💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
07
Kul, larai karki qara fadawa matata, wadannan munanan kalaman malam iro ne yake magana cikeda bacin rai a fuskarsa.
Kuma wallahi a yau sai kinbar gidan larai, idan baki fita ta Allah ba zaki fita ta duka ne, zage2 ta dingayi a tsakar gidan kuma dama zan bar gidan amma ki sani zulai sai kinyi Dana sanin fitar dani a gidannan wannan alqawari ne na dauka.
Shiga daki tayi da gudu ta qunduma wa lami da mejidda ashar, kuzo nan en iskan yara an cimin mutunci amma kuka tsaya kamar ba jinina ba shegu kawai, haba mama kina ganin baba ne a gurin da wallahi sai nayiwa shegiyar yarinyar nan da zulai dukan tsiya lamice take magana cike da bacin rai, yawwa ai dama nasan wataran kina fin wannan shegiyar yayarta ki, haba mama bakisan abinda yake raina ba yasin abinda nayi niyyar yi duk yawuce tunanin ku yawwa yarana dama nasan ku bakwa qyalewa ku tayani hada kaya mubar musu gidan matsiyata kawai.
Bangaren su feenert kuwa daki suka koma suka bar baba a gurin kamar wata gunki.
Da shigarsu dakin feenert ta kuma ce musu dan Allah baba ka fadamin gaskiya nasan bazaka boyemin komai ba na rayuwa. magana takeyi amma fuskar nan sharkaf da hawaye.
Toh shikenan diyata dena kuka yau zan fada miki wacece ke, kwashe duk labarin ta yayi ya fada mata da irin wahalar da yasha a gurin baba, sannan ya Dora da fadin ko da wasa diyata karki zargi iyayen ki akan haka ki fawwalawa Allah lamuranki nasan kina ilimi uwa uba ga tarbiyya dai2 gwargwado munyi miki ita ni da innar ki, ki dage da addu'a Allah ya bayyana miki iyayen ki, kuka ne yaci qarfinsa, sannan ya Dora da fadin kije makarantar ki diyata kiyi karatu banda shiga abinda ba akan karatunki yake ba sannan ki kasance mai biyayya ga malamn ki dama nasan bazaki bani kunya ta nan bangaren ba.
Kuka feenert take kamar ranta zai fita kana tace insha Allah baba baxan baka kunya ba sannan nayi alqawarin cewa bazan dawo gidannan ba sai naga iyaye na, kul daina fadin haka diyata ki dawo idan kun kammala karatu kinji insha Allah zamu tayaki da addu'a har Allah yasa a dace cewar inna da take goge qwallar data zubo mata.
Sallama suka jiyo daga tsakar gida wanda babu tantama ta qawayen feenert ne, inna ce ta amsa musu sannan take tambayrsu suwaye? A take feenert ta shaida muryar minal tace inna qawaye nane to maza tashi kije diyata sannan ki goge hawayen ki to tace sannan ta Kama hanyar fita tsakar gida.
Tana fita minal ta taho da gudu ta rungumeta, sannan daga bisani ta cikata take cewa lafiyar ki qalau kuwa qawata? Feenert ce tace me kika gani, naga idonki kamar kinyi kuka sannan sun kumbura, Hmmm ohhh wallahi kaina ne yake ciwo shiyasa ohk To Allah ya qara sauki, Amin sukace sannan suka gaisa dasu karima.
________________
Yawwa dauko jakarki mu tafi tun dazu muke jiranki, da mukaga baki zoba shine muka biyo baya. To shikenan tace sannan ta shiga daki ta dauko kayanta a nan ma sunsha kuka itada inna kamar ransu zai fita da kyar baba ya lallashe su suka rabu sannan feenert tayi bye2 da garinsu.
__-__-__-__
Tunda suka bar gidan feenert taketa kuka har suka isa makaranta bata daina yiba anyi tambayar duniya tace kanta ne yake ciwo, haka suka shiga mota bata baryin kukan ba.
Minal ce takers lallashin ta amma taki hakura, Hajiya tayi ta barta domin batasan metakeyi wa kuka ba, aranta takeyin maganar batare da kowa yaji ba amma a fili haka tace ki daina kuka mana feenert nasan dole kiyi kukan rabuwa da inna, amma hakuri zakiyi haka Allah ya qaddara, muma fa munyi kukan amma yanxu munyi hakuri dan kanmu munyi shiru, bazaki ganeba minal ni kadai nasan radadin da zuciyata takeyi, to naji kuma kiyi hakuri qawata.
