Skip to main content

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞
( a true life story)

🖊by *_Reefat Yahya_*💞

💦 *Talented writers forum*  💦


*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*

_domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻

_To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com

_dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘

*5&6*

Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai khairat sai yaushe ne zaki daina gudu? Ba na gayamaki banason kina wannan guje-gujen ba? Ki tuna ke fa mace ce ita kuma mace da nutsuwa akasanta ya kamata ki nutsu kisan kin girma hakanan.." Ummi tace cikin fada-fada ta karasa kuma da yima khairat nasiha.. Jikin khairat sanyi yayi taji ta nemi karfin guiwar da tazo da shi na gayama ummi sahibinta zaizo ta rasa.. "Kiyi hakuri ummi insha'Allahu na daina.." "Ai kullum haka kike cewa khairat.. Toh Allah yasa ki daina din." "Ameen!" Kawai khairat tace tayi shiru ta saka ummi a gaba ta kasa gayamata abinda ya kawota wajenta.. "Kinsakani a gaba kina kallo ki gayamin abinda zaki gayamin din mana" ummi tace tana yiwa khairat murmushi ganin yanayinta ya canja saboda tasan halin khairat sarai ba dai bakar zuciya ba abu kadan ne yake batamata rai shiyasa take tayata da ad'dua Allah ya ragemata wannan saurin fushin..  Ganin ummi tayi murmushi yasa khairat itama tayi murmushin a take taji karfin guiwar magana yazo mata tace "Ummi dama Ahmed din nan da nake baki  labari ne yace zaizo gobe kuma ana partyn graduation dinsa dan Allah ki barni naje.." Kara fadada fara'arta ummi tayi tace "Masha'Allah har ya gama karatun kenan ya dawo?" "Eh ummi ya gama dama karo karatu yajeyi a can already yayi karatunsa a Malaysia." Khairat tace cikin son ta kara kuranta sahibin nata saboda tasan halin umminsu sarai mace ce mai son kudi batason a kawo mata mara kudi shiyasa ta dage tanason ta hadata aure da dan yayarta wadda ke auren maikudi amma khairat takiya.. "Masha'Allah Allah yasa alkhairi ya kaimu goben lafiya" ummi tace cikin jin dadi saboda tanason diyarta ta auri miji na kece raini Maikyau da kudi asalima ita ce ta cusama khairat ra'ayin yin saurayi sai mai kudi saboda a cewarta khairat  din matar manya ce.. "Ameen" khairat tace cikin jin dadin ganin ummi ta bata goyon bayan yin soyayya da sahibinta yanzu matsalarta kadai abbah ne..
Dakinsu ta koma ta aje wayarta a gefen gado bayan tayi saving number da sahibin nata ya kirata da ita ta shimfida abun sallah dan yin sallahr isha'i da taji ana kira.. Bayan ta idar da sallah ta haye kan gado ta ja wayanta ta kunna data da niyyar hawan Facebook sai taga message ya shigo da number da tayi saving da "handsome " murmushi khairat tayi na jin dadin ganin sahibin nata yau a WhatsApp saboda ita dama dan shi kawai take hawan Facebook dinnan bata cikason yinsa ba.. "Hello beauty" taga ya turomata.. Ta mayar masa da "Hi handsome" Haka dai su khairat suka cigaba da chatn  a nan yake kara shaidamata da party din murnar dawowarsa da za'ayi gobe yanaso lalle lalle ta halarci wajen fa da fatan babu matsala dai.. "Babu matsala har na gayama ummi kuma ta yarda dama abbah ne matsalar kuma bayanan gobe da safe zaiyi tafiya kuma kwanaki zai yi a can.. Ai dole ne ma na taya Maikyau dinah celebrating din murnar gama karatunsa." Khairat tayi masa reply. "Yauwa shiyasa nakesonki beautynah" yace.. Haka dai suka cigaba da chatn har Islam ta gama duk abinda takeyi taci abinci darenta ta kan haye gadon itama tun tanajin dariyar khairat ko  ihunta sama sama har baccinta yayi nisa ta daina jinta ma.. Dama ita khairat ba ma'abociyar cin abincin dare bace ba hakan yasa ta cigaba da chatn dinta hankali kwance ba tare da ta Ankara ba har 1am tayi hakan yasa suka hakura da chatn din da suke hakanan sukayi sallama maimakon khairat tayi ad'dua ta kwanta sai ma ta saka earpiece a kunnenta ta kunna  waka tanaji.. A haka kuwa bacci ya dauki khairat tanajin waka a earpiece ba tare da ta sani ba..
