💞 *Nadamar Soyayya*💞
( a true life story)
🖊by *_Reefat Yahya_*💞
💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com
Or visit our Facebook page @ *Talented writers fans*
_dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘
*3&4*
Wani irin kallon rainin wayau khairat ta kama bin yarinyar da shi kawai saboda takaicin abinda yarinyar ta fada.. Wai balarabe? Shiru khairat tayi bata kara yin magana ba har saida malamin dake a first period din ya fita..
Yana fita yan ajin suka hau tambayar khairat ya sunanta? "Khairat" kawai ta basu amsa da shi a takaice.
Surutu yan ajin suka hau yi sakamakon ajin da babu malami a ciki saboda mai second period din baizo ba bashida lafiya..
A cikin hirar ta su ne khairat taji ko mai sunce malam Al-ameen.. Duk yanmatan ajin sunyi group a waje daya ana hirarsa sunata shewa ko wacce tana fadin irin wulakancin da ya tabayi mata. Wasu ma har kwatanta yanda yake acting idan yana wulakanci sukeyi..
Wani irin bakinciki ne ya kama khairat ta ya za'ace mutum yanayi masu wulakanci irin haka amma basuda wani zance sai nasa ai dole ne ma ya daukesu a wasu marasa aji ya rainasu.. Kuma a yadda ta fahimta ma kamar har jin dadin zancen nasa da ake suke mtswe! Khairat taja wani dogon tsoki wanda yayi sanadiyyar maidoda duk hankalin yanmatan ajin zuwa wajenta..
Hararsu takeyi a ranta tace "Kai amma dai wadannan anyi marasa zuciya wallahi."
Wata daga cikin yanmatan da suka rako khairat aji dazu ne ta tambayi khairat da "lafiya?" Khairat ta bata amsa da kanta ne yake mata ciwo.. "eyyah! Sannu Allah ya baki lafiya" dalibar tace da khairat cikin yanayi na tausayawa.. Khairat ta amsa da "Ameen! Nagode." Ganin haka yasa dalibar ta samu karfin guiwar dawowa kusa da khairat tace da ita "ni sunana khadijat ina zaune ne a cikin unguwar nan ke fa kina a wanne unguwa ne?" "G.R.A." khairat ta bata amsa a takaice.. Ganin khairat batason hayaniya da yawan magana yasa dalibar nan ta yanke maganar ta mikawa khairat paper da Biro ta bukaci da ta rubuta mata numbertah please.
Babu musu kuwa khairat ta hau karantoma khadijat numberta tana rubutawa.. "thanks zankiraki da na koma gida." Shine abinda khadijat tace tana mai murmushin jin dadin ta samu karbuwa a wajen khairat saboda ita ma a rayuwarta Allah yayita mai son gayu ce a yanda ta lura kuma kusan halinsu zaizo daya da khairat..
"Assalamu alaykum.." Sallamar malamin last period ce ta katsewa su khairat hirar da sukeyi da dukka sauran daliban ajin ma "Wa'alaykumus salam.." Yan ajin suka amsa ma malamin sannan yaja sit din da malamai ke zama akai dan yin darasi ya zauna ya fara da yin bayanin inda suka tsaya a darasinsu na karshe a sirah sannan ya cigaba daga inda suka tsaya.. Sosai malamin nan ya burge khairat saboda yanda yake bayani dalla-dalla komai dakikancin mutum dole ne ya fahimta..
Tabo Khadijat khairat tayi tace. "Please ya sunan wannan headmaster din naku?" Murmushi khadijat tayi tace "sunansa malam auwal haka yake shi akwai ilimin addini da son karatu amma kuma akwai shi da barkwanci lokacin wasa ayi wasa lokacin karatu kuma abar wasa ayi karatu.." Khadijat ta bawa khairat amsa da har abinda khairat din bata tambayeta ba ma." "Ok Allah sarki ba ruwansa yanada kirki gaskiya.." Khairat tace.
