💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfahainmu🤝k'ungiya da'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
_To get access to talented novels check_
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼
💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
💐💐
💐
*ZALLAR YAUDARA*
💐
💐💐
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐
*Based on true life's story*
*Dedicated to Habiba Idrees (hubbey) wolla har ga Allah nima ina kaunarki sosae, Allah ya bar zumunci dear*
Story & Written
By
Pherteenjeey✍🏻
61⚡65
Rannan Abdallah yace da nihla yanaso yazo gidansu gaida Abba, amsa masa kawai tayi amma tarasa yadda zatayi ta fadawa Ummi ta fadawa Abba.
Haka ta yini cikin jimami, dakyar dai ta fadawa Nusy, da yamma kuma Nusy ta samu Ummi a daki da maganar.
Atake Ummi ta amince, da daddare kuma ta fadawa Abba.
Washe gari kuwa nihla Saboda kunya kasa hada ido da Ummi tayi, da kyar dai ummi ta janyota jikinta tace "haba diyar albarka yau Ummin ki kikejin kunya? Saukar da fuskar ta tayi kasa sannan ta Rufe ido.
"wlhy Ummi ba kunyar ki nikeji ba, "menene"? "babu komai ummi.
"Tohm shknn diyar arziki, da karfe nawa zaizo? "bayan magrib yace.
"Toh Allah ya kaimu"
"Tashi kije ku shiga kitchen da babbar yaya, naga time yana kurewa, "tohm shknn Ummin mu.
Bayan magrib kuwa Abdallah ya sauka a gidansu Nusy, dakin baki aka kaisa saida aka dire masa kayan motsa baki sai da yaci abinci ya koshi sannan ya shiga cikin gida.
A parlou akayi masa masauki, bayan wasu lokuta Abba da ummi suka shigo parloun, dauke da junior yanata dariya.
Gaisawa sukayi cikin Fara'a sannan Ummi ta basu waje, Abba ne yace dashi "inason nasan cikakken asalin waye Kai, "Tohm shknn Abba" fada masa cikakkan waye shi yayi sannan yace yana zaune a zooroad da iyayensa.
Yayyansa biu mata Aisha da Fatima, sai kannansa biyar karimatu, muhd, Husna Amina da lil baffa.
"Masha Allah hkn yayi malam Abdallah, sannan Abba ya tashi ya shige cikin daki.
After 3min nihla ta fito, fita sukayi har waje ta rakashi sannan ta dawo cikin gida.
Haka nihla ta kasance cikin farinciki ranar.
*Bayan 2yrs*
Wasu kyawawan gals na gani suna ta tafiya, a hankali kamar bazasu taka kasaba, wani gida nagani sun nufa, zaro ido nayi nace wolla kamar nasan gidan nan, da hanxari nabi bayansu nima muka shiga gidan tare.
"Oyoyo ga babbar yaya da Aunty nihla wani yarone wanda baxaifi 3yrs ba yana magana irinta yara, naga ya fito dg wani daki, mamakine cike a fuskata kaidai ace wadannan Nusy ne da nihla.
Ban gama tunani ba naji ance "kunje gdn su Hanan kun Kai mata ankon? "Eh ummi munje yanxu ma yaya mujahid yace zaizo ya karbi pieces en gidansu wai zasuyi irin namu ankon, "to ai ba matsala Allah ya kawoshi, "Amin.
Suna shiga daki nihla tace "babbar yaya nan da 2month bakya gidan nan koh? "kika sani ko tare za'a hada da naki, "rufamin asiri babbar yaya nida ko kudi ba'a kawoba, Abdallah ma yaushe rabonda muyi waya, "meyasa toh bakwa waya,? Naji frnds enshi sunce wai ya tafi Karin karatu India, tohm Allah y bada sa'a Amin babbar yaya" haka suka dinga fira har bayan la'asar.
Rayuwa tanata tafiya inda yau shekarar Abdallah da tafiya daya da Rabi amma ko sau daya bai taba kiran nihla ba, kuma tashajin Labarin ance ya dawo gari, ko kuma taganshi a fexbuk, gashi wutar sanshi kullum Kara ruruwa takeyi a ranta.
A haka dai nihla ta fara cuta ba kakkautawa inda likita ya tabbatar ta samu (hypertension) hawan jini, ummi tayi tambayar duniyar nan tace ba komai, haka kowa sai ya tambayeta amma shiru.
Bayan wasu kwanaki aka sallameta, akan cewa dole ta rage tunani, haka suka koma gida anata jinya.
Comments
Post a Comment