Skip to main content

Hajja hadiza

💦💦 HAJJA HADIZA💦💦

🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥

💦Talented Writers Forum💦
        TWF

Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻

kugiya daya tamkar dubu👌🏼

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

Written & story by Qz

My greetings to Yar Aljanna(namesyy) on the death of her grandpa,may Allah grant you & ur family the hrt to bear d lost & may jannatul firdaus be his final abode😪

💦21-25

Washe gari da safe takira wayarsa taji akashe,haka tayita kira har yamma amma baya zuwa duk dai zance dayace wai swtchoff,karshe dai bayan sallar magrib ta kira Hajja Ghaji akan tazo ta rakata gurin saurayin yayanta ko zata samu information akan inda zata sameshi.

6angaren Saleh kuwa hankali kwance har yama manta dacewa wata ta kirashi jiya harta 6ata mishi rai don kuwa tunda yatashi ya cire sim din data kira dashi yasa wani a cikin wayar yaji damuwarsa ta tafi.

              Ranar ma a unguwar su Hafsa budurwarsa ya yini daganan yadan zaga gun majalisa aka ta6a hira kafin ya dawo gida.

Meanwhile a 6angaren su Hajja Hadiza har sun tari dan adaidaita don shigowa anguwarsu Sule,sunkoyi dace domin suna sauka suka hango shi a bakin masallaci, batare da tunanin komi ba suka karasa inda yake cike da jindadin ganinsa, shi kuwa mamakine ya kamashi akan meya kawosu a wannan lokaci kusan ishai, ganin cewa gunsa suka nufo yasa ya tashi yaje yasamesu.

"Hadiza lafiya na ganki a wannan lokacin kusan goshin ishai?"ya tambaya yana nazarinta

"Lafiya ba lafiyaba yaya, dama munzo ne akan kozaka nuna mana gidansu abokinka!" ta fada kai tsaye

"Abokina kuma, wanne toh a ciki, ince dai bawani abun ne yafaruba?" yana magana yana tunani kala kala

Hajja Ghaji tayi saurin cewa"eh toh abokinka wanda kabamu lambarsa jiya dakazo dama munkira shi yau ne wayar akashe tun safe kuma munada wani muhinmin business dashi shiyasa muke nemansa".

"Au okay wai Saleh kuke nufi,inaga kila yacire layin awayarsa amma barin baku sauran layikansa guda biyu,amma samun shi a gida yanzu zaiyi wuya kila ma yana majalisa ta chan gangaren babban masallaci". yafada yana lalibo numbern

yana gama fada musu sukayi mishi godiya suka kama hanyar majalisan da ya kwatanta musu,shikuma ya fadane batare da tunanin ko zasu iya zuwa ba.

bayan sunwuce ya tsaya tunanin hali irin na yaran zamani toh koma wani irin abunw ai sai subari zuwa gobe tunda bagun mace yar uwarsu bane, gashi sai wani rawar kafa Hadiza keyi "Allah dai yasa bawata akasa". yafada tare da komawa bakin masallacin

Su kuma anasu 6angaren har wajen majalisan sukaje, ai kuwa sunyi saa yana gurin,dialing dayan layin da akabasu sukayi ai kuwa bajimawa yashiga amma dai baa dauka ba saida sukayi kira sau kusan uku ana hudun ya dauka.

"Hello waye ne naga anata kirana lafiya koh?" ya tambaya cikin jin haushinsu domin ya hango su kuma yagane Hadizan saboda kasancewa inda suka tsaya akwai haske sau dai basosai ake ganin fuskarta su ba.

"Lafiya kalau, dan Allah ko zamu iya ganinka minti biyu,muna daga gefen inda kuke zaune". tafada cikin lumana

Sai da yadan jinkirta kadan kafin yace "okay gani nan zuwa".

Kashe wayar tayi murna fal ranta "kawata kinga wai yana zuwa fa".

"Amma dai wallahi yacika dan rainin wayo sai da ma tayu tubani kafin ya amsa da zaizo din mtsss". ta fada cikin jin haushinsa

Hadiza ce tayi charaf tace "A'a kar ma kifara ai banta min shi ehe ni duk abunda zaiyu bazai dameni ba indai zai na kulani".

Tana gama rufe bakinta sai gashi ya iso yana wani yamutsa fuska kamar yaga kashi itadai Hajja Hadiza bata ji haushi ba amma Hajja Ghaji kam kamar ta rufeshi da duka aranta tace "dan rainin wayo wato ma irin ga matsiyata nan sunzo  nemansa mtss".

Sannu Sale yanzu muka hadu da Sule abokinka ya bamu numbrnka,nayita kiran dayan layin naka baya shiga dama shine mukazi muji ko lafiya dai koh". tafada ba ko kunya

Shikam abun ma mamaki ya koma bashi lailai kuwa wannan yarinyar da alama dai bahuwace babba ma kuwz ya fada a ransa kafin yace "eh lafiya kawzi banason yawan yin wayar ne shiyasa
na kashe don kar adameni dayawa kinsan wasu matar ba hankaline dasu ba sai surin ga kai kansu inda baasan suna yiba ma". yafada cikin gatse yana murmushin mugunta


Batare da takawo komai aranta ba tace "eh wallahi a wasu matan basuda kunya gaskiya,toh tunda kana lafiya mu zamu koma gida amma zankiraka anjima, wannan kawatace Hajja Ghaji". tafada tana nuna masa Ghaji wacce mamakin maganar da ya ya6a musu kadai ya cika zuciyarta ga karin abun haushin ma wato ita hadizan bata fahimci hausar ba harda tayashi zagin..

😍DEDICATED TO S.U❤

✨QUEEN ZAHRA✨✍

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...