*6:00pm*
*ZAFIN KISHI*
*WRITED BY*
*husnah mb*
*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*
*58*
_Wannan shafin na sadaukar dashi gareki ke kadai na gode da kulawarki a gareni Allah ya kara zumunci_ *Ameen*.
Maijidda.
*After 1week*
Yau aka kawo lefan fatee kaya yayi kaya kowa maganan yawan kayan yakeyi, yadda kasan ba kudi aka zuba aka saya ba danko kayan hadda na hauka, Akwati dozin 2 ne ko wani set din akwati daya ansa Atamfa kaloli 40 kayan shafe shafe kan ba,a magana dogayan riguna mah ko wani set din akwati guda 20* yasa mata kayafah yakai kaya ko yar shugaban kasa iyaka kenam.
*2days later*
Manal ne ta fito cikin shirinta parlon downstairs ta nufa faty ta samu zaune tana jiranta.
'Faty ne tace sai yanxu kika gama shirin nakin tun dazu na fito fa ina jiranki kinsan ni yau lectures din 9 nake dashi gara ke kuma yanxu inaga har 8:40 plz kiyi sauri mu tafi manal ne tace nikam karki cinyeni nama gama komai mu tafi dariya faty tayi sannan tace to ai kedin ne wlh sai a hankali kina abu wani lokaci kaman bakida jini manal ne tace eh din bandashi ai da naki nake aiki harsun nufi bakin kofa manal ta tuno ta manta key din mota cewa faty tayi bari ta dauko key din motan ta mantashi akan Tv stand mita faty tayi tayi dama kekam ai wlh saikace wata mai aiki da batry nikam inkin dauko key din ki sameni a parking space ta wuce abunta
[9/29, 9:15 PM] Ma Asaa4😘: *12/9/2017*
*6:00pm*
*ZAFIN KISHI*
*WRITED BY*
*husnah mb*
*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*
*59*
Shi inzai tuna ma rabon khadija taje ta gaisar da mamie harya manta dai inzai tuna zai iya cewa tun kafun ya auri manal last zuwanta gidansu nan ma saida ya takura mata kuma yasa ta shirya ya kaita..
waje yayi ya barta a wajen bayan yayi sallan magrip ne yazo ya samu su manal har sun shirya shi kawai suke jira fitowa sukayi basu tsaya ko ina ba sai gidan mamie, aiko da mamie taga manal ina kansa ina kan ajiye sai tattalinta takeyi ita dai manal abun har kunya ya soma bata dan tunda taga yadda mamie take tarairayarta tasan tabbas Aliyu ya fada mata tanada ciki, hira Aliyu yasha shida mamien sah ita ko faty gunsu hanan ta tafi dan su bata labarin kayan aurenta dan bata gani ba lokacin da aka kawo bata gida tana gidan Yaya Aliyu, hanan sarkin surutu haka tata zubawa faty labarin kayan auren fillah filla babu abunda bata fada mata ba danko ta karewa
kayan kallo faty har kwadiyin kallon kayan natan taji but hakan bazai samu ba saboda kayan a dakin abbansu yake kuma yana gida so babu yadda za,ayi ta kallah,
Ita kuma Khadija tunda su Aliyu sukabar mata gida ita kadai murna take kaman an mata kyautan Aljannah direct dakin Aliyu ta nufa a bude ta samu danko inzai fita bai damu da rufewa ba tunda a tunaninsa akwai mutum acikin gidan duk da kuwa yasan halin matan tasa sarai kawai aniyarta ya tura mata a ganinsa yafi karfin kudin da take dauka masa,
Har zata shiga dakin Aliyu sai kuma ta dawo handle din kofan dakin manal ta murda sai taji a kulle dakin Aliyu ta shiga har uwar daka direct bakin wadrop dinshi ta nufa wajen da yake ajiye keys din safe dinsa kash saidai bata ganshi a wajen ba nema tayi sosai bata samu ba maida kayan tayi ta rufe wadrop din dakinta ta nufa dan in bata manta ba tanada sapiya din key din safe din daukowa tayi da mamaki kuma sai taga ya canza keys din danko tasa yaki bude mata tsayawa tayi tana tunani tafi minti10
''Murmushi tayi alama ta samo solution dakinta ta nufa saita dauko abun bude key din da getman ya sayo mata lokacin d
lokacin da key din dakinta ya bata,
Aiko zuwa abun tayi daidai bakin wajen key din baiyi wata wata ba ya bude murmushi tayi tare da ajiyar zuciya dan abunda idanunta suka gano mata kudi ne sosai acikin safe din dan tunda take bata taba ganin Aliyu yayi ajiye kudi mai yawa irin wannan bah dan har tsoro kudin suka bata rafa rafa kawai take dauka ita kanta batasan iya kudin data dauka ba san yawansu...
_Nidai a yanda naga kudin cewa nayi zasu kai miliyan1_
A hijab din dake jikinta ta kulle kudin rufe safe din tayi tasa abunda ta bude ta kulle shi saidai garin saurin da takeyu karsu dawo su sameta danta bata lokaci ta manta key din cikin dakinta data taho dashi acikin safe din,
''dakin ta jawo ta kulle kaman ba,a shiga ba dakinta ta nufa akwatin da Aliyu ya mata na fadan kishiya ta dauko ta zuba kudin aciki kwado ta saka ta rufe ajiye key din akwatin tayi karkashin katifanta...
