*KECE KADDARATA*
*2017*
*Story and written by:*
*Halieymerh Ameen💕*
*T.W.F*
*BISMILLAHIR_RAHMANIR_RAHIM*
*Page 01 to 05*
*KING'S👑 CLINIC AND MATERNITY🏥(KATSINA)*
*ROOM 19*
Gadaje biyu ne a cikin dakin,na farko wata majinyaciyar dattijuwa ce wacce zatakai kimanin shekaru hamsin a duniya zaune take ta a bakin gadon da wani kyakkyawan saurayi me mugun kama da ita ne a gefenta yana bata abinci suna hira cikin walwala da alamu ta fara samun sauki. A dayan bangaren kuma wani matashi ne kwance da drip a daure a hannunsa damuwar dake shimfide a fuskarsa da hawayen dake bin kuncinsa basu hana kyawunsa fitowa ba sedai kallo daya zaka masa ka gane yana cikin matsanancin damuwa........
Dattijuwar dake dayan gadon ne ta bi wannan saurayin da kallo tacewa danta "Habib kalli wannan bawan Allan tunda nazo asibitinnan na sameshi kuka yakeyi ko gaisuwa na daga masa sedai ya dagamin hannu yayi murmushi Wanda da kagani kasan na karfin hali ne baya tashi se lokacin sallah abinda yafi damuna ma shinesafe taba ganin kowa yazo wajensa ba se nurses dake zirga zirga akansa ko abinci su suke kawo masa nanma bayaci sedai ruwan tea wannan wace irin rayuwa ce" "Nima na lura da haka Umma dan wataran idan naje ina yi masa hira murmushi nan kawai yake yimin baicemin komai".Tea Habib ya hadawa Umma a cup ya mika mata amsa tayi ta tashi ta nufi wajen wannan saurayin Habib ya bita da Ido.
Zama tayi a plastic chair dake gefen gadonsa ta sa hannu ta dafa kafadarsa,a hankali ya juyo fuskansa yana kallonta "'Da na meke damunka?meysa baka magana?banajin dadin ganinka haka gashi ba lafiya gareka ba ace baka dai aiki se kuka kullum dada lalacewa jikinka yake kayi hakuri kayi magana kaji ko kuma ka kasance me juriya da duk halin da ka tsinci kanka a rayuwa" kura mata idanu yayi yana nanata kalmar da ta fadamasa a zuciyarsa *ka kasance me juriya da duk halinda ka tsinci kanka* wannan itace kalmar da kullum zai bar gida Ummanshi take fada mishi ,Wani abu yaji ya wuce makoshin sa nan take yaji sonta ya shigeshi dan ko bakomai ta sanyaya masa zuciya murmushi ya mata a hnkli ya furta "Nagode" ba karamin dadi taji ba ta mika masa cup din hannunta "Ungo amshi ka sha" da kanta ta bashi yasha seda ya shanye kab tabashi maganinsa yasha ta koma gadonta a haka bacci ya debesa Habib yana gefe yana kallonsu yana murmushi.
Washegari da safe kamar jiya Umma tazo suka gaisa ya amsa mata zama tayi tana masa hira da ta lura hankalinsa baya kanta tace "Yaro ya sunanka"
"Abdul Ali" ya amsa mata "Allah sarki Abdul sannu ko kadinga rage damuwa kaji Allah ya maka albarka" "Ameen" ya amsa, komawa gadonta tayi zata kwanta said Ga nurse ta shigo dubata sai ta dubeta tace "Nurse nikam suwaye yan uwan wannan bawan Allan" a tsanake tace "Hajiya wannan da like gani yakai kimanin sati 3 a asibitinnan, mutumin da ya bigeshi tun randa ya kawoshi baisake dawowa ba gashi shi ba magana yakeyi ba munyi naci har mun gaji amma daga sunansa baisake cemana komai ba abinci ma Doctor ne yasa akebashi a kitchen nanma ba koda yaushe yake ci ba" "Subhanallahi to Allah ya bamu lfya" "Ameen" tana gama abinda take ta fice.
A cikin kwana biyu sabo ya shiga tsakaninsu sosai har shima yana musu hira sosai sunzama abokai da Habib kusan wajensu ma Habib yake yini suna hira sedai har yanzu bai sanar dasu labarinsa ba wajen da ya fito, Umma ta lura a duk lokacin da aka mai wannan tambayan mood dinsa sai ya canja shiasa tace subarshi tukunna har zuwa lokacin da zai fada masu da kansa...........
*🕯Halieymerh Ameen🕯*
Comments
Post a Comment