💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....👇🏻👇🏻👇🏻
_To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na _*Sunhera*_
*dedicated to* _*Reefat yahya*_
*47&48*
Yau Afreen ta cika 5 days a gidan amma sau d'aya kawai ta had'u da Salina tun ranar da Shuraim ya had'a su ya musu fada da Nasiha akan su xauna lafiya tun wannan ranar basu kara haduwa ba. Khalid kuwa yana son Xuwa gun Afreen amma Sam Salina bata barin yaron sai da Shuraim yake Xuwa bangaren Afreen wannan ma don babu yadda xatayi ta hanashi ne, Afreen tana xaune a harabar gidan bisa wasu fararen kujeru tana rike da wayarta chat take a watsap matan gidan gyara na tsokanarta wai tana can tana dirje amarci murmushi take tana hira da yan group d'in. Khalid ne ya fito daga bangaren su cike da xumudi ya fada jikinta yana dariya "anty na " murmushi tayi ta ajiye wayar tana shafa kansa tace " yarona ya kake?" "Lafiya antyn Abba na" dariya Afreen tayi tace " kai Khalid ba dai iya magana ba, toh yau ba islamiya ne?" B'ata fuska yayi ta kura masa ido yana matukar kama da ubansa sak! Ya turo baki yace " ba mum na ba taki ta min assignment " " meyasa ?" Afreen ta tambaya
" uhmm..nima ban sani ba, tun jiya na bata taki ta min zan nuna wa Abba idan ya dawo" murmushi Afreen take tace " toh jeka kawo mu gani ko zamu iya nida kai zamu yi ynxu koh?" Cikin farin ciki yace " Allah?... tohm nagode anty baby"
Ware ido Afreen tayi tace " ina kaji wannan sunan kuma?" dariya Khalid yayi yace " toh ba Abba na bane yake ce miki baby " dariya tayi kai yaro sai shegen wayo da surutu, Khalid ya wuce bangaren su da gudu don d'aukar littafin dai-dai nan aka wangale gate d'in gidan motar Shuraim ta hango ya shigo harabar yayi parking ya fito fuskar sa d'auke da murmushi ya nufo inda take " barka da dawowa yaya" ta fad'a a yayinda take kokarin karbar jakar dake hannunsa " barka de my baby amma ni gaskiya bana son wannan yaya da ake kirana dashi, ynxu matsayi na ya wuce nan" murmushi tayi ta sunkuyar da kai. Khalid ne ya fito yana kuka da karfi gaba daya suka fara tambayar sa lafiya cikin gunjin kuka yace " ba mum bace naje d'auko littafi na don anty baby tace zatamin assignment shine ta hanani kuma ta mareni " tsaki Shuraim ya Ja yace " sorry baba na zo muje mu d'auka koh" nan ya rike hannun yaron suka shiga part d'in Salina. Tana xaune a falo ta harde kafa sai kada su take tamkar wata basarkiya ta cika tayi fam ko sannu bata ce masa ba , d'akin ta suka shiga nan ta harzuka tabi bayansu Khalid ya bude school bag yana duba littafin ta shigo sai huci take " uban me zakayi littafin ,ba nace da dare xan ma bah ehh Khalid.. " yaron yayi rau rau da ido yana kallon mahaifinsa Shuraim yace " ka d'auko littafin mu tafi baba na "
" ehh..sannu me mata wato ni jahila ban iya ba shine xaa kaiwa shafaffiya da mai yar boko tayi koh? Toh wllhi baxata koyawa yarona karatu bah salon a rabani dashi koh" murmushi Shuraim yayi ya fisge jakar tare da rike hannun Khalid ya juya zasu tafi tayi saurin shan gabansa tace " ban amince bah"
" Salina banson hauka pls ynxu na dawo bana son hayaniya" " ai hayaniya kai ka nema ka kyalemin yaro sai ka tafi a xauna lafiya " murmushi yayi yace " sannu me yaro, toh idan naki fah?"
"Sai ranka ya baci" ta bashi amsa kai tsaye yasa kai zai fita ta rike school bag d'in nan kuwa ya d'auke ta da mari babu b'ata lokaci ta saki jakar ta fara kunduma ashar bai kulata ba ya Ja hannun Khalid suka fice yana jin Zafin Marin da ya mata .
