💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
_To get access to talented novels check_
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na _Sunhera_
*dedicated to* _*Reefat yahya*_
*masu kira na a waya da masu turamin text cewa meyasa na raba shuraim da Afreen kuyi hakuri evrtin wil b fyn lol😘😘🐠ga naku❤❤❤🐠ina ji daku fans tnx 4 d kia*
*gaisuwa gareku writers d'in meelert, Takari, Batul , kawartace Sanadi n Zallar yaudara. hakika muna jin dad'in littafan Allah ya kara basira👍🏻👍🏻*❤😘🤝🏻
*53&54*
Hawaye wani na bin wani gaba d'aya Afreen ta kasa controlling tears nata daga karshe d'aki ta wuce ta bar mami a falon, hakika mami taji Zafin abin kuma ta tausayawa y'ar tata amma ya zama dole ta nuna jarumta don gudun batawa Afreen rai ya Xama dole ta nemo mata farin cikin ta.
Haka Afreen ta yini kwance salla kadai tayi bata nemi abinci bah har yamma zazzabi ne ya rufeta magrib ya gabato nan mami ta d'auke ta Xuwa hospital don jikin nata yayi zafi sosai, an bata gado tare da sanya mata drip inda likita ya shaidawa mami cewa Afreen na d'auke da cikin wata d'aya. Mami ta tausaya mata ba Kadan ba nan ta kira Abba a waya dama baya gari ta shaida masa komai, ransa yayi mugun baci yace gobe zai dawo ze kira Shuraim yaji dalilin sakin .
Shuraim kuwa yayi tafiya Xuwa Gombe amma Sam hankalin sa bai kwanta da sakin da yayi ma Afreen bah, can kasar zuciyarsa zafi yake ji ta wani bangaren kuma haushi tare da tsanar Afreen ne ya cika masa zuciya. Abban Afreen ya kira sa a waya cewa yana son ganinsa nan ya shaida masa cewa yayi tafiya sai bayan nan da sati d'aya.
****
Falon yayi tsit tamkar ruwa ya ci su uncle Mohammed ne ya harzuka yace " wallahi dole ya maidata don ubansa, wato so yake ya tozarta mu ya b'ata mana sunan zuri'a koh? Ynxu ma yana ganin yanda abubuwa suke ai shikenan makiya sun samu abin gorantawa" murmushi modibbo yayi ni Sunhera nace shin modibbo wane irin mutum ne?? Uncle Usman kam kunya tamkar ya shige cikin kasa, mami tana share hawaye tace
"Kuma tana d'auke da juna biyu " murmushi modibbo ya sake yi a karo na biyu sannan yace " Zainabu Ki kwantar da hankalin Ki babu abunda zai faru insha Allah, aure ne anyi an gama dama kaddarace da rabon abunda ke cikinta zai zo duniya amma ni modibbo Hammantukur ban amince Aisha ta koma gidan Shuraim bah. Kamar yanda na had'a auren ynxu ma ni xan raba koda a ce Shuraim ya nemi ta koma gidan sa ne ni ban amince bah, kuma daga rana irinta yau babu zuriar modibbo Tukur babu auren zumunci insha Allah kowa ya zabi wacce yaga dama ya aura amma ni modibbo na daina had'a auren zumunci har abada"
A firgice suka juya suna kallonsa tabbas ran modibbo ya mugun baci tunda yayi wannan furucin lallai abin da mamaki, Hajja Dada ta share hawaye tace " don Allah a masa uzuri wautanci ne ke damunsa, ni zan masa magana " kallon ta yai sannan yace " mata kenan! Toh Dada nidai na gama magana kuma daga yau kar wani ya tunkareni da zancen Shuraim dafatan zaku kiyaye" gaba daya sunyi shiru uncle Mohammed ne yace
"Ba don tana makaranta a nan ba da wallahi Abuja xata koma can gidana inda bazai kara kallon ta bah, kuma nima ina goyon bayan maganar Baba. Wllhi Shuraim ya kuskure yace zaije biko gun Uwata ( Afreen) sai na mugun saba mishi, don iskanci ma ya zaayi saki babu wani dalili ko hujja"
Nenne tace " da de an masa uxurin ni ina ganin kamar wannan lamarin da sa hannun mutane, Duk da cewa zato xunubi ne amma ni gaskiya gani nake kamar ba banza ba musamman idan kukayi laakari da irin son da yake mata" Diddi tayi carab tace " nima de zargin da nake kenan "
Ayya wace tayi jugum tun dazu sai ynxu tace " hakan ma zai iya faruwa kunsan dan Adam abin tsoro ne bare ma wannan matar tasa ai bata xauna bah"
Modibbo yace " koma menene shiya sani nidai na gama magana, zaku iya tafiya ke kuma Zainab kiyi hakuri Ki koma gida Ki rarrashi Aisha Ki bata hakuri kaddara ce bata wuce ranar ta donhaka kuyi hakuri mu taya ta da adua Allah ya sauketa lafiya ya kuma zaba mata mafi alheri. Kuma Allah ya mata albarka bisa umarnin da tabi ta xauna dashi"
Nan taro ya watse matan suka koma cikin gida mami da Hajja Dada an rasa mai rarrashin wani gaba d'aya kuka suke daga karshe mami ta musu sallama ta koma gida.
