🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖
*AMANAR RAYUWA TA*
_{A very short and interesting story}_
🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖
*Na*
*_Sadieey Smart_*
*_⚜Talented Writers Forum⚜_*
_~Bismillahir Rahmaanir Raheem~_
*Godia*
~_Dukkan godia su tabbata ga Allah wanda cikin yardar sa da amincewar sa nake wannan rubutu, Ina kuma rokonshi da ya taimakeni wajen ganin na fara lafia na kuma gama lafia duk wani mai niyyar sharri gareni Ya Allah ka maida masa gareshi_~
*Jinjina garemu Online Writers hakika muna namijin kokari wajen ganin mun isarda sako har izuwa inda mu bamu taba tunanin zuwa ba to 'yar uwa/Dan uwa ku sani ta wannan hanyar pa wani/wata na iya shiryuwa ko akasin haka.*
_To Writers please muyi k'ok'arin ganin mun rubuta alkhairi don ganin bamuyi da nasani ba anan gaba_
*Na sani kin sani cewar shi Marubuci mak'aryaci ne,wanda a kullum yake rubuta gaskia da kuma fad'ar ita kanta gaskiar ta hanyar amfani da tashi basirar*
*_Shin bazamuyi tunanin cewa ba kowa bane Allah ya mallakawa wannan baiwar ba? Shin mu da muka sami dama ba Allah bane ya bamu ko kuwa tamu dabarar ce da ta zarce ta kowa?, Meysa bzamuyi amfani da Baiwar da Allah ya bamu ba wajen isar da saqon Allah,wajen ganin mun godewa Allah a bisa zaban mu da yayi cikin d'umbin al'ummah?_*
_~Marubuta ina k'ira da babbar murya muji tsoron Allah mu kar garin neman gira a rasa ido,muyi kokari wajen ganin mun kiyaye hannuwan mu daga rubuta abinda bai dace ba domin idan har ka yad'a bad'ala to tabbatar cewa daga nan zuwa zamani goma duk Wanda ya aikata wani mummunan aiki ta dalilin abinda ka rubutu ko da baka raye sai ka sami taka kamishon sbd haka mu farka daga duniyar rud'un da muke ciki na ganin in baka rubuta wani abin badala ba ba zaka sami fans ba wannan Sam ba haka yake ba please mu gyara~_
*Gargad'i*
_Ban yarda wani/wata ya canza min salon lbr ba nawa ne kuma mallaki na ,yin hakan dai2 yake da sata kuma shine abinda ban yafe ba so akiyaye_
*Tsokaci*
*_~Duk wani/wata wanda lbrn nan yayi dai2 da rayuwarshi akasi aka samu all the story is based on Fiction and Fictitious~*
_Shafin farko naku ne frnds forever_
*Zainuddeen Zain*
_Faty Afreen_
*Cwt Jiddah*
_Action Bae💥_
*01~05*
Yau sun tashi gidan sai shirye2 suke da alamu tafia zasuyi don naga sai harhad'a kaya suke musamman wata budurwa wacce take ta sauri ta had'a wannan ta had'a wancan
Wani mutum wanda ga dukkan alamu mahaifinta ne yayi murmushi "Haba Anty *Janaan* wannan saurin pha duk yinki sai k'annenki sun dawo daga schl kafin a tafi _why d eagerness_?"
Murmushi itama tayi sai kuma ta turo baki alamar shagwa'ba "Allah Baba ni am eager mu ne tafi wlhy sbd kasan yadda nake son zuwa garin nan kamar yaya I feel like flying kawae in ganni can".....
Yayi daria "Oh ni kaina nakan zauna wataran inyi tunanin meysa kk son garin *Jos* sbd ke naga baki k'i ma mu koma can da zama ba"
"Allah Baba ina son *Jos* fiye da tunanin mutum ko May be sbd can aka haifeni ne oho"
Wata macece ta k'araso wajen da ganinta kaga bafulatana fuskar ta d'auke da murmushi
"Oh ni wannan wane irin Baba ne ana aiki sai ya tsare d'iya da surutu, kuma kai in anyi magana kace baka son tafiyar dare amman baka bari mu gama shiri"....
Ta maida dubanta ga yarinyar "ke kuma da zaran yy magana sai kizo ki zauna wai ku kuna lbr duk shiyasa kuka maidashi kaman kakan ku wlhy"
Kallon juna yarinyar sukayi da Baban nata sukayi murmushi ya mik'e yana shirin fita waje tace "Laa Baba ka kira *Nass* kace ya kawo min dinkunan mu yace ya gama gogewa yake, kuma Baba wannan atamfar da jiya ka siyo mana na bashi ya d'inka sbd you promise me in muka dawo zaka kaini *Yola*"
Ya ce "toh naji je ki karisa aikin ki In Sha Allah da kin dawo zamuje Yola hankalin ki ya kwanta".....
