Skip to main content

Rabon kwado

💞💞💞💞💞💞
*RABON KWA'DO*
*(Ko ya hau sama zai fa'do)*
💞💞💞💞💞💞

*STORY*
        *&*
     *WRITTEN BY:✍🏻*
           *ANTY MAIMOUNATH💞*

*💦Talented Writers Forum💦*
               *💦T.W.F💦*

*Had'in kan mu abin alfaharin mu🤝k'ungiya d'aya tamkar dubu*

_Domin samun litattafan mu shiga....

*To get access to talented novels check*

Hpp://
Talentedwritersnovels.blogspot.com/

🎂🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂
*HAPPY*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*🎂🎂BIRTHDAY*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*REEFAT*🎂🎂

*Allah ya k'aro wasu shekarun masu albarka,i'm so happy for u dear*

🍦🍦🍦🍦🍦🍦🍦🍦🍦

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page *43 to 44*

Mutane na hango cike da wajen accident d'in ana ta ciro mutanen cikin motar ana sakasu a ambulance....

Mutum biyar suka mutu,saura sunji mummunan rauni,Atika ko harbawa batayi ba,Hajara kuma kariya biyu tayi d'aya a hannu d'aya a k'afar dama,subhanallahi,Allah ka karemu da hatsarin mota,ameen.....

Asibiti aka kawo su Hajara saï ihu take wa mutane,hmm,aka shiga dasu emergency,bayan wasu lokuta Dr ya fito yana goge gumi ya kalli mutanen da suke tare yace''ko kun san 'yan uwan wannan matar mai ihu kowa yace bai sani ba,toh fa.....

A takaice saï da Hajara tayi kwana uku ana neman ta a gida,alhaji ya rasa abinda ke mishi dad'i dan bata fad'a mishi inda zataje ba,yana office a zaune aka nuno fuskar Hajara a T.V ana cigiyar 'yan uwanta tana asibiti,idan 'yan uwanta sun ji suzo nemanta,......

Zumb'ur alhaji Hafeez ya tashi tsaye ya d'auki wayar shi ya kira k'anen shi alhaji Al'ameen Kenan,ya fad'a mishi inda Hajara take,ya kira su Ameena su ma ya fad'a musu.....

Kusan a tare suka shiga asibitin da su Ameena,Dr ya fara gani yayi mishi bayanin shine mijin matar nan da ake cigiyar 'yan uwanta,Dr ya kalleshi yace''biyo ni office to'',bayanshi alhaji ya bi su kuma su Ameena suka zauna a nan.....

Dr yayi wa alhaji bayanin saï dai fa ayi ma Hajara aiki a k'afar a cire ta dan bazata k'ara moruwa da ita ba,alhaji ya dafe kai,dr yace''am so sorry alhaji haka Allah yaso'',nan take alhaji ya saka hannu ayi mata aikin, yaje ya sanar dasu Ameena halin da ake ciki kowa yaji ba dad'i dan ba'a biyewa halin mutum,hakane...wannan Kenan.......

Anyi aiki an cire mata k'afar,yanxu su Hajara an zama gurguwar k'arfi da yaji,hmm duniya kenan,su Ameena ne suka kawo abinci da dare da suka shiga wajen ta Hajara tana ganin Ameena ta fara tonawa kanta asiri,duk makircin da ta aikata saï da ta tona a gaban kowa....

Kowa yana mamakin abin banda alhaji da Hajiya Maryam wato maman su Kenan,su daman sun gane ta tun ba yanxu ba kawai ya kyaleta ne har ya kamata dumu dumu sannan,to gashi nan ta tona da kanta....

Ta fashe da kuka tana cewa suyi mata aikin gafara,sukace sun yafe mata,alhaji kuwa saï da hajiya tasa baki ya yafe mata saboda ta jima tana cutar su,kuma a nan asibitin ya ya saketa yace bazai iya zama da ita ba,ta koma gidan su,amma zai rink'a basu kud'in magani shima dan saboda iyayen ta ne zai yi.....

*Bayan sati d'aya.....*

An sallamo Hajara kai tsaye aka wuce da ita gidan su,'yan uwanta sunzo sun kwashe kayanta,Ameena bataji dad'i bâ,har tayi wa alhaji maganar meyasa zai saketa yace haka yayi niyya taja bakinta ta rufe dan yana cikin fushi sosai......

A gidan su *FAROUQ* kuwa *MUFEEDAH*ce a kwance a falon ta,dan wani irin jiri ne yake d'ibar ta idan ta tashi tsaye,gashi har *FAROUQ* ya wuce wajen aiki ta rasa me yake mata dad'i,batason ta kira shi hankalin shi ya tashi kawai saï ta kyale har
dai ya dawo......

