Skip to main content

Zumunci

💦 *Talented writers forum*  💦


*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*

_domin samun littattafan mu shiga....👇🏻👇🏻👇🏻

_To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na *Sunhera*

*dedicated to* _*Reefat yahya*_

_dis page is for u , u r d best sisters in d world Anty Fareedah n Anty Zahrah I love u so much Allah accinam Mon_😘😘😘❤❤

*49&50*

Bayan sallar ishah suna xaune a falonta dayake har ynxu be koma bangaren Salina ba sai ya cika 7 days kamar yanda kowa ya sani. Afreen ta juya tana kallonsa ganin hankalinsa na kan TV a hankali ta kirasa" yaya!" Lumshe ido yayi sannan ya juya bangaren da take wato suna fuskantar juna ya kura mata ido , sunkuyar da kai tayi tace " yaya dama cewa nayi yaushe xan koma skul?" Sauke numfashi yayi cikin kasaita ya fara magana
" baby ynxu ko 1 week bakiyi a nan gidan ba shine har kike tunanin komawa makaranta? Toh gaskiya aa ba ynxu ba , sai na ajiye baby na a jikinki sannan xaki koma skul"  ware ido tayi don ta gane manufarsa ynxu ko Kadan baxata iya mishi tsiwa bah ko a banza yafi karfin raini ga kuma wani irin kwarjini da yake mata. Shiru ya xiyarci falon babu Wanda ya sake magana a cikin su sai can Shuraim ya waiga yace " na manta gobe Ki shirya zamu tafi Lagos Jirgin 2 zamu bi" da sauri ta d'aga kanta suka had'a ido ta sauke Shuraim ya share zancen ya cigaba da kallon da yake.

*****

Modibbo ne xaune da iyalansa suna hira cikin nishadi uncle Mohammed ne da uncle Usman sai  iyayen su mata, Suleiman ne ya shigo ransa a bace gaba daya suka xuba masa ido . wata takarda ya ajiye gaban uncle Mohammed yana cewa " dubi irin rashin mutunci da rashin hankali irin na baffa Bukar, wai sammaci ya turawa Baba daga kotu kan zancen raba estate da kuma dukiyarsu ta gado"
  Uncle Mohammed de dama readers kunsan halinshi nan take ya harzuka idanunsa sun kada sunyi Ja sai hura hanci yake yana cewa " ynxu mu xaa ciwa mutunci , gaskiya Baba wannan karon sai de kayi hakuri ni xan dau mataki" murmushi modibbo yayi yace " d'ana kullum ina maka nuni na muhimmancin *zumunci* amma Sam ka kasa ganewa, na horeku da Ku kasance masu hakuri da juriya sannan Ku rike zumunci domin an karbo daga Abdulrahman dan Auf yace yaji manzon Allah (s.a.w) yana cewa : Allah mai girma ( s.w.t) yace " Nine mai rahma, kuma ni na halicci zumunci kuma na cireta daga suna na, Duk Wanda ya sadar da ita zan sadar dashi ( zuwa ga rahmata) wanda kuma ya yanketa zan yanke shi ( daga Rahmata).toh kunga kenan zumunci abu ne daga Allah ba yin mutane bane kuma ba wai al'ada ce bah donhaka ko bayan raina ban amince Ku yanke zumunci da zuriar Bukar bah, haka nan zancen raba estate kuma da izinin Allah zamu raba shi kamar yanda suka bukata nidai fatana akoda yaushe shine hadin kai da zaman lafiya Allah ya bamu iko " gaba daya jikinsu yayi sanyi suka amsa da "Ameen" tabbas modibbo dattijo ne mai hakuri da sanin ya kamata mai kuma tsoron Allah da bin dokokinsa Allah yasa mu gane hakika a wannan zamani mutane suna sakaci da zumunci musamman ma masu kud'i , idan ana da kud'i dai shikenan an manta da sauran dangi Wanda basu da karfi wai kwarya tabi kwarya koh? Toh kowa de ya sani manzon Allah ( s.a.w) yace " duk mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna bah" donhaka muyi kokari mu gyara mu kyautata ayyukanmu Allah yasa mu dace Ameen.