"Eh sosai ma rashin kirki ai sai su malam al'ameen wannan" mtswee! Khairat ta ja tsoki jin ankira sunan wanda ta tsana tun kafin ta gansa.. Khairat tace "wallahi har kunja naji na tsani wannan malam al-ameen din naku tun kafin na gansa ma.." Khadijat ta bude baki da mamaki tace da khairat "wallahi ke ma dan baki ganshi bane ba da sai ya tafi da imaninki ya hadu sosai guyn.." Cikin jin zafin abinda khadijat tace mata khairat tace cikin masifa "Aa kin manta da ruhina gaba daya zai tafi karewar imani.. Dan bakisan kyawon saurayin da name dating bane da baki kuranta kyan wani malaminku ba babana." Khadijat ta bude baki kenan da niyyar mayarwa da khairat amsa, headmaster ya katseta saboda hankalinsa da ya maido a gunsu yana kallonsu a yanzu babu damar yin surutu...
"Ke yar bakuwa ya sunanki ma?" Malam auwal ya tambayi khairat. Ta bashi amsa da "sunana khairat" "ok karanta karatun da nayi maku a yanzu nasan dai a islamiyyar da kika baro kunkai wajen tafiyarsa annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ta biyu zuwa sham ko?" Malamin yace yana mai kallon khairat "eh malam mun ma wuce nan khairat ta bashi amsa.
"Dakyau haka akeso toh bismillah karanatamana nan din malama khairat." Murmushi khairat tayi hade da yin gayaran murya ta fara da bismillah...
Lafiyalau take kawo karatun tana bawa ko wanne harafi hakkinsa a cikin muryarta mai dadin sauraro saboda lura da tayi da malamin nan ya rainamata wayau so yake kawai yayi challenging dinta a cikin mutane..
Ai kuwa sosai khairat ta bashi mamaki saboda yadda yaga yanayinta ya dauka ba za'a samu komai ba a cikin kan nata sai shirme. "Masha'Allah! Barakallahu fikiy.. Kinyi kokari sosai.. Amma bakuwa gobe idan zakizo karda kiyi kwalliya irin haka kamar zakije party dan idan har kika bari malam al'ameen yayi arba dake a haka da irin wannan kwalliyar toh a gaskia haduwar taku bazatayi kyau ba saboda shi mutum ne da babu ruwanshi da duk girman wanda ya karya masa dokarsa ke har wadanda suka fiki girma idan ta kama sukai masa laifi dukansu yake ko ya sakasu wani punishment.. Ina fatan zaki kiyaye ki zama daliba ta gari mai kiyaye dokoki..." Malamin yace yana mai bawa khairat shawara. Murtuke fuska sosai khairat tayi kamar bata tabayin dariya ba saboda jin kowa dai bashida wani zance sai na wannan malam al'ameen din.. Dakyar khairat ta iya furta "toh malam nagode insha'Allahu zaka sameni mai kiyayewa" A ranta kuwa tana maijin babu wanda ya isa ya bugeta a yanzu dai da girmanta haka.. "Madallah" malamin yace sannan ya fara yimasu ad'duar tashi daga islamiyya.
Ana tashi khadijat ta kama hannun khairat suka nufi bakin gate a can suka hadu da Islam tsaye tana jirana azo daukarsu..
Waje suka samu a kusa da Islam suka tsaya suna yin hira basu dade da tsayuwa ba ma sai ga drivern gidansu yazo daukarsu.. A nan khairat tayiwa khadijat sallama ta shiga mota ita da kanwarta islam suka nufi hanyar gidansu itama khadijat nan ta wuce zuwa gida..
6:15pm su khairat suka isa gida, da sallamah suka shiga main parlor din gidan nasu suka tarar da babu kowa a falon hakan yasa suka wuce ciki zuwa dakin umminsu don su shaidamata da dawowarsu.. Sai da sukayi sallamah ta basu izinin shiga dakin sannan suka shiga...
Tana kokarin shimfida abun sallah dan yin sallahr magriba suka sameta... Gaishe da ita su khairat sukayi suka shaidamata da sundawo.. Cikin fara'a ummi ta tamabayesu "toh yaya islamiyyar da fatan dai lafiyalau ko?" "Eh ummi lafiyalau" suka bata amsa a tare. "Toh alhamdulillah haka akeso ai Allah ya taimaka.." "Ameen" sukace tare da yimata sallama suka wuce zuwa nasu dakin dan yin sallahr magriba su ma..