Afreen ta gama shirya masa komai bisa dining tana xaune a falo suka shigo a Kasan kafet suka xauna tace " yaya abinci fah?" " Ki bari sai anjima " ya bata amsa ta lura kamar ransa a bace yake Sam yaki hada ido da ita , batayi kasa a guiwa ba tace " wanka fah?" Shiru yayi kansa na kallon kasa ta tashi Xuwa kusa dashi ta rike masa hannu tare da cewa
" muje kayi wanka pls" a hankali ya tashi ta maida kallonta gun Khalid tace " bari nazo muyi assignment koh" gyada mata kai yayi daga nan suka wuce bedroom.
Bisa gado ya xauna kansa na kallon kasa Afreen ta risina ta fara cire masa takalma ga mamakinta digon hawaye ta gani tayi saurin d'aga kanta sai ga Shuraim yana xubda kwalla
"Subhanallah..yaya lafiya?" Zama tayi kusa dashi nan ya jawota ya kankame yana ajiyar zuciya ,shiru sukayi har na 10 mins daga karshe ya saketa ya tashi ya tube kayan jikinsa daga shi sai boxers da vest a haka ya wuce toilet. Shiru Afreen tayi tana mamakin wannan lamarin tana nan xaune ya fito daga wanka daure da towel kanta na kallon kasa har ya gama shirinsa cikin kananan kaya ya fesa turare sannan ya juya bangaren da take.
Murmushi ya sakar mata yace " na gama muje Ki bani abinci " babu gardama tabi bayansa suka fita a kasan kafet ya xauna nan ta sauke kwanikan ta xuba masa nan Khalid ya matso tare suka ci suna santi Khalid yana cewa " anty baby kin fi mumy na iya abinci " Shuraim yayi mmki jin wannan furucin kunya ne ya kama shi yayi fuska kamar beji ba haka ma Afreen shiru tayi batayi magana, sallama suka jiyo daga bakin kofa Afra ce tare da Afiya da kuma Zee cike da jin dad'i Afreen ta daka tsalle ta rungumi Afra Shuraim sai kallon mmki yake mata yanda take murna tamkar wacce akayi wa kyauta. Cikin girmamawa suka gaida yayan nasu nan ya tashi ya koma bedroom tare da plate din abinci Khalid ma yabi bayan sa, zama sukayi Afreen ta gabatar musu da kayan motsa baki tana cewa
"Shegu sai yau kuka ga damar Xuwa " tabe baki Afiya tayi tace " mu a su wa? Ynxu ma kinga wani kallon da yaya yake mana, uhmm Nide muyi mu tafi kar mu katse musu jin dad'i " duka Afreen ta kai mata cikin wasa a yayinda Afra kuwa ta gyara Xama
" ynxu tweenie Ki bani labarin amarci nasan tuni Yya ya angwance" dariya sukayi Afreen tace " shegiya sai Ki shiga yayan naki ya labarta miki ai" ido ta xare tana yin kasa-kasa da murya
Tace " ke...rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mata bah, Tabb.. ai wllhi sai de a d'auki gawata " murmushi Zee tayi sai ynxu tayi magana tana cewa " dota kin ji labarin uwar d'akin Ki xata samu kishiya koh?" Cike da mamaki Afreen tace " waye? Badai anty Aysha ba? "
Hade baki sukayi wajen cewa " dama waye in banda ita" afiya tace " wllhi kowa yayi mamaki da jin wannan labarin, ke har ankai lefe ma ynxu haka bikin saura wata d'aya "
" innalillah... gaskiya na tausaya mata" Afreen ta fad'a tana jinjina lamarin , Afra tayi carab! tace
"Ai dai-dai kenan tunda ta hana Ki shiga gidan gashi xaa kawo mata 'yar maiduguri ai, tana ji tana gani a rabata da miji a mallakeshi tsab babu yanda ta iya" " ke..yar Maiduguri zai aura? Kutt wllhi xata ji jiki"
" uhmm..yayi kyau ai Allah ne ya kama ta " Afreen de ta tausayawa anty Aysha tace " amma ya akayi modibbo ya yarda?"
Zee tace " shine ai..kowa yayi mmki , baki ji yadda mutuniyar ta rude ba har kuka take tana cewa dama ke d'in ya aura" gaba daya suka dara haka suka cigaba da hira har kusan magriba sannan suka ce zasu tafi dama yini suka zo a gida shine suka biya gun Afreen.
Comments
Post a Comment