___________________
To naji qawata na share hawayena Na barwa Allah komai, yawwa haka nakeso qawata ( a kullum tana jin dadin kasancewa da minal domin qawace mai hankali da nutsuwa uwa uba ga ilimi da tarbiyya).
Da isarsu gidan sarki wani bafade yazo shi da wani mutum da farin gilashi, gaidasu sukayi sannan suka umarcesu dasu debo kayansu su shiga cikin gidan domin dare yayi sai gobe za'a rabasu ko wanne daki.
Kwasar kayan nasu sukai sannan suka rufa musu baya, basu tsaya ko inaba sai bangaren Fulani wato amaryar sarki.
fatimaauwal1999@gmail.com
Pherteenjeey✍🏻
💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
*Aradun Allah wannan gaisuwar takice ke kadai KIHIYA ina fatan kin sauka lafiya Allah ya bada sa'ar karatu the great (PHARMACIST) hope bazaki dawo 9ja ba sai kin iya dafa tuwon shinkafa saboda OGA yace baya bidarki dawo baki iya girki ba lol* 😂😂😂
*Beelerh mohammed beyllorh heart u baby* 💋❤
08
Da isarsu bangaren, wannan mutum mai gilashi ya kai su wani daki a cikin bangaren, sannan ya sa bayi suka kawo musu abinci da lemuka kala2, kowa yaci abinci amma banda feenert sunyi2 taci taqi ci haka suka gaji suka barta kowa ya tashi sukayi sallah sannan suka kwanta bacci.
______________
Washe gari da sassafe wata baiwa tazo ta tashesu sukayi wanka sannan ta kawo musu karin kumallo suka ci, daga nan kuma ta sheda musu cewa fulani tana sashenta tana jiran su domin zasu shiga makaranta, da sauri2 suka shirya sannan sukabi bayan wannan baiwar, da isarsu sashen suka shiga wani tafkeken rumfa wanda yasha kayan alatu kai daga gani kasan yasha kudi fadar kyawun wannan rumfa bata baki ne, sannan suka shiga can wani dan lungu, daga nan kuma suka shiga wani qaton daki shima dai yasha kayan zamani, sannan suka shiga wani rumfar itama dai tasha kaya amma na gidan sarakai.
Sannan suka shiga wani dan ma dai2 cin daki yasha ado irin na gargajiya, can na hango muku wata mata ta kishingida wanda tasha alkyabba ruwan qasa da ratsin ja ajiki dagowar da zatayi nagan ta kyakkyawa fara tas wadda daka ganta zaka san jinin buzaye ce.
~~~~~~~~~~
Da fara'a ta karbesu, sannan wannan baiwa ta umarcesu su mika gaisu ga wannan mata.
Zubewa sukayi kaf suna gaisheta amsawa tayi sannan ta umarcesu su tashi tsaye, tashi sukayi sannan ta tambayi kowannen su sunanshi, daya bayan suka dinga fada mata sunan su, da aka zo kan *feenert* tace sunana *nafisatu* amma qawaye na ne suke kirana da *feenert* Allah sarki sunan mamana gareki nima daga yau Ammi zan dinga ce miki, murmushi tayi mata sannan daga bisani tace da baiwar nan ta kaisu inna dawakai yake su sami sir Sadeeq shida dogari su kaisu makaranta sannan ki fada musu inason ganin sir Sadeeq idan sun dawo haka kuwa akai ta kaisu sannan ta fada musu saqon uwar gijiyar tata ta dawo.
```````````````````````
su feenert kuwa da isarsu makaranta aka kaisu office din principal, da sallama suka shiga sannan kowannen su ya gaisheshi, interview aka kuma yi musu domin tattance wani aji ya kamata aka kaisu, Alhamdulillah minal ce ta fara cin jarrabawar inda ta samu ajin science, sannan akazo kan uwar gayya wato feenert itama dai nan taci sunyi murna sosae itada minal, sannan akaxo kan karima ita kuma ta samu ajin commerce, sannan sauran qawayen feenert suma an rabasu ajin da sukaci.
Daga nan aka umarcesu su tashi akaisu ajinsu, babu musu suka rufawa dogarai baya aka kaisu, suna shiga kuwa malamin chemistry dinsu ya shigo.