Da shigarsu dakin khairat tayi wani irin tsalle tace "hello sweet room" islam kuma da sallamah ta shiga dakin direct wajen wardrobe ta nufa ta fara neman kayan da zatasaka da sauri saboda har anfara kiraye kirayen sallar magrib.. Khairat kuwa bakin masoyinta mirror taje tana karewa kanta kallo taga komai very neatly bata wani bata kwalliyarta ba.. "Yauwa" shine abinda khairat tace saboda ita a rayuwarta batason ta zauna haka babu kwalliya ko kadan a tare da ita sai dai idan bacci takeyi ne.. Karar wayarta dake a cikin jikka ne ya katse mata abinda takeyi da sauri ta nufi kan gado inda ta wurgar da jikkarta tun a farkon shigowarsu dakin.. Wata sabuwar number ce ke kiranta tagani ashe ma.. Sai da kiran ya kusan yankewa kamar bazatayi picking ba sai kuma ta dauka ta kara a kunnenta tare da cewa "hello" aka amsa mata da "hey khairat khadijat ce ta islamiyyarku wadda kukayi exchanging number dazu" "ok Allah sarki khadijat yakk ya kikaje gida?" *lfylau wlh hup kema haka?" "Yeah haka" khairat ta bawa khadijat amsa. "Ok kiyi saving wannan ne number nah sai anjima naga lokacin sallah yayi.." "Alright bye" khairat tace tana aje wayarta tata a kan madubi ta nufi wardrobe da sauri ta cire uniform din dake jikinta ta saka kayan gida sannan ta nufi hanyar bathroom din dakinsu tayo alwalla tazo nan kusa da Islam itama ta kabbara sallah..
Bayan sun idar da sallah da yan mintoci khairat ta jawo wayarta ta kunna data ta hau Facebook dan yin chatn da sahibin ran nata wanda yake tashe a cikin zuciyarta yanzu.. Tana hawa kuwa ta iske sakonsa inda yake shaida mata da akwai big surprise din da ya tanadar mata zuwa gobe.. Reply tayi masa da "Allah ya kaimu sahibin... Na hau online naga bakanan kuma Nakira layinka na kasar da kake amma baya going ko..." Bata karasa rubuta abinda tayi niyyar rubutawa ba kira ya shigo a wayarta da wata bakuwar number.. Ganin special number ce mai kiran yasa khairat bata wani ja aji ba sosai tayi picking call din tare da fadin "hello! Who's on the line?" Dariya khairat taji me kiran yanayi mata yace "matsoraciya ba dan yankan kai bane ba.."
"Uhmm" kawai zahra tace saboda ta kasa tuna a ina ita ko tasan wannan muryar sai dai muryar tanayi mata kama da ta sahibinta.. Toh amma ai wannan number Nigeria ce shi kuma a yanzu yana a England ne.. "Surprise..! Baby na dawo Nigeria yau ina nan zuwa gobe.." Wani irin ihu khairat tasaka da sai da yasa shi kanshi mai kiran yayi sauri ya toshe kunnensa yace "oh my God! Baby wannan duk murnar ganin nawa ne haka?" "Eh mana sahibin I'm very happy zan ganka gobe wlh" murumushin jin dadi yayi yace "thanks mu hadu online anjima kadan after isha'i"
"Ok see you then" khairat tace tare da yin ending call din gaba daya ta nufi hanyar dakin ummi a guje tana kwala mata kira dan yimata albishir din labari maidadi saurayinta dan kasar wajen nan mai kama da turawa zayazo wajenta gobe..
Islam dake a zaune tana duba wani assignment a a dakin tana sauraren duk abinda ya faru tun dazu tayiwa khairat rakiya da harara tace a fili "Mtswee saurayin social media har wani saurayi ne Allah na tuba kadan dinsu ke da tabbas..
Comments
Post a Comment