*KECE KADDARATA*
*2017*
*Story and written by:*
*Halieymerh Ameen💕*
*T.W.F*
*Page 06 to 10*
Ranan asabar da safe Doctor Faruq yashigo dakinnasu bayan sun gaisa da Umma ya wuce ya duba Abdul bayan ya gama har zai fita seya dawo ya dubi Umma yace "Hajiya ranan Monday idan Allah ya kaimu zaki samu sallama" yafice, a bangare daya taji dadi a dayan bangaren kuma tana tunani halin da zatabar Abdul Ali a ciki.
Tunda yaji abinda Doctor ke cewa yaji jikinsa yayi sanyi baiji dadin maganan ba yanda suka saba yanzu ace zasu rabu.
Habib ne ya shigo dakin bayan sun gaisa da Ummansa ya tambayeta Abdul bacci yakeyi ne ta ce eh, sunacikin hira take fadamasa za'a sallame ta ranan Monday sedai batasan ya za'ayi da wannan bawan Allah da ta sakashi a ranta ba.
Shiru tayi se can tace "Mezai hana mu nema masa sallama shima tunda ya samu sauki idan yaso mutafi dashi ya zauna tare damu har ranan da Allah zaisa ya fadamana wajen da ya fito" "Umma abinda kikeso shi zaayi", murmushi tayi tace "Allah ya maka albarka"
"Amin Ummana bari naje nai masa maganan naga kaman ya farka".
Yana bude ido ya hango Habib ya nufo shi murmushi sukayiwa juna, zama yayi a gefensa ya mika masa hannu suka gaisa
"Abokina ya jiki" ya tambaya,a hnkli ya amsa
"Da sauki aboki"
"Mashaa Allah sannu ko...…....Ammmm Abdul da ni da Ummana muna neman wata alfarma a wajenka ko zamu samu?"murmushi Abdul yayi yace
"Wace irin alfarma kenan ai kunfi karfin komai indai inada ikon muku zanyi"
"Abdul tanaso idan an sallameka mudauke ka bimu gidanmu muzauna tare dakai tunda bakada kowa anan" kama hannun Habib yayi yace
"Aboki kar na daura muku dawainiya "
"Haba Abdul miye abun wani dawiniya karma damu dagani sai Umma ne a gidan sai masu aiki da kanwata itakuma batacika zama ba tana makaranta idan kaqi Umma bazataji dadi ba kaga tana sonka sosai"
"Nagode abokina kacewa Umma na amince zanbiku" dadi Habib yaji dan yasan idan yaqi dole ran Umma zai baci gashi tanada hawan jini abun zaiyi affecting dinta.A ranan Habib yayi wa Doctor maganan sallamar Abdul na ya shaida masa dama ganin bashida kowa ne yasa basu sallameshi ba dan ya riga ya samu sauki,Ranan monday da safe aka sallamesu suka wuce gida.
A cikin yan kwanakin da basu shige 5 ba shaquwa sosai ta shiga tsakanin Habib da Abdul suka dawo tamkar ciki daya suka fito komai tare sukeyi idan kaga basa tare to Habib ne ya tafi wajen aiki ko break yadawo tare sukecin abinci koda yaushe.
*GIDANSU HABIB*
*HAJIYA HAUWA WACCE AKAFI SANI DA UMMA FULANIN KATSINA NE MIJINTA ALHAJI HABU MAHAIFIN SU HABIB YA RASU SHEKARU UKU DA SUKA WUCE YABAR MUSU DUKIYA MAI TARIN YAWA DA COMPANY BIYU,SUNHAIFI YARA GUDA BIYU HABIB DA KANWARSA NAZIFA.*
*HABIB YANADA SHEKARU 28 A DUNIYA YAYI DEGREE DA MASTERS DINSA A GERMANY YANZU HAKA YANA JAGORANTAR DAYA DAGA CIKIN COMPANY SU ME SUNA (H&Ns SHOES AND BAGS COMPANY), NAZIFA YARINYACE NITSATSTSIYA ME SANIN YA KAMATA TANADA SHEKARU 23 TANA KARANTA MEDICINE A CAN KASAR SUDAN TANA MATAKIN KARSHE WATO FINAL YEAR.....WANNAN SHINE TAKAITACCEN LABARINSU.*
*Muje Zuwa.......🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀🚶🏻♀*
*🕯Halieymerh Ameen🕯*
Comments
Post a Comment