Skip to main content

Feenert

💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
             { ~*Diyar sarki ce*~}

   © *Talented  writers forum*
 
      *(T. W. F)*

      *By*
  ® *pherteenjeey*

  *Dedicated to Islah tee (Mrs. Jameel)*

*Gaisuwa ta musamman ga*

*Dahara Nuri Galadima namcy na inayi miki barka da dawowa da fatan kin dawo 9ja lafiya tnx 4 your support n care luv u lodi lodi Namcy muahh*💋💋💋

            
              03


  Ana isa asibiti aka wuce dasu emergency aka basu taimakon farko. Aka ware matattu aka sakasu a mutuware, Allah sarki duniya sai dai muce Allah ya jiqan wadanda muka rasa ciki kuwa hadda Malam tukur, duniya kenan. acan bangaren masu rauni na hango abokin Malam tukur nace dama shi bai mutuba, ikon Allah kenan, kwanan sa daya yace a sallame shi domin akwai Dan uwansa a cikin matattu Dan.haka zaije ya kai gawarsa Gida a sallace shi.

   Babu bata lokaci aka sallameshi yayi duk wani abu daya kamata yayi ya wuce da gawar abokinsa garunsu.

   Acan bangaren iyalan Malam tukur kuwa maryam da danta sun damu sosae inda halima kuwa ko ajikinta, dan har gidan abokin malam tukur taje akace mata basu dawoba, Ai kuwa tana shirin fita domin takoma gidan abokin mijinta tayi kicibus da shi a cikin gida tare da wasu mutane.

  Ahhh sannun ku da zuwa maryam ce take magana cikeda damuwa a fuskar ta, yawwa maryama ya gida, cewar abokin mijin nata.

   Yawwa ina uwargidan taki take ne??? Hmmm sai dai a duba dakinna ta ko tana nan. Yawwa to duba ki gani ko tana nan,  juyawar da zatayi sai gata nan ta taho.

   Nasiha yayi musu mai ratsa zuciya inda ya basu hakuri sosae akan duk abinda ya sameka, sannan daga bisani ya fada musu cewar mijinsu ya rasu da abinda ya faru da Su.

  Tun kafin ya gama maryam ta zube a gurin ta dinga kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

  Da kyar aka bata hakuri tayi shiru, halima kuwa cewa tayi a ranta shikenan yanzu zanyi yadda nakeso a gidannan Dan wallahi sai zaman gidannan ya gagareki ke da danki.

  A fili kuwa kuka take hadda majina tana cewa shikenan gatana ya qare Malam ya tafi ya barni.
 
   Hakuri aka bata tayi shiru sannan aka yiwa Malam tukur sutura aka kaishi makwancin sa Allah sarki duniya.

  Tun daga wannan rana Halima ta takurawa Maryam da danta batada sukuni ko kadan inba abokin mlm tukur ne yazo ba, shi kadai ne yake taka mata burki takeji.

abincin da zasuci ma gagarar su yakeyi inba shine ya Kawo ba.

  Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Malam tukur inda a halin yanxu iro yanada shekara 27 maryam kuwa kullum babu lafiya iro ya rasa yadda zayyi ga babu abinci ga rashin kudi ballan tana ya kaita asibiti.

  Yau ta Kama ranar lahadi cikin dare maryam ta dinga aman jini ba qaqqautawa kafin gari ya waye Allah ya karbi abinsa.

   Wayyo Allah maraici (littafin zeenasir) shikenan iro ba uwa ba uba sai dai muce Allah ya jikan Maryam yakai rahama kabarin ta.

Da safe kuwa aka shirya ta aka kaita makwancin ta, iro yasha kuka kamar karamin yaro.

Halima kuwa murna ce cike a ranta yanzu burinta ya fara cika saura iro shima ya mutu ta gaje dukiyar gaba daya, *(Dama kafin Malam tukur ya mutu ya hada kaf dukiyar sa ya bawa Maryam sai wadda tayi saura a gurin abokinsa)* da wannan farin ciki Halima ta kwana a ranar, bayan mutuwar maryam da kwana arba'in abokin Malam tukur yazo da mai gari da alqali aka raba dukiya, inda iro ya samu kaso mai tsoka.

  Halima kuwa kamar ta hadiyi zuciya ta mutu Dan bakin ciki.

  Tun daga wannan rana halima (baba) take tarairayar iro kamar danta data haifa.

Samun iro tayi a dakinsa yanata tunani da sallama ta shiga, kai iro meyasa meka kake kuka, laa babu komai baba me kika gani, hawaye na gani yana yawo a idonka.

kadai na kuka haka sannan ka cire damuwa zuwa nayi da wata magana mai mahimmanci a gareka, to baba inajin ki cewar iro dayake gyara zaman sa.

Da zaman da kakeyi iro kayi aure mana jiyar maganar ta doki kunnen sa, toh ni baba wacece zata soni bayan ba gurin kowa nake zuwa ba.

hamdala baba tayi aranta tace faduwa taxo dai2 da zama a fili kuwa haka tace karka damu akwai yar qanwata na yaba da hankalinta sunan ta larai itama bata kula kowa cewar baba.

Iro dai shiru yayi domin baisan mezaice mata ba harga Allah shi baya zuwa gurin wata budurwa sannan kuma bazai iya bijirewa maganarta ba.

  Dago kansa yayi yace babu komai baba na amince da maganarki kije kiyi duk abinda ya dace ayi. zo kuga murna gurin baba burinta ya cika



Fatimaauwal1999@gmail.com

Pherteenjeey✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...