💞💞💞

Salina ta gyara zama tana kallon aminiyar tata tare da tabe baki tace " ke..hmm bari kawai wannan yarinyar ta wuce duk inda nake tunani, shu'uma ce wllhi " tsaki Hafsy ta Ja tare da cewa
  " kedai anyi asara wllhi, a ce kana nan xaune wai miji ya dauki amarya ya wuce Lagos da ita mtsww...ni banga amfanin wayewar taki bah gaskiya baki da wayo"
   "Toh Hafsy ya zanyi ? Ai na fada miki jiya na b'ata masa rai kila da dani yayi niyyan Xuwa amma ya fasa don ya bakanta min" tsaki Hafsy ta sake Ja tare da cewa
     " toh ai sai Ki xauna yaje can suyi holewarsu ya d'ura mata ciki su dawo ke kuma gaki nan ba haihuwan bah" xare ido Salina tayi a yayinda ta ajiye apple dake hannunta Wanda ta kawo ma Hafsy, wani zufa ne ya fara keto mata tabbas idan Afreen tayi ciki a wannan lokacin toh lallai ta gama mallakar Shuraim domin a halin ynxu babu abunda yake so kamar haihuwa.

  Hafsy ce ta katse mata tunani da cewa " wannan mayyar na rasa ma ya akayi ta fito daga wancan gidan da na sa a tsaremin ita"
"Uhmm..nima ai nayi mamakin dawowarta, shiyasa nace da fyade aka mata da yafi min alheri"  " ke dallah can! Idan fyaden aka mata me zai faru? Mijin zai daina sonta ne ko me? Kedai Ki nemi mafita tun wuri wllhi kan ta rabaki da Mijin Ki" Salina kamar zatayi kuka tace
    "Gaskiya bari na kira mom tasan abin yi don am confused"
    "Ahtoh! Kya xauna kiyi saka reshe kama ganye " haka de Hafsy ta cigaba da tunxura Salina tana bata gurbatattun shawarwari ita kuwa kishi ya rufe mata ido sai d'auka take ba tare da yin nazari ko dogon lissafi bah..ahir dinku masu wannan halin Ku tuna akwai ranar hisabi , ke kuma jaka kin baza kunne wai ke mai kawa koh? Tohm a juri Xuwa rafi dai Allah ya tsaremu da sharrin mugaye ka had'a mu da kawaye nagartattu Ameen .

******

Afreen ce kwance bisa katafaren gado dake cikin mansion d'in Shuraim a can Banana island a birnin Lagos masha Allah gidan ya tsaru komai na more rayuwa an xuba a cikin gidan, tun lokacin da Shuraim yake matsayin visiting professor a Lagos university ya seyi gidan babu Wanda ya sani sai iyayensa.
    Wayarta ne tayi kara Ruky ce me kira nan ta d'aga ta kara a kunne " shegiya sai yau kika tuna dani" daga can bangaren Ruky dariya tayi tare da cewa " ni da kiran amare rufa min asiri kar prof ya kaini prison " Afreen tace
" Allah ya shirya ya kk ya gida "
"Lafiya Alhamdllh ya amarci da fatan an gogu" " shegiya ba abunda ya faru toh"
   "Kai friend da gaske? Toh meyasa ?" Tabe baki Afreen tayi daga bisani tace " don rainin hankali ya hanani komawa makaranta wai ba ynxu ba, sannan ya kawo ni wata duniya ya kulleni a gida sai dare yake dawowa yau kwana biyu kenan "

"Wace duniyar ya kai Ki?" " uhmm wai Lagos , yazo seminar ne kome ne oho" wani ihu Ruky tayi cikin jin dad'i tace " girl kice kina kawo wuta kenan , wllhi Ki Kara himma Ki saye zuciyar sa tsab Ki mallake abin Ki" dariya Afreen take tana cewa " wllhi ke Ruky muguwa ce wato ina tausayawa Mijin da zaki aura Allah "
" ahtoh ke Ki xauna kina acting innosy wai kunya.. Toh kiyi wasa wata ta kwace miki shi"
       " wallhi karya ne" dariya Ruky take harda kyakyatawa tace " shegiya ana so ana wani nokewa ga kishin tsiya " haka de suka cigaba da hira cikin nishadi daga karshe sukayi sallama kowacce ta katse kiran.
    Da dare tana kwance ya dawo sannu ta masa gaba d'aya ta rikita shi da kwalliyar ta kananan kaya ne masu daukar hankali shawarar Ruky kenan, dakyar ya saita kansa sannan ya wuce d'aki bayan ya ajiye mata takeaway d'in abinci. Wanka yayi tare da gabatar da sallar isha sannan ya fito cikin shigar kayan bacci

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...