifi danta namiji sak kamarsu daya da ita.inda yaro yaci suna sule.
Bayan shekara uku ta kuma haifar diya mace mai suna mejidda, sai kuma bayan shekara daya da wata Tara ta haifi yarinyar ta mai suna lami.
kaf dukiyar iro larai ta kwashe ta bawa baba ita, a dalilin haka iro ya dawo matsiyaci ( da yai magana cewar baiga dukiyarsa ba sai sukace ai daya fitane barayi sukazo suka kwace komai na gidan haka ya dau hakuri).
Tun daga lokacin baba ta sauyawa iro fuska masifar yau daban ta gobe daban.
Haka ake rayuwa gidan malam iro cikin qunci sai ya fita yayi ciyayi ya sayar sannan ya samu ya bawa larai tayi cefane.
Randa kuwa ba'a samu ba sam babu zaman lafiya a gidan.
Tunda iro yaga tsantsar Halin baba da larai shine ya samu wata yarinya mai hankali a layinsu ya aura wato zulai, shekara zulai daya a gdn larai ta haifi er ta inda tasaka mata sunan baba wato Halima, (tunda zulai tazo gidan bata taba samun kwanciyar hankali ba larai da yaran ta suyi mata baba ma tayi mata, sai malam iro yazo take samun kwanciyar hankali).
*cigaban labarin*
A haka rayuwa tacigaba da gudana a gidan malam iro, inda yanxu nafisat (feenert) take maida hankali a karatun ta, Dan takusa hadda ce izu goma, bangaren boko kuwa yanzu tana aji biu saboda qwazon ta.
Zulai kuwa gwargwadon iko tana farantawa yarinyar tata rai, duk abinda takeso tana bata.
Wata rana feenert ta fita tsakar gida yin wanke2 sai ga lami ta fito daga bayan gida, wani wawan mari ta dauketa dashi ke shegiya uban waye yace ki taba mana kayan en halal lami ce take magan ciketa facin rai afuskar ta.
Da gudu feenert ta koma daki domin taji marin har cikin ranta.
Tana shiga ta fada kan cinyar innar ta kuka take wiwi kamar ranta zai fita inna (zulai) ce take tambayar ta ke mamana ke dawa tana sheshsheqa ta fada mata inna ba lami bace ta nareni wai karna qara taba kayan en halal wai ni shegiya ce.
Daina kuka mamana keba shegiya bace ba domin nice na haifeki malam kuma shine baban ki yawwa inna ta daman nasan lami ba gsky ta fada ba rungume ta innar ta tayi aranta kuwa cewa tayi oh ni naga ta kaina ace wannan qanqanuwar yarinyar lami take cewa shegiya meta sani.
Allah ya kyauta juyowar da zatayi taga feenert har tayi bacci, kwantar da ita tayi ta fita tsakar gida domin qarasa wanke2.
fitarta keda wuya ta cigaba da wanke2, sallama taji ana dokawa ta amsa shigowar da za'ayi tayi tozali da fuskar larai wata uwar harara ta doka mata sai da tazo dai2 da ita ta fara yada mata da bakaken maganganu mejidda ce ta fito daga uwar daka domin jin hayaniyar da akeyi a tsakar, fitowar ta keda wuya ta amshe da....yo ce mama ai idan aka bibiya itama shegiyar ce bata rufe baki ba taji wa2n mari a fuskar kafin ta dago taji an qarayi mata wani hagu da dama. Dagowa tayi da zummar ganin waye ya mareta sai taga ....wa babanta wallahi kika qara zagin matata sai nayi miki dukan da babu wanda ya taba yi miki shi.
kai malam akan wannan shegiyar matar taka ka dakar min ya wallahi yau sai anyi ta a gidannan.
Wucewa tayi fuuuu sai a bangaren baba taja burki, kwashe labari tayi ta fadawa baba ai kuwa kamar ana tsungurar ta tace muje naci ubansu su duka fita sukayi tsakar gida amma me sai sukaga babu kowa a gurin.
Mejidda ce tace da larai kina barin gurin nan suka shige daki suka kulle.
ashar suka dinga yi, sannan daga bisani da sukaga sun gaji shine kowa ya tafi dakin sa.
Akwana a tashi babu wuya gurin Allah feenert ta sauke Alqur'ani sannan tasan littafai da dama a bangaren hadda kuwa tana da izu arba'in da biyar, a boko kuwa tana ajin qarshe na qaramar sakandare wato jss 3, kyawun ta sai fitowa yakeyi inda a yanxu feenert tana da shekara goma sha biyar. Kuma a yaune baba ta bujuro da alqawarin da sukai lokacin da aka kawo feenert gidan inda ta fito tsakar gida tana ta banbami, ita ala dole sai feenert ta bar gidan a yau ba gobe ba.
Wannan magana ta tayar wa zulai da malam iro hankali ba qaramin kidime wa sukai ba. da kyar ya bata hakuri cewa ta bari zuwa wani lokaci. Sallamar feenert ce ta ankarar da su juyowa sukai gaba daya suna kallan ta domin wani farin ciki ne dauke a fuskar ta, wani tsawa larai ta daka mata ke shegiya garama kidaina wannan farin cikin da Kikeyi domin kuwa kin kusa barin gidannan, ko kulasu batayi ba ta shige daki domin inda sabo ta saba jin wannan bakaken kalaman daga bakin su.
fatimaauwal1999@gmail.com
Pherteenjeey✍🏻
Comments
Post a Comment