💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
{ ~*Diyar sarki ce*~}
*Talented writers forum*
*(T. W. F)*
*By*
*pherteenjeey*
*Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*
*Gaisuwa ta musamman ga*
*Zarah Ms writer din juyin lamari*
*Maman Fareeda writer din Dan Maliki mai hadarin naira inayi miki fatan alkairi da kammala shi ubangiji ya bada ikon cigaba da (samun wuri) lafiya ILYSVM* 💕
❤❤❤❤❤❤
02
Rarrashin baba ya farayi amma fur taki yadda da shi dole saiya fitar da yarinyar, haka ya fita ya koma dakin zulai ya qirga mata yadda sukai da baba kuka ta dinga yi wiwi hadda majina, hakuri yake bata da kyar tayi shiru yace daina kuka yanxu zan je na fadawa Malam habu idan yaso yazo yayi mata nasiha ko taji
Toh zulai tace ta dauki jaririyar ta Goya ta a baya shi kuma Malam iro ya koma gurin Malam habu da Isar sa ya iske bayanan, ya tambayi mutanen gurin suka fada masa ya shiga gida.
Yaro ya aika yayi sallama dashi yana fitowa yayi masa bayanin yadda sukai da baba, hakuri ya qara bashi sannan yace suje ko zai jarraba tashi nasihar,,,
Suna isa gida suka shige sashen baba tana ganin Malam habu ta washe baki tayi masa sannu da zuwa amsawa yayi rai a sake tayi mai iso har rumfa sannan ta kawo masa ruwa yasha.
Gaisawa sukai sannan Malam habu ya fara koro mata bayani, kamar haka, kamar yadda kika ganni a gidannan baba kinsan alfarma nazo nema a gurinki Dan Allah baba kibar iro ya rike wannan jaririya, kai Malam habu dakata oho zuwa yayi ya fada maka qarya da gaskiya to wannan shegiyar yarinyar ba'a gidannan ba wallhi, haba baba taya za'ai kice mata shegiya bayan ba'a San iyayen taba Malam habu ne yake magan cikeda damuwa a fuskar sa, yooo Malam habu inba shegiya ba wadansu iyayene zasu haifi yayrinya su ajjeta a bola, Aah ba haka bane baba kowa da qaddararsa a rayuwar sa, inajin sato yarinyar akayi aka jefar Dan Allah baba kiyi hakuri kibar yarinyar nan takai shekara goma sha biyar a lokacin tayi wayo inya so sai ta nemi iyayen ta da kanta, da kyar da sidin goshi baba ta yadda, shidai Malam iro yana tsakar gida yana jinsu, godiya Malam habu yayi yasa hannu a aljihu ya fito da Dari biyar ya bata, tana washe hakora ta karba tayi godiya sannan tace dashi ya gaida gida, fitowa yayi suka wuce cikin gida gurin iyalan sa suna shiga larai ta fara bala'i da zage2 to Su Oo ko me ya kawosu aka bibiya anzo munafurcin da aka saba ne ko kulata basuyi ba suka shiga dakin zulai.
Gaisawa sukai Malam habu ya karbi jaririyar yayi mata addu'o'i sannan yace da Malam iro wani suna kuka saka mata.
Sai a sannan suka tuna basuyi mata suna ba, zulai ce ta sunkuyar da kai tace ina Neman wata alfarma Malam a gurinka, wata irin alfarma ce zulaiha fadamin kowacce iri ce indai batafi qarfina ba zanyi miki ita, godiya tayi sannan tace dama sonake asaka mata sunan mahaifiyata.
Farin cikine ya cikasu Su duka Malam habu da iro sai shi mata albarka sukeyi a take a gurin Malam habu yayi mata huduba da sunan mahaifiyar zulai wato *NAFISA*.
Tun daga wannan lokacin rigima take hawa a gidan Malam iro zulai bata da ikon fitowa tsakar gida sai Malam iro yana gida, larai kuwa da yayanta kullum suna qudure da niyyar dauke yarinyar su jefar da ita.
A haka rayuwa taci gaba da gudana a gidan Malam iro dadi da badadi .
Kuma ayau ne Nafisatu tacika shekara hudu cif da haihuwa inda Malam iro ya sanyata a makarantar allon Malam habu, kullum Malam iro ne zai kaita ya dauko ta saboda masifar larai.
*Shin wanene Malam iro*
Malam tukur yana da mata daya mai suna Halima (baba) wadda ta kasance bata haihuwa ga masifa da San abin duniya arashin haihuwar ta ya qaro aure inda ya auri kanwar abokinsa wato maryama, ta kasance mai addini da tarbiyya, Watan maryam uku ciki ya bayyana zo kaga murna gurin ta da mijinta, tun daga lokacin Malam tukur yake bata kulawa ta musamman a dalilin haka ne Halima ta tsani Maryam, haka suka cigaba da rayuwa dadi da rashin sa inda cikin maryam ya tsufa haihuwa yau ko gobe.
Wata ranar alhamis maryam ta Tashi da naquda cikin ikon Allah ta sauka lfy inda ta haifi santalelen yaronta namiji.
Da labari ya iske halima Maryam ta haifi da namiji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu, tun daga wannan rana halima ta tsani maryam da danta, a kwana a tashi babu wuya gurin Allah yau ne sunan maryam inda yaro yaci suna Ibrahim, amma suna kiransa da iro.
Ahaka rayuwa tacigaba da tafiya inda yau Malam tukur ya tashi da shirin tafiya birni domin sayar da wani kaso a dukiyar sa domin yayiwa dansa karatu.
Shiri yakeyi domin ya kusa makara, sallama yayi da iyalansa ya Kama hanya ya fita, tunda ya fita maryam gaban ta yake faduwa.
bangaren malam tukur kuwa yana fita ya wuce gidan abokinsa dama tare zasu tafi da isarsa ya iske shi a kofar gida dama shi yake jira, bashi hannu yayi suka gaisa sanna suka kama hanya zuwa tasha.
Suna Isa suka iske saura mutum uku motar ta cika babu musu suka shiga, sannan suka jira dayan yaxo suka tashi, tafiya sukeyi cikin nutsuwa, tafiya sukeyi babu qaqqautawa sunje dai2 wani junction sai ga wata qatuwar mota ta bigi tasu motar.
Bugar ta keda wuya motar ta kifa ta dinga juyi har saida ta shiga wani daji. babu shiri aka kira ambulance aka ciro wadanda suka mutu wanda suka ji ciwo aka tafi dasu asibiti gaba dayan Su.
*Shin Malam tukur da abokinsa mutuwa sukayi ko rauni sukayi sai kun biyoni zakuji cigaban labarin*
Pherteenjeey✍🏻
fatimaauwal1999@gmail.com
09077726072
4 comment only👌🏻
Comments
Post a Comment