Skip to main content

ZAFIN KISHI BY HUSNA_MB

[9/29, 9:11 PM] Ma Asaa4😘: *7/9/2017*

    *6:00pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*50*.

_my kawa my abokiyar gulma my kishiya my abokiyar shawara wannan page din nakine shona nah kina raina_
   I _love u so much nd i_ _will forever lurv nd_ _cherish u_. _muah of love_ _beb_

Harzata shiga sai kuma ta tsaya kaman tana tunanin wani abu downstairs ta sauko tana duba ina Aliyu yayi ganin motarsa tayi waje ne yasa ta haura kofan dakinshi ta murda sai taji a bude shiga tayi taga babu kowa sai tv ne kawai yake aiki shi kadai kofan ta maiyar ta rufe tare da murda makullin kofan ta rufe
Karewa falon kallo tashiga yi yau kusan kwananta 5 kenam bata shigo dakin ba cikin daki ta nufa kan gadon take kallo yasha shimfidi yayi kyau babu karya shimfidin dake saman gadon ta yaye ta ajiyeshi a kasa katifan ta daga ta jingineta gefe kullin maganin dake hannunta ta kunce barbada maganin tahauyi kan flow bed din gadon saida ta tabbata ko ina ya samu sannan ta maida katimfan ta shimfida zanin gadon ta dauko ta shimfidashi yadda yake da yadda kikasan ba,a daga gadon ba sauran maganin ta kunshe shi a skirt dinta falo ta fito fuskanta dauke da murmushi kofan ta bude a hankali ta fito abunta
dakinta ta nufa.
Misalin karfe 8 o'clock Aliyu ya dawo daga gidan mamie dakin manal ya nufa kwance ya sameta falo kan kujera tana charting,
   "Kusa da ita yazo ya zauna yana tambayanta yaya jikin dai yayi sauki tace tana murmushi dariya yayi sannan yace eh dama xakice yayi sauki manah tunda bakyason Allura
  Wayace maka allura ne banaso habibi yayi sauki ne fah da gaske shys ka taba jikina kaji babu xafi yanzu hannunsa ya daura kanta yana shafawa jin da yayi kan babu zafi ne yasa yaji wani sanyi a ransa ledan da yake hannunsa ya mika mata gashi bari zo koh Wify karba tayi
tashi yayi ya nufi dakin khadija dayan ledan ya mika mata sannan ya fito dakinshi ya nufah tv ya samu kunne kashewa yayi ya nufi uwar dakin yana sa kafansa sai yaji gabansa ya fadi innalillahi wa'inna ilahin raju'un yaketa fada a ransa wani hajijiya yaji yana shirin dibarsa gini ya dafa a hankali ya samu waje ya zauna yana rike da kansa ji yake kaman kayinsa xai fita dan wani irin sarawa kan nashin yakeyi saida yayi kusan 10minuts yana xaune addu'a yake tayi a zuciyarsa har yaji ya dainajin abunda yakeji sai kasala kawai toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower bayan ya gama wanka alwala yayi jallabiya ya dauko sabuwa a cikin wadrop dinsa ya saka yayi sallah isha'i addu,a yayi sosai yayi
yayi addu'a Allah ya hada mata kan matansa.

Wayansa ya dauko ya nufi dakin manal inda ya barta yazo ya tarar da ita tana xaune kusa da ita ya xauna yana tambayanta meyasa bataci naman daya bata ba yasan kuma bataci komai ba kai nake jira tacemai to ai gani nan nikam ya fada yana kwaikwayon irin magananta dariya ta kelkele dashi tare da tashi ta shiga kitchen plate ta dauko ta baza musu naman a ciki sunaci suna tadi cikin so da kaunan junansu
bayan sun gama manal ne ta tattare wajen toilet ta shiga wanka tayi ta fito wata doguwar riga ta dauko me colour pink wanda bata wuce zuwa gwiwanta ba bakin mirriow ta nufa body spray ta feshe a jikinta humra ta dauko ta shafah harzata kwanta saita tuna bata kashe tv falo ba akunne ta barshi fitowa tayi zaune ta samu Aliyu yana danna laptop mamaki tayi sosai dan ita tayi zaton ma ya kyaunta yanxu tambayanshi tahau yi yaushe yashigo ce mata yayi ai tunda ta tashi shi dama babu inda yaje ina khadija tahau tambayanshi tana dakinta manah shiru tayi tana mamaki yadda duk kishin khadija ta yaye mijinta Allah ya kyauta tace a ranta zama tayi a gefenshi tana tayashi hira
Muje zuwa.......☺