Wajen 3am khairat ta fara wani irin mafarki mai ban tsoro.. Mafarki take gatanan a farfajiyar gidansu sunata fada da wata irin haliita mai kawuna kusan guda hudu tanaso ta tafi da ita.. Halittar jikinta yanada girma sosai gata da tsawo bata da kyan gani ko kadan ganinta kadai ya isa yasa mutum ya suma.. Gudu khairat take da dukkan karfinta wannan halittar tana biye da ita duk inda tayi har ta kusan cimmata kenan sai ga wasu mutane guda biyu mace da namiji wadanda bata taba ganinsu ba a rayuwarta sun bayyana a tsakanin khairat da wannan halittar suka shiga ganin haka yasa wannan bakar halittar suma tayo kansu gadan-gadan fada ya kaure a tsakaninsu yayinda a karshe wadannan mutane guda biyu sukayi nasarar raba wannan halittar gida biyu da takobi.. Baaat! Gangar jikin halittar ta bace daga gabansu suka nemeta suka rasa hakan yasa suka juya bayansu dan yin magana da khairat amma suka nemi khairat sama ko kasa suka rasa.. Khairat kuwa ganin wadannan mutanen da batasan ko su waye ba sunyi nasarar kashe wannan halittar gudun kada itama su dawo kanta yasa tayi hanyar waje da gudu ta fice daga cikin gidansu tana fita akan center unguwarsu ta hadu da wannan halittar tana kokarina hade jikinta da aka raba shi gida biyu.. Cikin tashin hankali khairat ta fada wani gidan kasa da ta gani a gabanta ya bayyana.. Da shigarta ta nufi wani daki da ta hanga a bude tana shiga ta iske wata mata a zaune a gefen katifa sai zare mata idanu take.. Jikin khairat ne ya hau yin rawa da ganin wannan matar saboda sam ta kasa  yarda da kallon da matar takeyi mata.. Ji tayi an dafata ta baya da sauri khairat ta juya a tsorace dan ganin waye ganin Islam tayi tana mata murmushi "kizo Abbah na kiranki yaya khairat" shine abinda Islam tace tare da jan hannun khairat da tayi mutuwar tsaye a wajen ta kasa motsawa.. Lafiyalau suka fita daga gidan Sam wannan matar batayi yunkurin hana islam tafiya da khairat ba.. Suna fita a kofar gidan khairat ta hango motar abbansu wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyar khairat da gudu ta karasa garesa ta rugumesa.. A lokacin Islam ce da ta tashi dan yin sallahr dare taga khairat sai kyarma take duk ta hada gumi tana wasu irin sabbatu.. Earpiece din kunnen khairat Islam ta fara cirewa sannan ta hau tofamata addu'oi.. A lokacin shima  abbah dake dakinsa yana sallah ya idar da nafilolin da suka zame masa jiki kullum sai ya tashi yinsu.. Addu'o'i ya hau yi yana nemawa kansa tsari da shi da ya'yansa daga Sharrin duk wasu masu cutarwa.. A dai-dai lokacin ne kuma khairat dake mummunan mafarkin nan ta farka daga baccin da take tare da yin wata irin kara ta hau duba Inda take taga dakinsu ne ga Islam nan ma tsaye a kanta.. "Yaya khairat kiyi ad'dua mana ba kara ba.." Islam tace cikin jin tausayin irin rayuwar da khairat ta saka kanta wadda take tunanin shine wayewa.. Ad'dua khairat tayi kamar yanda Islam ta umurceta ta koma bacci Islam kuma ta wuce dan yin alwalla.. Abinda khairat batasani ba a lokacin wadannan mutanen da ta gani a mafarki wadanda suka ceceta ad'duar yar'uwarta ce da ta mahaifinta..