Da murnarta ta juya harda doka tsalle kamar wata yarinya nidae ina mamakin k'aunar da mahaifin nata ke mata ko mgn zai mata cikin murmushi yake yinsa alamun yana son ganin ya faranta mata to ko haka yake wa sauran yaran? Maji ma gani ........
*1:20 pm*
Yara ne guda biyu sukayi sallama mace da namiji sanye da uniform d'in makaranta mai kalar *Green&Milk* namijin na sanye da green *Cardigan* macen kuma ta d'aure nata a k'ugun ta Schl badge dinsu na kalla an rubuta *_Imperial International College Bauchi {I.I.C.B}_* a hanzarce suka shigo gidan suna jin muryar *Umma* suka sauk'e ajiyar heart sai kuma suka kalli juna suka fashe da daria suka ce
"Umma ina yini"
"Lafia qlau kuzo maza kuci abinci kuyi wanka kunga ku muke ta jira".
Da hanzari ko wanne ya nufi kitchen suka d'auko food flasks d'insu suka zauna ci a nutse, yayarsu ce ta fito daga d'aki tana sanye da Hijab da alamu sallah ta idar suka had'a baki wajen fad'in
*"Anty J* sannu da gida"
Ta wani sha murr "dallah kuyi sauri shi wannan principal din naku d'an iyayi saida nace mishi yau bazakuyi lesson ba ya barku ku dawo amman yak'i mtsw"
Daria suka kwashe dashi har *Umman* tasu namijin wanda da alamu shi ke binta yace "ji wannan matar kin manta 2pm muke tashi ne kafin mu shiga lesson? to dan ma ya barmu daga yin sallah yace muzo mu tafi shine kk k'unkuni sannu hajiya zumud'i"
"Kai ina wasa dakai ne? Wlhy ynx zansa ka fasa tafiyar nan kowa ya huta"
Suka sa mata daria ya ce "oho ta haushi taxooo" ya mata gwalo ai kuwa sai ga hawaye wanda yy dai2 da shigowar Mahaifinsu
"A'a mutan Jos ya da kuka kuma zaki 'bata kwalliyar ki, ke d waye kuma"
"To *Baba* ba *Na'eem* bane ke tsokana ta kuma *Umma* tana kallonshi har tayashi daria take"
'Bata rai yayi "ni pha banso ake taba min yarinya kai kuma wlhy kana daf da fasa tafiar ka don wlhy baza kaje can kana mata rashin kunya cikin mutane ba _so u hv 2b vry careful_"......
Shiru *Umma* tayi ta wuce zuwa d'aki shi kuwa *Na'eem* mikewa yy yakai kularshi kitchen ya shiga wanka ita dai k'aramar tasu bata cewa komai don daman tasan za'ayi haka shiysa bata sako baki ba sai dai tayi daria.......
"Wuce kije kiyi wanke2 kafin su shirya wawiya kawae kedai kinji haushi wlhy,baki ta'ba jin dad'i sai kin hada wani da Baban ki ya mishi fad'a... Hmmm shi kuma yaci gaba da haka bazai san gaba yake shirin hadawa ba sai nan gaba"..........
"Kiyi hkr *Umma*" kawae ta fada ta fice zuwa abinda aka sata
3:00pm
Suka fito mai *Keke napep* na jiransu a k'ofar gida sukayi sallama da mahaifinsu kan sai gobe zai taho d'aurin aure tare da Yayyensu maza. Nan ya baiwa kowa kudin kashewa amman na *Janaan* yafi na kowa...........
Har suka isa tashan *Jos* wanda ke kwanar asibitin koyarwa na *ATBU* bb wanda ke kula *Janaan* mai chocolate ta gani tana son siya amman yana tsallaken titi dak'yar ta lalla'ba *Na'eem* ya fita ya siyo mata *Roxy,Cocos,Honey sweet,wafer~stick* da sauransu. *Meenerhl* ce ta kalleni "frnd kinga wata mayyar chocolate irinki"
Nace "hmmm wannan ai nata wasa ne" mukayi daria muka juya sai gani mukayi motarsu ta tashi
Cizon yatsa nayi "dallah can garin gulmarki kin sanya na rasa d'auko rahoto"
Daria tayi "to maida wuk'ar ga wad'ansu kud'i a purse dina jiya *Badaru* ya bani mu shiga mota kawae mu bisu ai naji sunan unguwar da zasu je *Dogon k'arfe* ne wai gidan *AB Ralla* "
"Kinga daga nan sai mu ziyarci *cwt Afreen* dina"
Take muka shige mota sai garin *Jos*
Duk mai son jin lbr ya biyoni garin *Jos* fans akwae chakwakiya anan gaba...........
*Smarty ce*💞
Comments
Post a Comment