*WhatsApp no*
08109990994
[9/29, 9:12 PM] Ma Asaa4😘: *7/9/2017*

  *12:30am*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*
*51.*

Hira sukeyi harta farajin bacci alaman data ga kaman Aliyu baida niyyan tafiya yanzu shys tace itakam bataje ta kwanta inya gama ya rufeta ta baya to kawai yace mata dan bayason jan maganan daki ta nufa kwanciya tayi tare da kashe wutan

1hour later
Aliyu ne ya gama aikin da yakeyi rufe laptop din yayi tv ya kashe tare da rufe musu kofan dakin manal ya nufa wutan dakin ya kunna hangota yayi saman gado tana bacci hankalinta kwance dan daga ganin yadda take baccin yayi nisa wayansa yayi plugging jikin charger bayanta yaje ya kwanta tare da rungumota cikin bacci takejin kaman motsi amma dayake baccin natan yayi nisa sai bata kula ba kamshin turaren daya doki hancinta ne yasa tadan bude ido a hankali da yake wutan dakin a kashe yake yasa bata gane waye bane dan harta tsorita ganin mutum
rungume da daga kanta tayi sama kunna wutan dakin tayi ganin Aliyu ne yasa ta sauke nunfashi a hankali bude ido tayi sosai tana mamakin meya kawoshi dakinta yauma kodai khadija ne yauma taki binsa dakinta ganin batada amsan tambayan da takeyiwa kanta yasa ta kashe wutan ta kare rungume habibin natan taci gaba da baccinta

Washe gari!
Misalin karfe 10 Aliyu ya gama shiryawa tsaf bayan yayi breakfast ya fita office jin dadin da manal taji bataji ne yasa yau batama sauka downstairs ba tunda ya fita baccinta tasha bayan ta tashi kuma tadau waya ta kira momyn ta dan jiya tata kiran wayanta a kashe hira sukayi sosai bayan sunyi sallama da momy ta hau dialing din number zahra
Aiko ringing daya ta dauka

"Hello_
Kawata ykk
Zahra ce ta amsa da lafiya qlau wlh kwana 2
Ya mama?
   "Mama! Lfynta qlau
Manal ne tace ya ankawo kayan ne dariya zahara ta kelkyale dashi sannan tace an kawo manah yaushe xakixo ki gani jiya da yamma aka kawo

_manal ne tace haba To insha Allahu soon ina hanya xan tambayi habibi xaki ganni
    Allah yasa
Ameen manal tace nan ta katse wayanta.

Misalin karfe 8:00pm Aliyu ya dawo gida da yake yau yaje gun Auwal shys bai dawo da wuri ba dan sun kwana 2 basu hadu ba
   'Alwala yayi yaje yayu sallah isha'i b
bayan ya dawo ne ya shiga dakin manal bai sameta ba a toilet yaji karan ruwa da dukkan Alamu wanka yayi dakinshi ya koma kan gado ya kwanta domin ya huta dan yau yayi matukar gajiya da yake yadanyi biye biye
Kwanciya yayi amma gabaki daya gabansa faduwa yakeyi ga wata kasala da yakeji a jikinsa gabaki daya bayajin wani karfi a jikinsa kusan 10mints yayi a haka maimakon yaji abun ya ragu sai karuwa ma yakeyi nan da nan zazzabi me zafi ya rufeshi sai rawan sanyi yakeyi yana dunkule jikinsa acikin bargo

Ta bangaren manal kuma data fito daga wanka kaya tasaka ta feshe jikinta da turare shiru da taji Aliyu har yanxu bai shigo bane yasa ta dauki hijab ta nufi dakinsa cikin yanayin data iskeshi ne hankalinta yayi matukar tashi ta tsorita sosai ba kadan bah dan gabaki daya rawar sanyi yakeyi gadon da yake kwance a kansa ma kanshi rawa yakeyi da sauri ta karisa inda yake tana tambayanshi ko lafiya kasa bata amsa yayi dan bakinshi ma kanshi rawa yakeyi innalillahi wa'inna ilaihin raju'un ta fara furtawa gabaki daya ta gigice tama rasa meye xata farayi yanxu daya hannunshi ta rike tana ta yimasa sannu hannunta tasa ta janyo blanket din ta rufeshi sosai

A haka ya kwana cikin zazzabi da kasala duk a cikinsu babu wanda ya iya yin bacci manal kam ma kusa a zaune ta kwana
  sai kiran sallan farko na asuba ta samu bacci ya fara dibanta shiko Aliyu har yanxu dai yana kwance ne amma gabaki daya kasala ta hanashi ko iya mikewa haka yanaji har aka idar da sallah asuba bai iya tashi yayi ba
    "A hankali ya fara tashin manal sallah ta tashi tayi sannan ta taimaka mishi ya samu yayi sallah a zaune.....

