Skip to main content

Rabon kwado

💞💞💞💞💞💞
*RABON KWA'DO*
*(Ko ya hau sama zai fa'do)*
💞💞💞💞💞💞

*STORY*
        *&*
     *WRITTEN BY:✍🏻*
            *ANTY MAIMOUNATH💞*

*💦Talented Writers Forum💦*
              *💦T.W.F💦*

*Had'in kan mu abin alfaharin mu🤝k'ungiya d'aya tamkar dubu*

_Domin samun litattafan mu shiga....

*To get access to talented novels check*

Hpp://
talentedwritersnovel.blogspot.com/

*Ina mik'a sak'on ta'aziyya ta zuwa ga sister Zulaihat D.ladi,na rashin cousin d'inta da tayi,Allah yaji qanta da rahama ya kai haske a kabarinta,in tamu tazo yasa mu cika da kalmar shahada,ameen!!!*

*DEDICATED TO*
MAMAN AHMAD(ANTY MARDY)KAO'JE
MAMAN FAIRUZA(MOMY NA)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page *45 to 46*

Da safe bayan sunyi breakfast *MUFEDAH* ta kira UMMI a waya tace mata tana nan zuwa gidan ta yanxu,UMMI tayi murna har da ihu take yi zata ga 'yar uwarta dan sun kwana biyu rabon da su ga juna,hmm.....

Saï da *FAROUQ* ya ajiye ta a k'ofar gidan KAMAL zai wuce tace''honey bazaka shiga ku gaisa ba?",yace''no banson inyi late ne idan na dawo ai zan shiga zan bugo miki waya in na samu lokaci inji lafiyar baby na'',ya fad'a yana shafar cikinta,

Hannu tasa ta janye nashi hannun tace''kai honey k'ofar gida ne fa kuma mutane sai su kalle mu'',yace''sai me?, mamata ce fa wa zai hanani ta6aki?",tace''babu'',yayi mata kiss a baki ya shige motar shi ya fice,ita kuma ta shiga cikin gidan.....

Tun daga k'ofar falo take sallama tana cewa sister gani nazo,daman UMMI tana falo dan KAMAL bai jima da fita ba,da gudu tazo ta rungumeta tana cewa''welcom dear sister na,nayi missing din ki sosai wlhy,daman aure haka yake sai a rabaka da 'yan uwan ka?",

*MUFEEDAH* tace''hmm bari kedai sister,amma ni jiya munje gida'',UMMI tace''haba dai yaya ya kai ki ko ke kad'ai?",hararar wasa tayi mata tace''zo mu zauna sannan muji dad'in hirar ko?",UMMI tace''kinyi gaskiya'',taja hannunta suka k'arasa cikin falon nan suka zube bisa kujera....

*MUFEEDAH* tace''nima fa daga asibiti ne muka wuce gidan,kuma sallah kawai nayi muka taxi'',UMMI tace''duk da haka dai kin fini tunda kin ga 'yan gida'',MUFEEDAH tace''haka ne kam'',UMMI tace''waye ba lafiya kukaje ganin shi?",MUFEEDAH tace''nice'',UMMI ta kalleta tace''bakiyi kama da marar lafiya ba,ni wani kyau ma naga kin k'ara kinyi 'yar k'iba,fad'a min meye sirrin me yaya yake baki kinaci?",

Tayi far da ido tace''abin dad'i mana'',UMMI ta kad'a kai tace''hmm lallai kam har da su fari da ido kamar kina gaban yaya'',tace''au na manta ashe fa da ke nake magana'',UMMI ta kai mata dukan wasa tace''kiji ta fa,Allah sister i'm serious kin canza,kuma kince baki da lafiya me sukace yana damunki?",

*MUFEEDAH* tace''a,a ni ma ban sani ba,kawai dai jiya na tashi da zaxxa6i ga jiri da nakeji kuma,saï kwad'ayi da nakeji yanxu ma ki tashi muje muyi d'an wake yaji nakeson ci'',

UMMI kallon ta kawai takeyi,saï da ta gama tace''anya sister ba ciki ne gareki ba?",MUFEEDAH ta kalleta tace''wane irin ciki kuma,a,a ni basu ce mana inada ciki bâ'',UMMI tace''to kika sani ko sun fad'a ma yaya?",MUFEEDAH tace''anya kuwa?,to amma ni yaya bai ce min komai ba,zan tambayeshi idan ya dawo'',

UMMI tace''da yafi dai,dan ni naga kin sauya sosai'',tace''ko yaya ma cewa yake min wai na sauya,kuma da na fiye raki idan ya kusanceni amma yanxu banyi",me UMMI zatayi in ba dariya ba,saï da tayi mai isar ta sannan tace''hmm lallai ma yaya'',MUFEEDAH tace''to to me yaya yayi miki,wai ma me kike yiwa dariya ne?",

UMMI tace''ba komai,ni fa wlhy har yanxu tsoron KAMAL nakeyi,ya fiye naci sosai wata rana fa saï yayi so uku ma,shi kawai bai gajiya,idan nayi magana saï yace min wai so na ne yasa yake min nacin'',itama *MUFEEDAH* a nan ta rama dariyar da tayi mata tace''kai amma KAMAL ya birgeni,ai maganin ki Kenan'',tace''au haka ma zakice,naji,yanxu dai tashi mû shiga Kitchen d'in'',tace''to muje'',suka rankaya zuwa Kitchen.....

Bayan sun gama sun ci sannan suka cigaba da hirar su har 6:30 na yamma,a lokacin ne KAMAL yazo gida,amma *FAROUQ* bai iso ba,su *MUFEEDAH* an cika daman mai jiran k'iris kamar anty m....🙊ban ce ba

Saï kusan 8pm *FAROUQ* ya iso a lokacin suna falo dukan su,yayi sallama suka amsa *MUFEEDAH* kuwa a cikin mak'oshi ta amsa mishi,hannu ya mik'a wa KAMAL yace''ashe kai har ka iso'',KAMAL yace''eh wlhy tun d'azu na dawo na isko *MUFEEDAH* ta kawo mana ziyara,masha Allah mun gode sosai'',

*FAROUQ* yace''nop ai haka akeson zumunci'',ya kalli *MUFEEDAH* yace''dear tashi mu wuce wlhy yau a gajiye nake yau aiki nasha sosai a office'',KAMAL yace''ah haba dai ai ka bari har kuci abinci ko?",

Yace''a,a tafiyar mu zamuyi haka kawai muyi ta zama a gidanku'',dariya KAMAL yayi yace''au haka ne Kenan to shikenan'',FAROUQ yace''karka manta ni fa sirikin ka ne'',yace''naji dai'',

Har bakin mota sukayi musu rakiya sannan suka koma ciki,FAROUQ yaja motar suka fice.....mutuniyar tashi kuwa ko inda yake bata kalla ba,a ranshi yana cewa nasan za'ayi haka daman,hhhhh

Saï da ya biya wani restaurant yayi musu *take away* sannan suka fice gida....ko da su ka isa bud'e k'ofar motar tayi ta fita ba tare da ta waiwaya inda yake ba tayi cikin gidan ta bud'e ta shiga,kai tsaye bedroom d'in ta ta shiga ta fad'a bisa gado saï ta fashe da kuka,toh fa ikon Allah....

*'YAR MUTAN KAZAY CE💞*

*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...