Skip to main content

Feenert

💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
             { ~*Diyar sarki ce*~}

   *Talented  writers forum*
 
      *(T. W. F)*

      *By*
 
*pherteenjeey*

  *Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*


            
              05

....da shigarta daki zulai ta bita a baya, mamana meya faru na ganki kina murna haka, inna bana fada miki zamuyi jarrabawa ba kuma idan mutum yaci za'a kaishi birni ya cigaba da karatu. Eh kwarai kin fadamin diyata, to inna naci jarrabawa kuma makarantar gidan sarki naci, kuma kinsan wani abu kuwa inna, Aah sai kin fada diyata inna ce take magana cikeda mamakin yarta ta, haka aka ce a gidan sarkin zamu zauna inna.

A gaskiya mamana da kamar wuya na barki ki tafi karatu har na tsawan wani lokaci batare da na ganki ba, cewar inna dan Allah inna ki amince mana wallahi zamuna zuwa Hutu gida duk qarshen zangon karatu.

....to shikenan ki bari malam yaxo muji ta bakinsa duk abinda yace dashi za'ayi amfani. Toh feenert tace ta samu guri ta kwanta duk jikinta yayi sanyi dan tasan da kamar wuya baban nata ya yadda tayi nesa dasu, haka ta wuni sukuku babu walwala kamar yadda ta Saba, innar ta duk tana lura da halin da diyar tata take ciki.

Da daddare kuwa malam ya shigo domin yi musu sallama sbd ba'a dakin zulai yake ba, ajjiye musu Leda yayi da malam habu ya Bashi yace ya kaiwa feenert, ya juya da zummar fita, zulai ta katseshi da malam ina son muyi magana, wata magana ce haka zulai da daddaren nan, zayyane masa komai tayi da feenert ta fada mata,  ajiyar zuciya yayi yace da ita ta bari sai gobe xasuyi magana (saboda kar larai ta zargesu) toh tace domin tasan abinda yake nufi sukai sallama ya fita, duk hirar da sukeyi duk feenert tana jinsu sai tayi kamar mai bacci.

Cikin dare feenert ta tashi tayi alwala tayi sallah kamar yadda ta saba duk wani dare sai tayi sallah, sannan tayi addu'o'i masu yawa sannan ta koma bacci.

Washe gari da safe malam yana tashi ya wuce gurin amininshi domin tattauna wannan magana da feenert tazo musu da ita.

Kai tsaye gurin itacenshi ya wuce domin yasan anan zai sameshi, da zuwansa kuwa ya iske shi yana zaune bisa dadduma, gaisawa sukai sannan ya sami guri ya zauna, sannan ya fada masa abinda yaxo da shi.

...To malam iro abinda ya kamata anan shine ka bar yarinyar nan ta yafi karatun ta,  wannan fa dama Allah ya Baku, wata qila a dalilin haka ta samu iyayenta, sannan abu na biu shine yarinyar nan ilimi zataje nema ba wani abinba, sannan idan kana kokwanto akan nafisatu ka daina domin yarinyace mai hankali da nutsuwa ga kamun kai. Shiru malam iro yayi sakamakon maganganun da abokinnasa yayi masa masu gamsarwa.

godiya yayi masa ya koma gida domin tattaunawa da Matar sa.

Da shigarsa gida ya wuce dakin zulai ya samu wuri ya zauna,
Sannan ya kirata ta fito rumfa, Sannu da zuwa malam zulai ce take magana sannan ta debo masa ruwa a kwanon sha. Yawwa zulaiha maganar yarinyar nan nazo da ita, naje gurin malam habu ya bani shawara kuma haka za'ayi, to malam meyace maka, zulai ce take magana dauke da mamaki a fuskar ta.

Fada mata yayi duk abinda suka tattauna akai sannan yace da ita kinga zulaiha abinda nakeji idan auren yarinyar nan yaxo meza muce. Kinsan ko ni da ke mun boye larai da sauran mutane bazasu boyewa wanda yaxo neman auren ta ba.

Sannan kinsan yarinyar nan bata San ba mune muka haife ta ba.

Kawai abinyi mubarta ta tafi karatu ko Allah yasa ta samu iyayen ta acan,  idan kuma ba'ayi daceba sai ta dawo garemu muciga ba da riqeta har Allah ya bayyana iyayen ta ko.

Hakane malam duk abinda ka fada gaskiya ne, amma ka sani ko sau daya banasan mamana tayi nesa dani, wallahi inajin ta kamar jinin jiki na.

Zulai ce take magana tana sharar qwalla, nasan da haka zulaiha wallahi nima banso haka ba, amma ya zamuyi dole mubarta ta tafi.

*(Allah sarki duniya baka sanin ka shaku da mutum sai yayi nesa da kai)*

yawwa wai ina ta tafine, malam ne yake magana domin kawar da zancen da sukeyi akan feenert, Ai malam tana makaranta yanzu ma zaka ganta ta dawo.

Bata rufe baki ba sai suka jiyo sallamarta,  gaishe su tayi sannan ta dubi innar ta tace lafiya naga idonki sunyi ja, Aah babu komai mamana kaina ne yakemin Ciwo, Allah sarki innata sannu kinji amma kinsha magani koh,  ehh inna tace sannan ta tambayi diyar tata yaushe zasu tafi birni karatun.

Laa inna ai mako mai kamawa zamu tafi, toh shikenan diyata maganar da mukeyi kenan da babanki dan har ya barki ki tafi, wani runguma rayuwa innar tata, don murna sannan ta jiyo gurin baban nata tana tayi masa godiya tareda addu'o'i sannan ta shige uwar daki tanata murna.

Malam da zulai kuwa sai mamakin murnar ta sukeyi gaskiya feenert tana son karatu kowannen su magana yake a cikin zuciyar sa.

Tun daga wannan rana inna da malam suke shirye2n tafiyar diyar tasu, kuma a yaune zasu tafi tare da qawayen ta su husna,  Karimatu,  sannan minal.

Tun da garin Allah ya waye feenert take kuka.

fatimaauwal1999@gmail.com

Pherteenjeey✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...