*Kumin afuwa da yau nayi typing kadan hakan ta farune sanadiyyar nasha aiki sosae na gaji ga banajin dadi wlhy so ina neman wannan afuwar luv u oll my fan's*
fatimaauwal1999@gmail.com
Pherteenjeey✍🏻
💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
*Gaisuwar nan takice ke kadai my sahala Dalha Zarewa bisa ga yadda kikeson wanga littafi Allah ya bar so da qauna (er gatan chew 38) ana mugun tare* *~ILYSVM~* ❤❤❤💋💋
*Ina taya duk al'ummar musulmin duniya murnar shiga sabuwar shekara, da fatan mun shiga a Sa'a Allah ya yafe mana kura2n mu wanda muka sani da wanda bamu saniba Amin thumma Amin*
09
......tashi sukayi domin gaida malamin su, amsa musu yayi da hannu, sannan ya basu umarnin dasu zauna, babu musu suka zauna sannan ya fara yi musu darasi.
Tunda aka fara yi musu darasi hankalin feenert baya wajen duk abinda takeyi minal tana lura da ita, Allah2 take ya fita ta tambayi qawarta ta, bai dade ba kuwa ya fita (dama introduction yayi musu coz wannan shine farkon shigar sa class en).
Yana fita minal tace da feenert qawata lafiyar ki kuwa naga kwata2 hankalin ki baya kan karatu ko har yanxu kewar inna kikeyi, murmushi tayi mata wanda yafi kuka ciwo tace Aah qawata kaina ne kawai yake ciwo, to shikenan bari idan mun koma gidan sarki sai na fada a baki magani, to tace sannan suka fita karin kumallo.
Haka suka qarasa zama a makaranta kowanne malami yana shigowa a lokacin sa, sannan da aka tashi Fulani ta saka sir Sadeeq ya dauko su ya dawo dasu gida, suna isa gida suka shiga dakin su sannan sukaci abinci.
Basu dade da gamawa ba wata baiwa ta shigo, tana shigowa tace dasu ana San ganin ku a sashen Fulani, amsawa sukai sannan suka tashi suka bi bayanta.
Da isarsu suka tadda Fulani akan wata kujera tasha ado da kyalkyali, zubewa sukai a kasa suka gaidata, barka da rana, "yawwa barka dai en makaranta kun dawo lafiya " lafiya qlau sukace sannan suka ta umarce su dasu gaida wata mata a gefen ta, gaisheta sukai ta amsa fuskar nan a hade kai daka ganta kasan batada fara'a, sannan suka gaisheda sir sadeeq, daga nan kuma Fulani tace dasu ya kamata yau ace an rabasu ko Sadeeq eh hakane, Ranki ya dade, nuna qawayen su feenert yayi guda uku yace dasu ku kuna bangaren inna maryama, sannan ku kuma wadannan guda ukun kuna bangaren inna dija, sannan da yazo kan su feenert, minal da karima sannan yace ku kuma kuna bangaren fulani, murna ce ta cikasu saboda tunda sukazo gidan babu wanda yaake kula dasu sama da fulani, hamdala sukayi a ransu sannan kowa ya tafi da nashi mutanen.
Tun daga ranar wata qauna ta shiga tsakanin feenert da fulani tanajin yarinyar a ranta kamar er data Haifa da kanta, sakamakon sauran qawayen su feenert da suke shan wahala a sauran bangaren.
Yau ta Kama ranar juma'a tunda safe aketa girke2 a gidan takawa, feenert ce taceda fulani ranki ya dade wai meya faru a gidannan aketa shiri haka, mamana kenan wai banace karki qara cemin ranki ya dade ba, murmushi tayi sannan tace insha Allah baxan kuma ba, to shikenan yau sarki zai dawo daga Egypt shida babban dansa, Allah ya dawo dasu lafiya, Amin fulani tace sannan ta umarcesu dasuyi wanka.