K'arfe 5:30 na yamma *FAROUQ* ya shigo gidan ya isko ta a kwance a k'asa bisan carpet da sauri ya iso wajen ta ya d'ago ta yaji jikinta zafi ba na wasa ba,ya rikice yace''dear daman baki da lafiya shine bakiyi min waya ba?",da k'yar ta bud'e baki tace''banson in tayar maka da hankali ne'',

Yace''to meye amfanin zama da ciwo kuma ke kad'ai a gida,karki sake min haka kinji ko?",kai ta d'aga mishi yace''tashi mu tafi asibiti jikinki yayi zafi sosai'',ta nok'e yace''ya haka kuma?'',

Ta shagwa6e fuska tace''yaya bazasu yi min allura ba?",yace''eh bazasuyi miki ba tunda bakiso,tashi mu tafi bari in d'auko miki hijab d'in ki'',ya kwantar da ita yakai jakar shi ta labtop bedroom d'inshi ya wuce d'akinta ya d'auko mata hijabin ta ya dawo y'a saka mata,suka fice......

Wani clinic ne suka je inda ba wani tsaye tsaye aka karb'esu aka dubata,Dr yace''za'ayi mata test na fitsari kafin result ya fito saï a saka mata drip saboda jikinta yayi zafi dayawa'',ai fa nan *MUFEEDAH* ta fara hawaye dr yace''kiyi hak'uri madam saboda lafiyar ki kinji?",kyaleshi tayi ta juya kanta,da wayo ta yarda aka saka mata drip d'in tana k'ank'ame da hannun *FAROUQ* nurse saï dariya takeyi mata tana cewa mai tsoron allura,hmm lallai....

Result d'in bai wani jima ba ya fito,a lokacin *MUFEEDAH* tayi bacci,Dr ne ya kalli *FAROUQ* yace''congratulation friend,matar ka juna biyu ne da ita three weeks Kenan'',cike da murna *FAROUQ* ya rungume Dr yana cewa''thank u Dr nagode sosai,yanxu kana nufin *MUFEEDAH* na tana d'auke da d'ana a jikinta?",kai dr ya kad'a mishi yace''yes,sai a kula da ita da kyau kaga yarinya ce'',yace''insha Allah Dr,thank u again'',

Danjin dad'i har da kud'i ne ya ciro ya bai wa nurse wai tukwicin ta ne,hhhh,godiya tayi mishi suka fice ita da dr......

Kusanta yazo ya zauna ya rik'e hannunta da bâ drip a jikin yace thank u baby,kin kawo min farin ciki,Allah ya rabaku lafiya,ya koma kamar wani zautacce,hmm....

Waya ya d'auka ya kira gidan su yace suna asibiti,maman shi tace''lafiya kuwa?",yace''eh lafiya mama *MUFEEDAH* ce bataji dad'in jikinta ba shine mukazo ake mata k'arin ruwa,ya kusa ma idawa zamu biyo ku gaisa daman tana cewa kwana biyu bata je ba'',mama tace''subhanallahi,har da k'arin ruwa me sukace yana damunta?",k'eya ya Sosa kamar yana gabanta yace''mama kin kusa samun jika'',kit ya kashe wai kunya yaji,hmm ja'iri ba wata kunya....

Mama kuwa murmushi tayi ta tashi ta nufi 6angaren Ammi wato Ameena,ta kai mata albishir,itama tayi murna sosai.....saï kusan 8:30pm su *FAROUQ* suka shigo gidan daman shi yayi sallar magrib d'in shi a masallacin asibitin,6angaren Ammi suka fara zuwa,a can ma suka iske mama AYSHA,bayan sun gaisa ne sukayi mata ya jiki,shi kuma gogan naku saï wani sunne kai yake,ita kuma *MUFEEDAH* ko a ka dan bata san wainar da ake toyawa ba,ta nemi waje ta kwanta a kujera.....

Ammi wato maman ta Kenan ta kalleta tace''ke kuma har da kwanciya ki tashi ku tafi baki ganin dare ne?",tace''kai momy har ma korata kikeyi ko sallah magrib banyi ba'',

Momyn ta tace''eh naji tashi kiyi sallolin saï ku tafi'',tashi tayi jiki ba kwari ta shiga bedroom d'in momy dan yin sallah, FAROUQ kuwa fita yayi yace''zaije ya dawo,maman shi tace''kar dai ka jima,dan abban ku idan ya dawo fad'a zaiyi in ya ganku a gida warhaka'',yace''to insha Allah yanxu zan dawo'',yasa kai ya fita,su kuma suka cigaba da hirar su.....

