Skip to main content

Kece kaddarata

*KECE KADDARATA*
     
          *2017*

*Story and written by:*
*Halieymerh Ameen💕*

       *T.W.F*

       *Page 11 to 15*

*BAUCHI STATE*

   *Tuesday morning*
Unguwar G.R.A shiru kakeji kamar babu mutane a unguwar kasancewar sanyi ya fara busawa kowa yana cikin gida yara suntafi makaranta ma'aikata sunfita.

Wani katafaren gida wanda aka kawata shi da furanni masu daukar hnkli securities suna ta kai kawo a kofar gidan da gani kasan gidan wani babban ma'akacin gwamnati ne. Wata babbar mace ce zaune a babban parlourn gidan ta sanya blue lace ya haska ta sosai sabida hasken fatanta da kira me kyau da Allah ya mata sedai na hango damuwa a fuskarta,zaune take dirshan a kasa ta zuba tagumi tana kuka kamar karamar yarinya babu kowa a arean wajen balle wani ya rarrasheta.

Ta share kusan mintuna talatin zaune a wajen taji kara anbude gate din gidan da sauri ta ta nufi harabar gidan, wata 4matic ce tayi parking a daidai wajenda take tsaye sega wani babban mutum ya fito daga bayan motan ga dukkan alama shine mai gidan, a hankali ta karisa gabansa yaja ya tsaya
"Alhaji an sameta?" Ta tambaya,dogon numfashi yaja yanacew
"Muje ciki" gaba yayi tana binshi a baya.

Basu tsaya ba saida suka haura sama dakin Alhaji, a bakin gado ya zauna ita kuma tana tsaye a jikin kofa shiru yayi na dan wani lokaci kafun ya fara magana
"Duk inda ya kamata a duba yarinyar nan anduba amma babu alaman har yan sanda sunyi iyakan binciken su amma basu samu ko alama daya da zata nuna alaman za'a ganta ba yanzu haka daga wajen C.P nake amma bawani labari akanta"  wani irin kuka ta fashe dashi
"Yanzu ka kayauta min kenan ko ka kyautawa yarinyar nan to wallahi ka sani idan yarinyar ta cutu kaine kuma alhaki bazai barka ba akan wani dan iska marar tarbiyya gashi kasa mun rasa yarmu da ita kadai muka haifa a duniyannan"  "Kiyi hakuri nima fa inason yarinyar nan"   a fusace ta dago kai ta kalleshi tace
"So?wannan shine so abunda ka aikata shine so? Ai ga abunda son zuciyarka ya jawo mana yarinya mace ace yau sati uku bamusan inda take ba kuma duk kaine sanadi ka kyauta wa kanka kenan sai kace bakai ka haifeta ba" tana gama magana ta fice ta barshi yayi tagumi da alamu abun ya fara damunsa.

   *BAYAN KWANA BIYU*

Hajiya zaune akan darduma tayi sallah ta idar tana tasbihi a cikin dakinta,Yar aikinta Fa'iza ne ta shigo dakin da sauri ta tsuguna tare da mika mata waya
"Mummy kinbar wayanki a kasa ana kiranki" hannu tasa ta amsa itakuma ta fice, duba waye me kiran tayi sannan ta dauka (Alhaji Abba ne kanin mijinta yana zama a Lagos tare da matarsa da yaransa guda uku Nabil,Nabila da Amma)
"Salamu alayka"
"Amin wa alaiki salam.......Hajjajo ya gida?"
"Hmmmmm gida gashinan dai...baka da labarin yarka sati uku bata gida ba'asan inda take ba ko"   Murmushi yayi yace
"Mugodewa Allah yarinyanya tayi tunani mekyau"    a firgice tace
"Baaan fahimceka ba"
"Tun ranan da *FATIMA BINTU* tabar gida washegari ta taho nan Lagos kuma ta sanardani dalilin da yasa ta taho amma inason jin karin bayani daga bakinki amma ban fadawa yaya ba kema sabida nasan hankalinki ya tashi ne". Hamdala tayi ta tashi daga kan darduman da zauna bakin gado
"Aikuwa nagode sosai wlhy har naji dadin zuciyata"
"Yayata wani hanzari ba gudu ba Bintu ta fadamin yaya ya rabata da Wanda take so sabida bashida wadata ya hadata da Yasir yaronsa, meysa zaki zuba ido haka ta faru yarinya da iliminta da komai za'a cuceta ai mata auren dole ai arziki nufin Allah ne kuma ma tace yaron yanada degree dinsa aiki ne baisamu ba sabida basu da galihu,meysa zakui mata haka har tabar gida ko kun manta itakadai Allah ya Baku"  sauke numfashi tayi tace
"Nayi iya bakin kokari na ya gane amma na kasa shawo kansa, ni nafi tausayin yaron abun takaici ma Yasir ne ya tura aka kashe masa mahaifiya "
"Subhanallahi kuma shi yayan yana gani a haka zai aura masa yarsa kalen itama wataran ya kasheta"     hawayen idonta ta share ta cigaba da magana
"Yana gani se goyon bayansa ma da yayi alokacin da nayi magana masifa ya faramin wai banida hankali"
"Kiyi hkri ki daina kuka hajiya, yanzu shi yaron da takeson a ina yake zama"
"Hmmm tun kwana shida bayan mutuwar mahaifiyarsa Bintu taje gidansu nemansa ta samu gidan a rufe mutanen anguwan sukace mata ai tun kwana hudu da mutuwar aka nemeshi aka rasa kuma bai fadamusu wajen da zaije ba tayita kiran wayansa baya tafiya, yarinyar nan saida tayi kwana biyu a asibiti ni kaina seda na shiga tashin hankali akan zaluncin da akayiwa yaronnan amma su ko a jikinsu sedai kawai Allah ya saka masa,sai yanzu ma naga Alhajin ya fara damuwa"
"Gaskiya yayana bai kyauta ba ko kadan amma kinsan me karki sake ki sanar dashi anga Bintu tunda kince ya damu mu barshi har zuwa lokacin da zaiyi nadaman abunda ya aikata"
"Inshaa Allah bazaiji ba nagode sosai Allah yabar zumunci Allah ya saka da alkhairi"
"Ba komai yanzu sun fita cikin gari da Nabila sunraka Nabil kasuwa a can zasu sayo sabon Sim card idan ta saka zata kiraki amma dan Allah karki bari kowa yasan wajenda take mu samu mu kwato mata yancinta dan wani zai iya sanar dashi kinsan halin mutane"
"Hkne babu meji nagode sosai a gaida mutanen gida". Wunin ranan hajiya batada aiki said duba waya ko zataga kiran Bintu amma shiru sai washegari da safe sukayi waya, hiran yaushe gamo sukayi sosai hankalinsu ya kwanta saidai tunanin su daya basu san halin da yake ciki ba *ABDUL_ALI* .
Haka suka  cigaba day in waya ba tare da kowa yasani ba a bangaren Alhaji duk hankalinsa a tashe yake ya rasa meke mai dai dadi yafita a hayyacinsa sunanan suna bincike kusan kullum  Alhaji Abba seya kirasa yana bin diddigin al'amarin yana nuna masa bai ma san dalilin da yasa Bintu ta gudu ba.





*🕯Halieymerh Ameen🕯*

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...