Skip to main content

ZABIN ALLAH NIKE NEMA

💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
              ~nake nema~

*True life story*

*💦Talented writers forum*💦

          *{T.W.F}*
    
    
*Written by husnah mb*

*🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
   Thanks for ur support All the tym...

*3⃣7⃣-3⃣8⃣*

_To get acces to Talented writer's novel_

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

_Wannan page din kyautace a gareki duba da irin soyayyan da kikeyiwa Wannan novel din* syster. I love You so much dear Allah yabar zumunci_ Ameen❤

*The next day*

6:30pm su affan suka kama hanyan abuja shida nasreen tsawon 7 hours suka dauka suna tafiya kasancewa Affan 'a 150 yake tafiya duk da nasreen sarkin tsoro tana ganin yakai 150 take fara rokonshi har saitaga ya dawo tafiya a 120 hankalinta yake kwanciya.

1:30pm suka shiga cikin abuja" gidan Alh yusuf Suka sauka wato kanin baban nasreen 'shi kuma affan yayan mamansa kenam..."

Hajiya haleema" matar alh yusuf ba karamin tarbansu" nasreen tayi ba ta karbesu cikin mutumci da karamci" Inda aka sauki affan a extra dakin na gida nasreen kuma 'a dakin yaransu _Nabeela da Amnarh_

Koda nasreen taci abinci tana gamawa dakinsu Nabeela ta nufa number naseer tahau dialing ringing yayita yi harya katse baiyi picking bah haka tayita kira har sau 3 tukun ta hakura kwanciya tayi domin ta huta dan gabaki daya ba karamin gajiya tayi bah"

Ta bangaren naseer mah haka yana gama cin abinci toilet ya fada ya watsa ruwa tukun ya fito sallah yayi sannan ya nufi parlour Amnarh ya tarar zaune tana dannna laptop nabeela kuma tana kallo"
  "Cikin fara'a Amnarh tace yaya affan harka fito murmushi yayi tare dace mata na fito wlh ina Lil sis murmushi Amnarh tayi wanda ya kawata fuskanta sannan tace tana daki ok ya fada kawai tare dasa kai ya shiga dakin da Amnarh ta nuna masa.

Kwance ya hango Nasreen saman gado sai sharan baccinta take hankali kwance" tsurawa gashinta daya barbazu da fuskanta ido yayi wani farinciki yaji yazo ya lullubeshi kusa da gadon yazo yana kiran sunanta ganin da yayi kaman baccin natan yayi nisa ne yasa" yadan taba kafanta cikin muryan bacci nasreen tace" yaya naseer lfy kuwa! Naseer kuma? Ya tambayi kanshi jin muryan affan ne yasa nasreen tayi saurin mikewa dan batasan mah ya akayi bakinta ya kira sunan yaya naseer ba"

Tsaye ta sameshi kanta fuskanshi ko alaman dariya babu ga kuma wani kallon da yake mata na tuhuma" murmushin karya ta kirkiro tace bro yaushe ka shigo" waje ya samu ya zauna kusa da ita shiru yayi for almost 5 minutes sannan yace tun dazu na shigo kina bacci murmushi nasreen tayi sannan tace ayya sorry wlh duk na gaji ne murmushin shima yayi yace jita dan Allah waita gaji sai kace wani aiki tayi" Yanzu da kikazo kika kwanta kinyi salla ne lil sis nasanki dason jiki fah murmushi tayi kawai batace masa komai ba dan bayin sallan zatayi bah...."

Affan ne yace lil sis dake nake fah kika shareni. Sosai kai tayi tare da fadin" Uhmm uhm dama murmushi kawai yayi dan ya gane inata dosa" Shikenam to amma sis na tambayeki manah? Ya fada yana kallon cikin idonta
Murmushi tayi tace am all eyes bro" shima murmushin yayi sannan yace meye tsakaninka da naseer ne kam dahar kike kiran sunanshi cikin bacci? Da sauri naseer tace meka gani bro babu komai fah nikam tsakanina da yayan naseer" kawai dai kasan uncle din lesson dina ne shiyasa muka saba sosai" murmushi affan yayi yace to shikenam lil sis kwanta kiyi baccinki gobe xamu fita" da sauri nasreen tace da gaske bro, daga mata kai yayi alaman eh" Yawwa bro ni harkasa na dainajin baccin mah" To lil sis maza zo muje parlour to tace tare da jawo dankwalinta ta sauko daga saman gadon" gaba yayi ta bishi a baya.
   "Su Amnarh suka tarar a falo kusa da nabeela nasreen ta zauna affan kuma ya zauna akan kujeran da yake facing din inda nasreen ta zauna" kallo sukayita yi har saida akayi kiran sallan la'asar sannan suka tashi.

