💦💦 HAJJA HADIZA💦💦
🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥
💦Talented Writers Forum💦
TWF
Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻
kugiya daya tamkar dubu👌🏼
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
Written & story by Qz
Am using this opportunity to wish u a Happy anniversary my dear Islahatee🎊🛍🎁💝Allah ya karo sosayya I wish you peace and blessings of Allah to your union ALLAH ya kara dankon kauna da zuri'a dayyibah 💃🏻💃🏻Allah yasamuku albarka zaman lafiya farinciki da fahimtar juna me daurewa Allah ya kareku daga sharrin masharranta wish u all the success in ur life ,joy and more love with Abban abla 💝💝
💦26-30
Batare daya kalle taba yace "toh nagode da kulawa kawarmu". sannan yayi musu ban kwana ya kama hanyar gida domin sun 6ata mishi show yau dinnan.
Anasu 6angaren kuwa Hajja Ghaji ta kulu iya kuluwa don kuwsa ya balain ci musu mutunci sosai da sosai,bata ma jira Hadiza ba ta tari mai adaidaita tayi tafiyarta zuwa gida,ita kuwa Hadiza juyawar da zatayi taga har me adaidaitan yayi wucewarsa,bata kawo komai aranta ba ta tari nata tawuce gida itama zuciyarta fari kal.
Yana isa ya taras da Sule har ya kwanta, ai kuwa ya dundesa da karfi har sai da shima yaji zafi a hannun nasa.
"Kai bakada hankali ne meye haka dan Allah fisa bilillahi,ai zakasamin ciwon kirji". Sule yafada yana hararansa
"Nikuma da kake neman samin ciwon zuciya fa sai ince me, yanzu saboda Allah karasa wadanda zaka bawa numberta sai wadannan kida human yaran?"
"Banganeba nifa cemin sukayi kuna da muhinmin abu dasu shiyasa ma nabasu". nan ya kwashe komai daga basu number zuwa yau da sukazo gurin sa suka kara karban numbern wai akan wanchan baya shiga.
"Tabdijam nima kuma munyi drama daga daren jiya zuwa yanzu daka ganni a gida bashiri" nan shima ya zayyana masa abunda yafaru daga jiya data kirasa zuwa yanzu da suka rabu,
Zaro ido Sule yayi yana mamaki "ashe se da suka je gurinka, lailai yarannan basuda hankali, kaima fa dan rainin wayo ne haka ka zagesu hankali kwance sukuma dake garori ne basu gane ba kai Saleh". yafada yana ta kyelkyale dariya
"A'a toh mai zance musu wai harda fa anzo duba lafiyata ne sai kace wani kaninsu kokuma yaronsu". yafada yana tuna yanda wawiyar taketa zaro zance.
"A'a dai Sale kaga fa yarinyar tanasonka ka dai daure ka bata lokaci koda kadanne kaga irin nata jarumtar". yafada da iya gaskiyarsa,sannan ya gyara filonsa ya kwanta
"Haba abokina wannan gaular me zanyi da ita, amma dai shikenan zan jaraba tunda kasa baki". yafada cikin zolaya.. kafin shima ya kwanta
6angaren Hajja Hadiza kam tana isa gida tayi wanka ta yi sallah sannan tayi shirin barci ta dauko wayarta ta fara neman layinsa, saida yayi ringing sau biyar kafin akadauka cikin muryar barci yace "Hello dan Allah nafara barci kibari gobe mayi magana nagode". be jira cewarta ba ya katse wayar. itama kuma taji dadi dahar ya dauka yamata magana kuma ai yanada uzuri bakomai goben zatakirasa
Washe gari dasafe
Tunda safe ta shirya taje gidansu Ghaji tabata hakuri don kuwa taga alama fushi tayi sosai,ai kuwa ba jimawa ta saukko suka fara hiransu dama basu iya fada da juna ko sunji haushin juna ma na dan lokaci ne,sai kusan azahar ta koma gida..
Tana isa ta lalibo wayarta ta kira numbernsa ringing biyu ya dauka ba laifi sun danyi hira har ma da cewa zai kirata anjima,hakan kuwa bakaramin dadi yayi mataba don kuwa batayi tsanmani ba sai kuma gashi yamata bazata...
Suna gama wayar sai ga kira yashigo,kallon sunan jikin numbrn yayi yagadai itance wanda beyi expecting ba yama cire rai akan zata sake kiransa don kullun yakirata baya samunta,sai da ya tsinke aka sake kira kafin ya dauka cikin jin dadi domin yasan walwalarsa da kwanciyar hankalinsa zai dawo sosai a wannan lokacin.
"Hello manyan gari ganinku sai ancika form". yafada yana dariya
"Ahaba sai kace villa zaka shiga garda su cika form?" ta tambaya itama tana dariya
"ai ku dinne sai da register,layinka baya shiga kusan kullun sai na kira,ko yanzu ma na dauka gizo numbern naki kemin ai". yafada cikin zolaya
😍DEDICATED TO S.U❤
✨QUEEN ZAHRA✨✍
Comments
Post a Comment