*KECE KADDARATA*
*2017*
*Story and written by:*
*Halieymerh Ameen💕*
*T.W.F*
*Page 21 to 25*
Bayan sun gama cin abinci suka koma parlour suna hora ,Abdul dai tunda aka fara hirar baice uffan ba yana rike da carbi a hannunsa yana lazimi.Nazifa ce ta kalli Habib tace
"Yaya next week ma Inshaa Allah ya kamata na fara zuwa asibiti fa"
"Su autan Umma anzama Doctor ayya barka na dai" cewar Umma
"Wani asibiti kenan?"
"Eh Yaya medical centre zanje kuma tare da kai zamuje ko yayana" murmushi yayi
"To shikenan zamuje tare". Abdul dai mamakin surutun Nazifa yake bakinta baya iya shiru ga sakalci ina ma ace shima yanada kanwa nanda nan yaji zuciyarsa tayi masa zugi. Haka suka cigaba da hirarsu sai da lokacin sallar maghrib yayi kowa yatashi zuwa sallah.
Bayan kwana biyu Nazifa na kwance a cinyan Ummanta tana bata labarin makarantarsu, shiru tayi na dan kankanin lokaci sannan tace
"Umma dai baki bani labarin wayene wannan Yaya Abdul din ba har yanzu" kallonta Umma tayi kafun tace
"Meyasa kikeso ki sanine" marairaice wa tayi
"Ayya Umma bansan mutum ba naganshi a gidanmu yana rayuwa a gani na ba laifi bane idan na tambaya ko"
"Ba laifi bane autan Umma".
Umma ta fara bata labarin haduwarsu da Abdul da duk wani abun da ta sani a kansa. Tausayin Abdul ne ya kama Nazifa taji ta matsu taji tarihinsa da kuma abunda ya kawoshi Katsina tunda alamu ya nuna shi ba dan garin bane.
Kullum Nazifa tana cikin jinjina al'amarin Abdul duk tabi ta damu haka kawai take so taga ta kyautata masa wataran idan taga yanda yake zama shiru har hawaye takeyi, koda yaushe tana cikin saqe saqe a zuciyarta tana tunananin yanda za'ayi ta san labarinshi ko zata daina wannan damuwan.
Umma ta lura da chanji tattare da ita gashi kullum se tayi mata zancen Abdul tun tana biye mata har ta daina sabida yanda taga abinnata yana wuce gona da iri ga yanda take shishige masa da son jansa da surutu sedai shidin dama ba mutum ne maison magana ba sedai yana amsa mata jifa jifa yana murmushi wanda yake kara mata kwarin guiwan son zama tare dashi, haka kawai sai Nazifa ta shiga kitchen tayi girki ta kai masa tana zaune yaci koda ya koshi yana iya kokarin sa yaci sabida yaga ta damu dashi bai kamata ya gwasale ta ba.
*(MASU KARATU WAI ME NAZIFA TAKE NUFI NE?🤔 IRIN WANNAN CUSA KAI HAKA🤣🤣🤣🤣🙊........MUJE ZUWA DA SANNU ZAMUJI MIYE NAZIFA TAKE NUFI DA ABDUL-ALI)*
A kwana a tashi Abdul yana rage tunanin *KADDARAR SA*sedai kullum baya mancewa da mahaifiyarsa a koda yaushe zaka same shi da carbi a hannun sa yana yiwa mahaifiyarsa addu'a kuma kullum sai ya zubar da hawayen rashinta domin suna kaunar juna sosai bashi da wanda ya fiyemasa Ummansa a duniyan nan.
*WAI WACECE KADDARAR ABDUL-ALI KUMA MIYE MIYE DALILIN DA YASA YAKE KIRANTA DA KADDARAR SA🤦🏻♀? WAI KODAI BATA DA SUNA NE😲.....OHO😏MU CIGABA DA BIBIYAR ABDUL DON SANIN KADDARAR SA🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀*
*LAGOS*
Bintu tana zama gidan uncle dinta anan Lagos taji dadin zama dasu domin suna debe mata kewar gida sedai ta kasa daina tuna damuwarta kullum tana cikin addu'a Allah ya sada ta da farincikin rayuwar ta,wataran idan suna zaune da Nabila hirarsa kawai take masa har Nabil ma da yake namiji indai suna tare saita bashi labarin farincikin ta.
*🕯Halieymerh Ameen🕯*
Comments
Post a Comment