Skip to main content

Feernat

💧💧💧 *FEENERT* 💧💧💧
             { ~*Diyar sarki ce*~}

   *Talented writers forum (TWF) hadin kanmu abin alfaharin mu*

      *By*   
      *Fatima Auwal*
         *(Pherteenjeey)*

*Barka da sallah to ol Muslim umma, Allah ya maimaita mana Amin*
     
      Bissimillahi Arrahman Arrahim

  Ina godiya ga Allah daya bani ikon fara wannan littafin nawa mai suna *FEENERT* Allah yasa mudauki darussan da yake cikin wannan Dan karamin sako da nakeson isarwa Amin

*Gargadi* ban yadda wata ta juyamin littafi ba ko ta canjamin suna ba idan hakan ta faru Allah ya isa ban yafeba wuta balbal.🔥🔥🔥

  *The whole book is dedicated to my best friends, ISLAH TASI'U YA'U ( Mrs. Jameel ) thanks for the support and care ILYSVM* 💞💞
    
  *Gaisuwa ta musamman ga*

*Real khady*
*Faty azlan*
  *Sadiya Smart*
   *Nasiba I uba*
     *Reefat Yahya*

~*Wash hannuna bazai iya rubuto Ku ba ina kaunar Erin totally dinnan*~💋💋💋💋
           
          01

      Kuka naji yana tashi a gefen inda nakeyo ciyayi domin nasaida na samu abinda zanci da iyalina, kasa kunne na keda wuya najiyo kukan jariri, bbu musu na isa inda kukannan ke tashi, da isa ta  na hango wani kwali Wanda acikinsa kukan ke tashi da sassarfa na isa wurin, bude kwalin ke da wuya na hango wata kyakkyawar jaririya fara mai hanci gata da yalwar gashi kayan jikin ta kuwa kana gani kasan na yaran  masu hannu da shuni ne addu'a nayi na dauke ta,

   Gida na wuce da ita domin Samar mata maganin kukanta, da isata gida na wuce dakin zulai Amarya ta, da sallama na shiga na sameta a bakin gado tana kuka, dago idan da zatayi tayi tozali jaririyar da take hannuna da sauri tazo kusa dani ta karbi yarinyar ta bata ruwa tana gama sha ta jijjigata tayi bacci ta kwantar da ita akan gado, Malam aina ka samo wannan jaririya haka xulai ce take tambayar shi cike da mamaki, kwashe labari yayi kaf ya fada mata, hawaye ya gani yana bin fuskarta cikeda tausayi ya matso ya share mata ki daina kuka haka yau Allah ya amshi addu'arki zulaiha, wannan yarinya insha Allah sai ta zama abin alfahari agaremu.

  Insha Allah Malam nayi maka alqawarin cewa zan riketa amana kamar yar da na haifa, Allah yayi miki albarka zulaiha Allah yasa ki a aljanna Amin tace, cikeda murmushi a fuskarta inda sabo ta saba shan addu'a agurin mijin nata, to Malam wani hanzari ba gudu ba kana ganin kuwa cikin gdn nan zasu yadda kuwa, ki daina fadin haka zanyi musu bayani yadda zasu gane to zulai tace takoma kusa da yarinyar, kosuwa ye sukai miki haka Allah zai saka miki diyata Amin Malam yace ya fita, kallon yarinyar take cike da so da qaunar ta.

   Tashi tayi ta fara gyaran daki, fitar Malam ke da wuya yayi kicibis da Larai a kofar dakin zulai, to Annamimi munafuki kaje ka dauko shegiyar yarinya a bola to wallahi tun wuri ka maida ta gurin karuwar uwarta, Dan bazan yadda cewa tsintota kayi ba, banxa kawai daga hannu yayi da niyar marinya sai ya fasa, wani mahaukacin ashar ta luluka masa da ka mareni mana wallahi da ka gane kuranka, banxa Wanda baya iya ciyar da iyalansa sai yayi ciyawa ya siyar.

  Fita yayi domin bazai iya cigaba da jin munanan kalaman ta ba, ke kuma munafuka zaki fitone wallahi na tsaneki shegiya mayya kin mallakemin miji, kuma wannan shegiyar yarinya baxata rayu a gidannan ba larai ce take fadar munanan kalamai ga zulai.

Wuce wa tayi ta shige daki gurin yaranta domin kitsa musu labarin da ta jiyo a cikin gidanna su, kwashe labari tayi kaf ta fada musu lami ce da mejidda suka kunduma ashar wallahi ba'a isa akawo mana shegiya cikin gida ba, yanxu kuwa zamuje mu fadawa baba ta dauki mataki akai.

  Da shigar su bangaren baba suka fada mata karya da gaskiya ai kuwa ta hau tayi fam, tace kubarni da shi sai na dauki mataki wallahi a gidannan za'a kawo min shegiya, bara ya shigo gidan sai ya maida ita gurin karuwar uwarta.

  Fitar Malam keda wuya ya wuce gurin itacen Malam habu abokinsa ya qirga masa duk abinda ya faru Shawarwari masu kyau ya Bashi tare da nasihohi masu shiga jiki sannan ya Bashi hakurin rashin mutuncin da larai take masa, godiya yayi masa sosae sannan ya koma gida.

  Yana shiga larai ta galla masa wata uwar harara tace to kaje baba tana kiranka, bangaren ta ya nufa domin ya iske abinda data fada masa, sallama yayi ya samu guri ya zauna, baba sannu da gida ya rana, mtsww ban sani ba babace take magana rai a hade, inda sabo ya saba rashin amsa gaisuwarta, to naji abinda ya faru iro wallahi tun wuri ka maida ita gurin uwarta bansan musu karka sake shegiyar yarinyar nan ta kwana a gidannan.


*To masu karatu shin baba tana barin jaririyar nan ta zauna agidannan*
   
      Sai kun biyoni zakuji cigaban labarin ~Feenert~

  09077726072
Comments only👌🏻

   Taku har kullum pherteenjeey✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...