*Kuyi hakuri saboda yau nayi delaying typing wallahi bani da enough charge ne shiyasa gashi yau nepa sunyi mana halinsu, so karku damu Allah ya kaimu gobe insha Allah 2 pages zanyi ina qaunar ku masoyana irin da yawa dinnan* 💕💕💕💕💕
fatimaauwal1999@gmail.com
Pherteenjeey ✍🏻
💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
```I wish u quick recovery my dear momma, Allah yasa kaffara ne```
10
_Suna fitowa ta dauko wata katuwar Leda ta bawa kowa acikin su, gashi wannan nakune dazu na aika a siyo muku duk wani abun bukata na 'ya mace akwai aciki, godiya suka dingayi mata, ita kuwa sai shi musu albarka takeyi, sannan suka bude ledar kayane nagani na fada sun kai Kala bakwai2 sannan kayan cosmetics, Kara godiya sukai sannan tace kowacce ta shirya, kayan suka fara sakawa sannan minal ta fara kwalliya dama gwanace a wannen bangaren sannan tace da feenert tazo tayi mata, Aah feenert tace. Haba ke kuwa qawata dan Allah kizo nayi miki kwalliya mana kinga ni nayi sannan zan yiwa karima to kekadai ce baza'a miki ba duk minal ce take magana cikeda takaici don qawar tata ta fara bata haushi ace kullum makaranta take zuwa taki WAYEWA_
```Fulani ce ta shigo sakamakon maganar da taji minal tanayi Ahh en matana meya farune, hmmm wallahi mama wai feenert ce taki yadda nayi mata kwalliya, to meyasa haka mamana kina ganin minal tayi ga menene ke kuma baza'ayi miki ba haba mamana dan Allah tashi tayi miki kinji, to feenert tace ta tashi fuskar nan a hade dan babu yadda zatayi ne da fulani da minal baxatayi mata ba```
Minal ce ta farayi mata kwalliya ta shafa cen ta murza cen har ta gama feenert batace mata komai ba, wow qawata kin ganki kuwa kamar irin larabawan nan gaskiya kinyi kyau sosae, wannan idan wani ya ganki bazai ce daga qauyen gumel muka zoba, daka mata duka tayi sannan tace to ina wani kyau anan, ungu madubi ki duba ki gani in qarya nake miki, karba tayi ta duba fuskar ta wow gaskiya nayi kyau ba karya amma kinsan meye minal daga kwalliyar ce ba daga fuskar ba, hmmm haka dai kikace kinga tashi nayiwa karima itama kar lokaci ya qure mana, ina wani lokaci zai qure bayan babu inda zamuje, to shikenan dai tashi.
Karima ce tazo itama aka zizara mata tata kwalliyar kai masha Allah gaskiya kunyi kyau en mata na, muryar fulani suka ji daga mirror take kallan su.
Karfe uku dai2 jirgin su ya sauka a kanon dabo motoci sunfi ashirin suka zo tarbar mai martaba tare dansa wato _YARIMA KUMA DOCTOR MAI SUNA AMMAR_
da saukowar sarki daga step din jirgi fadawa sunfi goma suka rufeshi sannan suka dinga fadin gyara kimtsi da kyau, rakoshi sukayi har gaban wata mota kirar zamani baka wulik sai kyalli take kai daga ganinta kasan bata yaraa bace, yarima Ammar ne da mai martaba suka shiga baya sai gaba wani bafade dayake tukasu gefensa kuma waziri ne, motocine kusan bakwai a gaban tasu motar sannan sauran motocin abayan motarsu, tafiya sukeyi cikin nutsuwa duk inda suka gifta sai basu hannu akeyi, tunda ga gate aka shinfida wani qaton kafet mai ratsin ja da fari tunda suka shiga farfajiyar gidan sarki ko wanne gefe gari da dama bayine sunsha ankon doguwar rigar shadda suna watsa furanni masu qamshi.
Har suka isa cikin gidan nanma wasu bayine a gefen hagu da damansu kowanne dauke da kaskon turaran wuta na en borno ko ina qamshine yake tashi, suna isa aka bude musu mota suka fito sannan dogarawa suka lullube mai martaba daga nan suka qarasa dashi sashen inna maryama saboda itace uwar gida.
Hada masa ruwan wanka tayi, sannan yana fitowa wani dogari yazo ya shiryashi cikin kayan sarauta, kuzo kuga kyau a gurin wannan sarki mai tausayi da son talakawansa.
Yana gamawa ta kawo masa abinci yaci sannan ya fita zuwa fada, da isar kuwa fada ta cika dam da mutane kan kujerar mulkinsa ya zauna gefen damansa waxiri ne saai gefen hagu wambai ne sannan ragowar mutanen fada, daya bayan daya suka dinga mika gaisuwa ga sarkin nasu sannan daga bisani mai martaba yayi gyaran murya sannan ya fara da kamar haka, Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala wabaraka tuhu, Amin wa'alaikassalam kowa ya amsawa sarki sannan ya Dora da fadin, Alhamdulillah da Allah ya dawo dani lafiya sannan na qara gode masa bisa ga yadda ya bani lafiya to kusani Allah ya dawo dani sannan zan Dora daga inda na tsaya, nasiha ya dinga yi musu masu ratsa zuciya sannan daga qarshe ya musu sallama ya koma cikin gida.
Yana shiga ya aika jakadiyar sa data kira masa dukkan matansa, Angama ranka ya dade sannan ta fita domin cika umarnin mai martaba.
fatimaauwal1999@gmail.com
Pherteenjeey✍🏻
Comments
Post a Comment