Muje zuwa..........☺
*WhatsApp no*
08109990994.
[9/29, 9:16 PM] Ma Asaa4😘: *19/9/2017*
*3:00pm*
*ZAFIN KISHI*
*WRITED BY*
*husnah mb*
*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*
*60*
_sorry fans kunjini shiru kwana 2 wani dan uzuri ne ya hanani yin typing, bear with me luv u all_.
daukan key din yaya yanata jujjuyashi a hannunshi shiru yayi kaman yana tunani murmushi takaici yayi tare da ajiye key din ya maida kudin cikin safe
Key din ya dauka a fusace ya nufi dakin khadija...
''Kofan dakin da yagani a rufe ne yasa ya banko kofan da karfi shiga yayi ko sallama babu kwance ya sameta saman kujera tayi crosing leg daka mata tsawa yayi yana tambayanta uban waye yace ki daukamin kudi shiru tayi batace masa komai bah ina tambayanki kin ko baki jini bane ni ban dauka maka kudi ba ta fada tana yamutsa fuska
Kinma rainawa kanki hankali aliyu ya fada yana galla mata harara
Ko an gaya miki bansan duk abunda kikeyi bane kallonki kawai nakeyi barin fada miki shiru shiru ba tsoro bane amma tunda abun nakin rainin hankali ne mu zuba nida ke kukan munafurci khadiha ta fara tana ce masa ni ban dauka maka kudi bah key din hannunshi ya daga sama inbake kika dauki kudina ba meye yakai key din dakinki cikin safe dina kuma kinsan duk gidan nan babu wanda yake da irin wannan key din saike kadai ya jefa mata key din tare da cewa na baki nan da naje office na dawo wlh tallahi in baki fito min da kudina ba na lahira saiyafiki jin dadi ya fada tare da hankada kofan dakin ya fita
dakin manal ya nufa direct daka ganshi kasan ranshi ba karamin baci yayi ba faty ya samu xaune a falo tana waya aiko ko kulata baiyi ba daki ya nufa manal ya hango kan gado tana kwance amma da dukkan alamu dai kaman ba bacci take ba ganinshi da tayini yasa tayi saurin mikewa dan ba karamin tsorita tayi ba ganin yanayin da yake ciki dan tunda take da bata taba ganin bacin ranshi irin na yauba tambayanshi ta hauyi
_"Habibi_ lafiya kuwa meye ya sameka ba yanxu muka rabu kana cikin fara,a bah ta jero masa tambayoyin shiru yayi baicr mata komai ba kara tambayanshi tayi habibi _what's wrong with u_ murmushin takaici yayi sannan yace nothing Queen meye kika gani naga ranka a bace ne shys nake tambayanka
Babu komai yace mata shiru tayi a ranta tana cewa tunda yace mata babu komai baxata takura masa bah wata kila tsakaninshi da matarsa ne bataso ya sani shiyasa kwantar masa da hankali ta hauyi da kalamai masu dadi da sanyaya zuciya sanda ta tabbatar ya fara dariya sannan tace mai ya tashi ya tafi office karya makara dan taga rana ya fara yi jakan hannunshi ta karba har parking space ta rakashi...
Ta bangaren khadija kuwa Aliyu na fita ta kwashe da dariya tace kadanma ka gani akwatin datasa kudin ta dauko kayanta ta jera a akwatin. ta rufe dakin ta nufi gidansu
A falo ta tadda hajiya tana xaune tana kallo kuka ta farayi da sauri hajiya ta tashi ta nufo inda take lafiya ta fara tambayanta itadai kuka kawai takeyi batace komai bah jakan hannunta ta karba tare da rikota suka nufi daki ajiye jakan tayi ta xauna kusa da khadija tambayanta ta hauyi ko lafiya kusan 5mints sannan ta tsagaita kukan da takeyi nunfashi taja sannan tace
Aliyu ne yace na tattara kayana na dawo gida gwalo ido hajiya tayi tace ki dawo gida kuma meye kika masa kuka ta fashe dashi sannan tace babu abunda na masa yadai shigo ya samen ina kwance shine yacemin na dawo gida shiru hajiya tayi sannan tace bari abbanki ya dawo sai musan abunyi.
"maza tashi ki shiga kiyi wanka gacan abinci na gama saikici to khadija tace tare da mikewa ta nufi toilet.
Ta bangaren Aliyu kuma yau yadai fita office ne kawai saboda Queen dinshi gabaki daya baijin dadi don ba karamin batamai rai abunda khadija ta mai ba 5 o'clock Aliyu ya dawo gida a downstairs ya tarar dasu manal suna kallo itada faty manal ne ta tashi ta karbi bag din hannunsa tare da sakar masa murmushi wanda yake kara fiddo da kyawunsa...
*Muje zuwa.*
*WhatsApp no*
08109990994
Comments
Post a Comment