*The next day*

Around 11:00pm Nasreen ta shirya cikin doguwar riganta white nd yellow, Amnarh kuma black doguwar riga ta saka nabeela kuma white nd red din atamfa tasa ba karamin kyau sukayi bah" fitowa sukayi tamkar wasu taurari......"

A falo suka tarar da hj zaune tana kallo Sallama sukayi mata sannan suka fito a parking space suka tsaya suna jira affan ganin da sukayi bashida niyyan fitowa ne yasa" nasreen ta nufi dakinshi.
   Murda handle jin kofan tayi taji a bude kawai saita shiga zaune ta sameshi yana kallo waigowa yayi danyaga wayene ya shigo" ganin yanda lil sis din tashi tayi kyau ne yasa ya kasa rufe baki saida ta iso har kusa da inda yake zaune ya iya cewa _Wow sis kinganki kuwa_ murmushi nasreen tayi tace bro nayi kyau koh daga mata kai yayi alaman eh" kashe masa ido tayi tana murmushi affan ne yace lil sis matar manya kenam yau sai kika fito a matan manyan mutane sak"
     Kelkyalewa da dariya nasreen tayi tace eh ai dama mijina babban mutum ne' yatsina fuska affan yayi sannan yace Oh dama kinada miji ne da sauri tace nifa wasa nakeyi amma nidai nasan banyi kama da matan yaro ba" murmushi affan yayi nasreen ne tace kasan meye kuwa bro girgiza mata kai yayi kawai yana kallonta, Saida ta zauna a kusa dashi sannan tace nifa bazan auri yazo bah" inna tashi aure babban mutum zan aura" Da sauri affan yace to meyasa kikace haka lil sis? Saida tayi murmushi sannan tace saboda yanzu duk macen data auri yaro zakaga auren baya lasting kwana biyu saikaga an fara fada" kuma fah bro yaran yanzu basusan darajan mace bah" Shidai affan sake baki yayi yana kallonta dan tabbas maganan nasreen gsky ne amman kuma yana mamakin yanda akayi yarinya yar 15yrs tasan wayannan abubuwan.

Relaxing yayi sannan yace lil sis amma waya fada miki haka kinsan mutane fah kala kala ne kowa da irin halinsa kuma saikiga wani babba dan 35yr amma yaro dan 20yrs mah yafishi sannnin abunda yakamata" murmushi nasreen tayi tace eh to hakane amma dai ni bazan auri yaro bah shima murmushin yayi yace konima bazaki iya aura ba kenam kelkyalewa da dariya nasreen tayi sannan tace to ai kai bro ba yaro bane kuma mah ai kaikam bazan iya auranka bah" taya zan auri yayana Shiru affan yayi yana kallonta dan baisanma meye zaice mata bah"
   "Shirun da affan yayi ne yasa nasreen ta tuno ashefah tazo sanar masa sun shiryane tazo ta zauna tana surutu" Nasreen ne tace bro su nabeela fah suna jiranmu a parking space dama nazo nacema mun shiryane kai muke jira gabaki daya na manta nazo sai surutu nakeyi
Murmushi affan yayi sannan yace ba dole ki manta bah kinzo sai surutu kikeyi kaman wata parrot" itama dariyan tayi sannan tace sai surutu mukeyi dai' ai bani kadai nake surutun ba ta karisa maganan tana masa gwalo, gwaliyon datayine yayi mugun bawa affan dariya' kedai wlh lil sis ba'a rabaki da abun dariya...' bro mu tafi munbar su sis Amnarh a tsaye fah kasanta da saurin kuluwa yanzu zata fara surutai" key din mota affan ya dauka tare da cewa to basai tayi ba ai duk rashin kunyanta tunda baza tayi a gabana ba' ai aikin banza"

Murmushi nasreen tayi tace bro Amnarh fah batada rashin kunya tanada saukin kai dan nikam muna shiri sosai kaine dai tunda bakwa shiri shiyasa kakega kaman tanada rashin kunya amman da gaske babu ruwanta kagafa Nabeela ce mate dina adda amnarh she's 19 amman kwata kwata batamun girman kai ta daukeni kaman wata mate dinta
   "Dariya affan yayi yace to 19 din nawa take lil sis nidai mu tafi sarkin son jama'a......."

_I heart u all my fans❤_

_Husnerth mb ce✍🏻_

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...