💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
_To get access to our novels check_
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na _*Sunhera*_
*dedicated to* *_Reefat yahya_*
_manzon Allah (s.a.w) yace_... " *Mai yanke Zumunci ba zai shiga Aljanna ba*"
~'yan uwa mu rike *Zumunci* gam gam~🤝🏻🤝🏻
*43&44*
*12:40am* karfe d'aya saura minti 20 Afreen taji alamar bud'e kofa a firgice ta tashi xaune carab! Suka had'a ido da wannan matar cikin rad'a matar tace "zoka tafi kar su kama ka" cikin hausar ta irin na Igbo nan ta rike hannun Afreen tafiya suke a hankali ga tsananin hasken farin wata , wata yar karamar kofa ta hango a bud'e matar ta nufa Afreen na biye da ita har suka fice basu had'u da wani bah. Gudu2* sauri2* haka suke tafiya har sunyi nisa sosai da gidan sun share 20 mins suna tafiya sannan matar ta tsaya sai haki suke tace " a nan zan barka Ka cigoba da tofiya before den zan Baka phn ka kira mamanka yazo ya sameka a bakin road OK"
Kai Afreen ta gyada don gaba daya a tsorace take nan matar ta fidda wata yar karamar itel ta mika mata " oya call ur mama tel am say make her come n pick u for bambam side along A.y.m shafa oil hury " cikin rawar jiki Afreen ta karba tayi dialling num mami har ya katse baa d'aga bah, haka ta sake kira har sau 3 no answer nan ta kira layin Abba bugu biyu yayi picking tare da sallama cikin muryar kuka tace
" Abba nice ,Abba ka taimaka kazo ynxu ka d'auke ni" nan ta kwatanta masa yanda matar ta fada mata, a rude Abba yace " toh..toh gani nan Xuwa" he can't bliv dat Afreen ce nan ta kashe wayar ta mikawa matar tare da yin godiya.
Matar tace " no problem my dota u can go now ynx zan trowing sim d'in don kada a gane cewa ni na taimaka miki, hurry up n run" Afreen tace " wat about u?" Murmushi mai sauti tayi tare da cewa " don't worry about me just go dats my life, go safely my dota " nan ta rungumi Afreen tare da kwatanta mata hanyar da xata bi daga nan suka rabu.
Guduwa take tamkar ranta ze fita tayi gudu mai dan nisa sannan ta hango gidan man A.y.m shafa can ta nufa duk da cewa akwai hasken farin wata amma hankalin ta be kwanta bah, a gefen ginin ta rakube sai xare ido take bayan kamar minti 30 ta hango mota na Xuwa har ya karasa dai2* gidan man mutum ne ya fito yana waige2* a hankali tace " Abba Nah" nan ta fito daga inda take tana sauri ta kirasa
"Abba nah*"
Yayi saurin juyowa nan suka kankame juna " kina lafiya ko ya'ta, dafatan basu tab'a min ke bah, su wanene suka aikata harkan"
Cikin muryar kuka tace " Abba mubar nan kar su samemu " babu gardama mota ya bude mata ta shiga ya Ja suka tafi.
Hankalin mami a tashe yake sai safa da marwa take cikin falon gashi taso Xuwa amma Abba ya hanata ina kam a tsorace take Kar wani Abu ya faru dasu, tana cikin wannan tunanin sukayi sallama lokacin karfe 2 da mintuna Afreen ta fada jikin mami suka kankame juna sai kuka suke Abba yace " godiya ga Allah zamuyi ba kuka bah " nan suka xauna a falo mami ta kalli kayan jikinta tace " muje kiyi wanka Ki huta koh"
Afreen ta mike suka haura d'akin ta nan aka had'a mata ruwan zafi ta shiga ta fara dirje jikinta rabon yaushe tayi wanka...
Kaifin ta fito mami ta dafa mata indomie da kwai sai kuma tea me kauri ta ajiye mata, Afreen tana fitowa taga abinci aikuwa tahau ci sai da tai nak ta kora tea sannan ta bud'e wardrobe ta d'auko wata Riga Mara nauyi ta sanya tare da mikewa bisa gado cikin kankanin lokaci bacci yayi gaba da ita. Mami ta shigo d'akin ganin bacci take ne yasa ta Ja mata bargo tare da kunna mata Ac sannan ta Ja kofa ta fice.
Washegari...gidan ya cika da 'yan uwa da abokan arxiki sunzo taya mami murna domin ta buga waya ta sanar da kowa ga mamakin kowa yau modibbo Tukur da kansa yazo gidan mami Wanda tunda tayi aure be tab'a Xuwa bah , lallai Afreen y'ar gata ce gaba da baya don en uwan Abba ma sunzo ga gidan de a cike mazan na falon Abba a yayinda mata ke bangaren mami.
*10:15am* Afreen ta tashi jin hayaniya da hira a falo ne yasa ta dora hijabi akan doguwar rigar dake jikinta, toilet ta shiga tayi brush dama tun bayan sallar asuba ta koma bacci sai ynxu ta tashi ta wanke fuska tare da goge baki sannan ta wuce Xuwa falon. Har rige-rigen rungumarta su zee suke ga yan uwa dai nan suka jajanta mata, sadiq ne ya shigo ya sanar da ita modibbo na son ganinta yana can falon Abba kowa a falon yayi mamaki da jin cewa modibbo yazo da kansa nan ta tashi ta fice.