Washegari tun da wuri khairat ta tashi tayi duk abinda zatayi ta gama.. Wajen ummi taje tace mata zataje kitso da kunshi. "Toh kamar nawa zaki bukata?" Ummi ta bukaci sani. "Dubu daya ma ta isa ummi" khairat tace. Kudin ummi ta mikawa khairat tanayi mata kashedin karda ta dade dai tasan yau akwai islamiyya "toh ummi bazan dade ba ma ai duk a gida daya ne za'ayimin" khairat tace ta nufi hanyar fita daga dakin ummi bayan tayi mata sallamah.

Napep ta tsaida ta hau ta kwatanta masa inda zai kaita.. Tafiya kadan sukayi ta kawosu unguwar a kofar gidan da za'ayimata kitson da kunshi aka sauketa ta biya mai napep kudinsa ta shiga gidan da sallama.. Da fara'a matar gidan ta tarbeta tana mata sannu da zuwa.. Bayanin abinda za'ayi mata khairat tayi..  Kunshi aka farayimata bayan angama aka hau tsantsara mata  kisto mai kyau sosai.. Gab da azahar aka gamawa khairat kitso ta wanke kunshinta da ya Bush's kafin a gama kitson dama.. Sallama tayiwa matar ta biyata kudinta ta kama hanyar komawa gida.. Bakin titi ta nufa saboda gidan yayi lungu da yawa babu napep sai an fita titi.. Tana cikin tafiya kawai sai ganin wani mutum tayi a mashin dinsa ya Parker a gabanta yana magana "yanmata minti biyu mana idan babu damuwa" shine abinda mutumin yace da khairat.. Daaam! Gaban khairat yayi wani irin bugawa saboda tozali da mummunar fuskar mutumin da tayi.. Baki ne wuluk da shi ga idanunsa yan'kanana ne jajawur da su kanshi yasha kwalkwali. Tsoro ne sosai ya shigo khairat a lokacin da taga fuskar mutumin nan bata fatan ta kara ganinsa hakan yasa da sauri tayi gaba tana hadawa da gudu gudu tsakaninta har ga Allah tsoron mutumin takeyi amma duk da haka mutumin nan na biye da ita ganin wankin hula yana Neman ya kaita dare yasa ta danne tsoron da takeji na mutumin ta ja birki ta tsaya ta hade fuskarta sosai kamar bata taba dariya ba. "Bawan Allah lafiya kaketa bina haka?" Khairat tace tana hararar mutumin amma maimakon taga ranshi ya baci sai ma washe hakura da ya kamayi ya hau yiwa khairat bayanin kansa da abinda ke tafe da shi.. "Amma ka cuceni wallahi.. Ka kalleni dakyau ni ba sa'ar irinka bace banda ma tsaurin ido irin naku na maza ai da ganina kasan ni din matar manya ce." Khairat tace tana zarewa mutumin idanu.. Murmushi mutumin yakewa khairat tunda ta fara fadan da takeyi kamar ba da shi take ba.. Gaba khairat tayi saboda takaicin wannan wanne irin  mutum ne sai kace bashida zuciya.. Bata gama zancen zucin da takeyi ba kawai taga mutum a gaban ta wani irin tsorata khairat tayi ta ja gefe da sauri gashi lungun babu mutane balle ta samu wani ya rabata da wannan jarababben mutumin.. Har khairat ta kusan kai bakin titi mutumin nan na biye da ita.. "Wai kai wanne irin maye ne? Ka daina bina haka idan har ka cika dan halak ka rabu da ni please... Ko mazan duniya sunkare ni kuwa me zanyi dakai?.." Khairat tace da karfi Wanda har sai da hankalin daidaikun mutanen dake a bakin titin ya dawo Kansu.. Wani irin jajawur idon mutumin ya karayi cikin bacin rai yace "inada zuciya kuma zan tabbatar maki da