Skip to main content

HAJJA HADIZA

💦💦 HAJJA HADIZA💦💦

🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥

💦Talented Writers Forum💦
        TWF

Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻

kugiya daya tamkar dubu👌🏼

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

Written & story by Qz

💦1-5

Sanye yake cikin Wando da Riga yar kanti,ga wani bakin Glass ya kafa kamar wani Boss,dube-dube yafara yi ajikinsa don ko za'a iya samun mishkila,ganin cewa babu komi yasa ya fito waje yana kiran Sale akan yayi sauri,shi kuwa Sale ganin Sule shuru yasa yayi tafiyarsa bakin kwalta wajen majalisar su.
            Ganin shuru bai ganshi ba shiyasa ya dau hanyar kofar sarki don yasan ba zai wuce yana gun majalisa ba, yana shan k'wana kuwa yaganshi sai zuba yake ana hira,"Sale,nagama kazo mutafi" ya fada kai tsaye yana faman goge takalmi. sale na dago kai yafashe da dariya ba sanya sai da yayi me isarsa alokacin har sule ya gama kuluwa yayi tafiyarsa sannan yatashi ya nufa inda sulen yabi yana kiran sunansa "Sule!Sule!! dan Allah ka tsaya yi hakuri dan Allah ni bada gayya nayi ba".
hararansa Sule yayi sannan yace "in banda rainin hankali shine zaka tsaya kanamin dariya fisabilillahi meye ne bai yiba a wanka na eh?" ya tambaya yana duba jikinsa ta ko ina,shi kuma Sale gimtse dariyarsa yayi yanacewa "yi hakuri nidai kawai ganin yanda kasha Bak'ak'en kaya da Jan takalmi da hankie kamar wani danmafiya shi ya sanya ni dariya, amma dai yi hakuri dole ma maryama taso wankan nan dan gaye dan kwalisa in kafaso dole ne abada hanya haba abokina dan murmusa mana eeh eeh" haka yayita mai kirari yana hura masa kai har sai da suka isa kofar gidansu maryama.
           dai-dai isarsu dai-dai fitowar Hajja Hadiza wacce kanwace ga maryama budurwar Sule,sake baki tayi tana kallon Sule kafin ta bushe da dariya sai da tayi dariyarta mai isarta sannan ta lura ashefa su biyu ne ai kuwa tana kai dubanta kan Sale taji yagama tafiya da ita kallonsa take ba ko kiftawa,fitowar maryama ne yasa ta dakata da maryama ta ambaci sunanta,sai da ta dan razana kafin ta juya tana guna guni ta dau hanyar gidansu Kubra kawarta inda aka aiketa sayan manja..
"kai masoyi wannan wankan duk nawa, gaskiya naji dadi kayi kyau sosai,kuma naji kishi akan duk wacce takalleka don kuwa tabbas sai ta sake kallonka" maryama  tafada tana mishi fari da ido,shi kuwa gogan kamar ya zuba ruwa akasa yasha don dadi har ya manta da rashin mutuncin da Hajja Hadiza tayi masa. Sale ne yayi gyaran murya sannan yace "masoya ni zan wuce dama rokosa nayi,yanzu wajen kallon kwallo na nufa daga nan indare bai yi ba kila inbiyo mutafi tare in kuma 10 yayi sai dai mu hadu a gida".   
          "Haba guy ya zakamin haka ai nazata tare zamu tafi ai,banma zaci zakaje wajen kallo ba" Sule yafada kamar gaske yana 6ata rai amma a zuciyarsa yaji dadin hakan "nidai kayi hakuri kawai muhadu a gida banson takura muku ne if not dana zauna har kugama, amma kaga inna zauna kaima zakayi saurin gamawa saboda you dont want to keep me waiting,so kar kaji komai sai mun hadu kawai". yafada yana bashi hannu,shima Sule ya mika masa suka tafa "shikenan tunda haka kace sai mun hadun nagode da rakiya". murmushi yayi sannan yace "haba dai abokina anything for you,toh gimbiyar Sulaiman sai kinsake ganina".
"nagode Sale agaida gida".tafada tare da yiwa Sule signal akan su shiga cikin gida.. shi kuma Sale yadau hanyar tafiya anguwar rasha don kallon kwallo.
        6angaren Hajja hadiza kuwa Allah-Allah takeyi tayi tagama kar6an sakon takoma gida don ganin wannan kyakyawan saurayin itakam dai gaskiya tafad'a tarkon sonsa domin ya kasance irin namijin da take matukar so woow gashida saje me kyau ga shi dark handsome ga ga ga kash "nikam Kubsi uma bata gama bane sauri fa nakeyi gaskiya". nazarinta kubsi tafara yi kafin tace "nikam Hajja Hadiza anya ba abunda kike 6oyemin kuwa, naga tunda kika zo ba'a nitse kike ba kuma da alama kina cikin farin ciki sai dai na fahimci ba'aso musan komi,amma intai tsami zamuji". tafada tana hararta da wasa,tsaki taja ta tashi tana cewa "kinga nikam barni tukun inji da abunda ke damuna kin tsaya kina dagulamin lissafi idan uma tagama dan Allah kibawa Laurat ta kawo min gida" batajira amsar Kubra ba tayi tafiyarta abunta,ita kuwa Kubra ta saki baki tana kallonta "kwajimin karfin hali toh in Laurat din bata gida ba,kaii Hajja halinki sai keh".

✨QUEEN ZAHRA✨✍

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...