Falon na cike ga modibbo, Abba,, uncle Mohammed, uncle Usman ,uncle Suleiman, uncle Abdulrahman , Saleem, Shuraim da dai sauransu sai kuma dangin Abba da abokansa dakyar Afreen ta gaishesu modibbo sai murmushi yake nan suka fara tambayar ta ya abin ya faru, ta kwashe labarin komai ta sanar musu modibbo ya jinjina kai tare da cewa " Allah ya tsare na gaba " gaba d'aya falon aka amsa da "Ameen" uncle Mohammed yace
" ynxu zaki iya gane gidan "
Kai ta girgiza masa alamar aah:ahh.
Modibbo ne yace " kar a tsananta bincike tunda ta dawo lfy Alhamdllh, Wanda suka shirya tarkon su suka sani da Allah donhaka abar maganar " " amma baba da de an nemosu an mika su ga hukuma zai fi" murmushi yayi yace
" a'ah d'ana mu barwa Allah ranar gobe shi zai mana hisabi "
Uncle Mohammed baiso hakan ba amma babu yanda ya iya dole su hakura. Afreen ta fice daga falon babu kunya Shuraim yabi bayanta Saleem kuwa haushi yaji amma ba yadda zaiyi sai hakuri.
"My baby!" Ya kirata cikin wani irin romantic voice cak! ta tsaya cikin zuciyarta kuwa cewa tayi "tohfah sabon salo kenan" a hankali ya karasa inda take ba tare da shakkar wani Abu ba ya rike mata hannu a hankali suke tafiya ga mamakin ta bangaren bak'i ya nufa da ita kai tsaye, suna shiga falon ya jawota ya kankame wani irin rungumarta yayi tamkar wani ze kwace masa ita sai ga Shuraim yana hawaye😪 har ya ban tausayi. Shiru Afreen tai tana jin bugun zuciyarsa sai kuma tausayinsa ya kama ta nan itama ta sa hannu ta rungume shi, sun share 10 mins sannan Afreen ta xare jikinta daga nasa zama sukayi bisa kujera ta sunkuyar da kanta kasa
" baby me suka miki?"
"Basu min komai bah" " kin tabbata?" Kai ta gyada masa , dogon numfashi ya sauke sannan yace " gaskiya nayi kewar Ki ba kad'an bah baby I rily missed u " tsigar jikinta ya tashi don yanda maganar cikin shauki . bata ce komai bah har ynxu ta kasa kallonsa shi kuwa ya kura mata ido kamar maye sai kuma yace " pls my baby kice dasu mami gobe zaki koma gidan Ki pls, wllhi I rily need u" da sauri ta d'aga kai tana kallonsa yace
"Yes da gaske nake "
Shiru tayi har ynxu ganin bata da niyyar magana ne yasa Shuraim dawowa kusa da ita, batayi aune ba taji ya cafke bakinta ya fara kissing gaba d'aya jikinta ya mutu .sallama suka jiyo daga waje Afreen tayi saurin tureshi gefe kanta na kallon kofa dakyar ta amsa muryar ta na kyarma Shuraim kuwa sai faman lumshe ido yake yana murmushi, zee ce ta shigo tace
" modibbo nason ganin Ku " "OK gani nan Xuwa Afreen ta amsa daga nan tayi saurin bin bayan Zee tsaki Shuraim ya Ja sannan yabi bayansu Xuwa falon Abba.
Gyaran murya modibbo yayi sannan ya fara magana " Alhamdllh godiya ta tabbata ga Allah ( s.w.t) daya bayyana mana Aisha cikin koshin lafiya, ya Allah ka kara tsaremu da zuriar mu baki d'aya albarka darajan annabi (s.a.w) "
Gaba d'aya falon aka amsa da "Ameen " sannan ya cigaba da cewa
" tunda Allah yasa ta dawo lafiya ni ina ganin babu amfani wani biki ko taro donhaka gobe in Allah ya kaimu sai ta shirya ta koma gidan Mijin ta" murna gun Shuraim da iyayen sa baa magana haka ma iyayen Afreen, modibbo yace " Shuraim gobe ka shirya nazo ka tafi da matarka Allah ya tsare gaba ya Baku zaman lfy" "Ameen aka sake amsawa" daga nan ya dora da nasiha sannan ya musu sallama har mota aka masa rakiya cike da girmama wa daga nan ya wuce gida.
Afreen ta koma d'akin ta zee da Afra suka kalli suka fashe da dariya Afra tace " ana so ana kai kasuwa " banza ta musu ta fad'a gado tare da fara danne2* a wayarta haka suka cigaba da tsokanarta amma taki kulasu , haka dangin suka cigaba da Xuwa suna taya mami murna har dare sannan suka watse.
Da dare mami ta ajiye Duk wata kunya tayiwa y'ar tata Nasiha me ratsa jiki tare da abubuwan da suka shafi aure daga nan ta bata magunguna masu inganci sai kuma suka shiga gyaran jiki , basu kwanta ba sai after 1 sannan tabi lafiyar gado mami kuwa ta mata sai da safe phn nata ta d'auka ta ga mssd calls 6 na Shuraim sai kuma text kamar haka
*my baby ba kira baki d'aga ba kodai bacci ne...just to hear ur marvelous voice n to tell u how much I missed u, gobe war haka muna tare I love u takkia n gudnyt* murmushi ne ya subuce mata wai wane irin so ne Shuraim ke mata?
hmmmm sunhera tace kad'an kika gani
Comments
Post a Comment