ni din na cika dan halak.. Kisa a ranki wallahi wallahi sai kinyi danasanin abun da kikayimin ko min daren dadewa ki je zaki gani.. " mutumin yace yana juyawa ranshi a bace ya nufi wajen mashin dinsa yana kokarin hawa khairat ta bashi amsa da karfi ta yadda zai iya jinta. "Babu abinda zan gani sai alkhairi kuma ni bazanyi wani abu ba wai shi da na sani.." Tana gama fadar haka ta hango napep ta tsaida shi da sauri ta shige tayimasa kwatancen unguwarsu..
Dai- dai bakin gate ya aje ta nufi cikin gidansu ranta a bace dakyal ta iya yin sallama a ciki-ciki ta shiga falon aka amsa mata jin muryar bakon da ya amsa mata yasa ran khairat ya kara baci sosai.. "Oyoyo amaryata tun dazu naketa jiranki ummi tacemin ba nisa kikayi ba.." Bakon saurayin yace da fara'arsa. "Ummi sannu da gida na dawo" shine abinda khairat tace tayi wucewarta zuwa daki dan batada lokacin kulasa ita a yanzu tana iya gayamasa abinda har ya mutu bazai manta da shi ba kuma a matsayinsa na dan'uwanta bazataso tayimasa wulakanci haka ba.. "Ke khairat dawo ki zauna" Ummi ta tsayar da khairat dake niyyar shiga daki dan har takai bakin kofa.. Babu musu khairat ta dawo ta samu guri ta zauna.. Gani tayi ummi ta tashi ta shige ciki ta basu waje falon ya rage daga ita sai wannan bakon.. "Ina wuni ya nura" Khairat ta samu tace da shi dakyal saboda wani irin mugun haushinsa da takeji. "Bazan amsa ba sai yanzu zaki gaidani?" "Sorry ya Nura kainah ne yakemin ciwo shiyasa wlh.." Sannu ya hau jeramata dan da nan hankalinsa duk yabi ya tashi.. Tausayinsa taji ya kamata saboda yanda ya Nura yake masifar Sonta babu Wanda yakesonta haka duk cikin samarinta tabbas da ace ya Nura irin mijin da takeso ne da babu abinda zai hana ta hakura da sahibinta ta auri dan'uwanta dan yaya Nura bashida muni akwai kyau dogon namiji ne irin mazan nan da ake kira da giant ga abinda khairat ke so watau naira ta zauna a wajensa.. Yanada hanci dogo kamar biro da idanunsa dara dara da su cikas dinsa daya kawai shi baki ne ita kuma a rayuwar khairat ta tsani bakin namiji Fari takeso ta aura tana bakincikin baki yace yanasonta ma.. "Ko mu tafi asibiti dai khairat dinah kiga doctor?" Yaya Nura yace cikin kulawa "Aa inada magani a daki zansha nagode." Khairat tace tana kokarin daure fuska dan karda ya gano yau daya taji tausayinsa ma hakan ya basa hope din ko zata so shi wataran.. "Toh shikenan Allah ya baki lafiya matas" yaya Nura yace yana kashe mata ido daya.. "Ameen! Amma ya Nura na sha gayama fa babu wannan a tsakaninmu.. Zai fi ka tsaya a matsayinka na dan'uwana saboda banayimaka wani so bayan haka ka daina yimin wani maganan aure please idan ba so kake naji na tsaneka ba... Khairat tace tana mikewa ta nufi hanyar dakinsu ta bar yaya Nura a gurin zaune idonsa har ya canja kala saboda bacin rai a rayuwarsa babu abinda ya tsana irin yaji khairat tace batasonsa yasan har yanzu khairat yarinya ce toh amma ai zuwa yanzu ya kamata ace ta rabu da shirmen samarinta tasan mai Sonta da gaskiya....

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...