💞💞💞
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Afreen ta rame Duk da cewa tana fama da laulayin ciki amma abin nata harda damuwa a ciki. Zancen saki kuwa ya baza ko'ina cikin family masu gulma nayi masu tausayawa na yi ita de tana fama da ciwon son Shuraim don gaskiya a wannan wata biyun da sukayi tare ya dasa mata sonsa a cikin zuciya a haka de har sukayi exam d'in first semester aka basu hutu . kullum Afreen tana gida babu inda take Xuwa sai gidan kakannin nata hutunsu ya rage sati d'aya su koma Abbanta ya d'auke ta suka Je kauyensu a can kojoli dake cikin garin jada, wani kanin mahaifin Abba ne da yaji labarin mutuwar auren nata nan yace zai bincika dama malami ne aikuwa ya ga komai nan ya tabbatar da zargin da yake wato asiri akayi aka rabasu.
Washe gari ya fara bata rubutu da magungunan gargajiya ta fara amfani dasu, sati sukayi suka koma yola bayan an had'a mata wasu magunguna. Cikinta ya shiga wata na uku ynxu laulayin da sauki sai shegen kwadayi kamar mum Abla lol.. Mami na tattalinta fiye da komai ta koma skul second semester part 3 ba laifi ynxu ta rage yawan tunani sai dan abunda baa rasa bah, Ruky tana yawan kiranta su sha hira a waya haka ta cigaba da rayuwa.
Salina kam abin nema ya samu Shuraim ya samu girma a matsayin Bursa na AUN kud'i baa magana ko'ina an sanshi , Salina sai fantamawa ake da dukiya ana bin gidajen malaman tsibbu .Shuraim kuwa ynxu yana dan tuna Afreen wasu lokutan ba kamar da bah kuma har yau baisan da zaman cikin dake jikinta bah haka nan babu Wanda ya fada masa bisa umarnin modibbo kenan kuma modibbo ya hana a kawo masa zancen Afreen wannan kenan.
*7 months later ( bayan wata 7)*
Yau ta kama ranar asabar yaune Afreen xata gama jarabawar ta na first semester part 4 ta gama ta fito kenan taji mararta ya kulle , tafiya take a hankali gashi wayar ta bari a gida bare ta kira yayanta sadiq. Haka ta daure ta cigaba da tafiya ga katon cikin nata ya bayyana sosai, Shuraim ne ya fito daga cikin makaranta zai koma gida kenan kamar ance masa juyo nan ya hango Afreen tana tura katoton ciki tana tafiya dakyar. Gabansa ne fadi ras! Rabon ya sanyata a ido yakai watanni 7 baya badai cikin sa ba ya ilahi! Toh idan ba naka ba na waye? Wata zuciyar ta tambayesa , tabbas hakane wannan cikin shine ubansa amma ya akayi bai taba jin maganar bah? Ynxu me abin yi? Ya sake kallon bangaren da take can ya hango ta xaune tana yatsina fuska da alama akwai abunda yake damunta toh kodai haihuwa ce??
Da wuri yayi parking ya nufo ta a wannan lokacin ciwon yayi tsanani ta fara xubda kwalla sai wani murkususu take.
Comments
Post a Comment