**********    ****

*Bayan kwana biyu...*

Jikin *MUFEEDAH* ya warware amma har yanxu *FAROUQ* bai fad'a mata cewar cikine da ita ba,ita dai tanajin kwad'ayi da ta ga Abu ko da a cikin T.V ne shikenan ba zaman lafiya saï tace saï an nemo mata,toh fa...hhhh....

Suna falo tayi pilow da cinyar *FAROUQ*yana wasa da gashin kanta tace''yaya'',yayi shiru bai amsa ba,saï ta d'ago kanta ta kalleshi tace''yaya kana ji na kuwa?",yace''eh'',tace''shine ka kyaleni ina Kiran ka'',yace''to a sauya min suna indai anaso in amsa'',tace''kamar ya?",

Yace''banson yayan nan,yanxu ni mijinki ne,so ya kamata a canza min suna ko?",ta maida kanta ta kwantar tace''to zan canza,wane suna kakeso in kiraka dashi?",yace''ke zakiyi choice Wanda ya dace dani'',tace''to zan r'inka ce maka honey,da sweetheart,yayi?",

D'ago ta yayi ya rungume yace''yes,yayi dad'i nagode dear'',hannu tasa a k'irjin shi tana mishi susar k'adangare,shi kuma har da lumshe idanu,yace''dear ai kinji sauk'i ko tashi mu shiga daga ciki'',ta wayance kamar bata san me yake nufi ba,amma ita kanta taji tana buk'atar mijinta,yanxu wani feeling takeji da ta rasa meyasa ta zama haka,ni kuwa nace magana kika d'auko irin na o'o bance komai ba😜

Tace''me zamuyi kuma? kallo fa mukeyi'',yace''wani abu mai dad'i zan baki kinaso?",kai ta d'aga mishi tace''eh'',yace''to oya tashi mu taxi'',hannunta ya kama suka shige bedroom...sister in bisu ko in tsaya😆Allah binsu zanyi cabb....

Bisa gado suka fad'a da kanshi ya cire mata rigar jikinta shima ya cire tashi,yau fa *MUFEEDAH* da kanta take sarrafa *FAROUQ* abin har mamaki yake bashi ada kuwa saï tayi mishi raki tace ita ta gaji kaza da kaza,amma yau gashi da kanta ta fara...

Harshen ta ta zura cikin bakinshi shi kuwa ya cafke yana mishi shan sweet,saga nan kuma saï aka wuce duniyar ma'aurata....

Saï da komai ya kammala sannan ya rungume ta ya farazolayar ta,yana cewa''dear duk kin gajiyar dani fa yau'',tace''kai honey kai ne fa,ba ruwana, bayan duk ka tsotse min jiki'',yace''ke d'in ce baby wani dad'i naji kin k'ara,wai meye sirrin'' ya kashe mata ido d'aya,

Tace''yaya wane irin dad'i kuma ya akeyi kuke ganewa?",murmushi yayi yace''a haka kawai na gane kin canza kinfi lokacin kina amarya sweet'',dukan wasa tayi mishi a k'irji tace''kai har da tsokana ko?",yace''no gaskiya ce'',tashi tayi zaune tace''ni fitsari nakeji zanje inyi saga nan inyi wanka bacci nakeji'',

Yace''hmm jeki kiyo fitsarin dai,amma wanka saï da asuba dan ban gama ba'',tace''baka gama me ba?",yace''shan zumar dear mana'',wucewa tayi taje ta tsabtace jikinta ta dawo ta kwanta'',yace''wato kinfi son kiyi wanka so biyu Kenan dan ni gaskiya baki isheni ba'',

Kanta ta dora bisa k'irjinshi tace''to naji amma ka bari in huta ko?",yace''naji'',tace''honey gobe in zakaje wajen aiki ka kaini gidan UMMI saï ka wuce,da yamma idan ka dawo saï ka biya ka d'aukoni'',yace''ke da baki da lafiya?",tace''na warke fa yanxu banjin komai'',yace''uhm saboda kinason tafiyar ba'',tace''ba haka bane'',yace''to yane?",tace''na kwana biyu rabona da ita saï dai a waya'',yace''ok Allah ya nuna mana safiya lafiya''tace''ameen'',gami da maida kanta ta kwantar......

*Mentudun mak'iyana n'ai muku kwalo😜*

*'YAR MUTAN KAZAY CE💞*

*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*

*'YAR MUTAN

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...