Muje zuwa.......☺

*Whatsapp no*
08109990994
[9/29, 9:12 PM] Ma Asaa4😘: *8/9/2017*
 
    *12:00am*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*52*

Haka yau ya yini kas a gida ko office bai iya fita ba sai around 3 na yamma yacewa manal ta taimaka mishi ya sauka downstairs ko zaiji karfi a jikinsa dan ya gaji da zaman daki.

Ta bangaren khadija kuwa yau itama a daki ta yini tunda ta fito da safe duba ko Aliyu ya fita office da bataga fitansa bane hakan ya tabbatar mata hakanta na kan cimma ruwa!

A garden ya karisa yininsa shida manal aiko tunda ya sauko yaji yama dainajin duk wani abun da yakeji yafarajin karfin jikinsa kaman bashi bane daxu inya tashi yake kokarin faduwa
Sai 6 o'clock sukabar garden falon downstairs suka zauna Aliyu ne ya tafi sallan magrip don yanxu kam yamaji sauki ita kuma manal ta hausa upstairs domin itama tayi sallah
Bayan ya dawo daga sallah da bai ganta a falon ba haura wa yayi dakinta yayi direct zaune ya sameta a falo tana kallo kusa da ita yazo ya zauna suna kallon tare bayan sunfi sallah isha'i ne suka tafi dakin Aliyu domin yin bacci dan kwana2 Aliyu ya daina hira mai tsayi yanayin bacci da wuri saboda fita office da wuri aiko baifi 10mints da kwanciya ba yauma zazzafi ta
rufeshi abu ya dawo sabo haka suka kwana a zaune yauma manal kuwa har cikin ranta take tausayawa habibin natan ganin halin da yake shiga.

   ********

After 2 mouth
Ta wajen Aliyu kuma jiki Alhamdullh yayi sauki sosai don manal tana ganin alamun yanaso ya tashi zata dauki kofi tamai addu'a yasha ya wanke fuskanshi ta shafe masa sauran a jikinsa ba karamin jin dadin yadda manal Take kula dashi ba Aliyu yakeyi shidai kullum addu'a yake
mata tabbas yayi sa,ar mata ba kowacce mace bace zata iya jurar irin wannan wahalhalun kusan ace wata 3 mutum na fama da irin wannan rashin lafiya kuma kullum babu bacci a da wasu matan ne da gudu xasuyi su barka cikin rashin lafiya.

A haka rayuwa ta canzawa Aliyu da manal kullum dare indai kwanan manal ne to cikin zazzabi da kasala yake kwana shi kanshi abun yana damunshi kuma yana matukar mamakin abunda yake faruwa dashi saboda duk randa

akace kwanan khadija ne bayajin irin wannan abun da yakeji ran kwanan manal.
  daga baya daya fahimci kaman abunda yake faruwa dashi a dakin nashin yake sai yazamana cewa kullum in kwanan manal ne saiya daina kwana a dakinsa dakinta yake binta su kwana ai kuwa tunda ya farayin haka saiya samu sauki.

Ta bangaren khadija kuwa gabaki daya batada sukuni ta rasa me yake mata dadi tana kwance akan gado tama rasa waye xata fadawa damuwarta waya ta dauko ta hau dialing number iklima don neman mafita aiko ringing daya sai tayi picking
  Hello_ kawata
Na'am khadija ta amsa cikin sanyin murya wadda da taji yadda take magana kasan tana cikin damuwa
Iklima ne tace yanaji muryanki wani iri kaman wanda tayi kuka
Khadija ne tace bari kawai kawata ai damuwar da nake cike ya wuce sanin dan adam shine na kiraki don neman mafita dan Allah inaso kizo dan mu tattauna wannan maganan to babu damuwa kawata anjima xaki ganni ai damuwarki damuwata ce khadija ne tace to saina ganki tare da katse wayan...

Aiko batafi 1hour ba saiga iklima a gidan khadija tana shigowa ne sukayi kicibis da manal a bakin stairs kare mata kallo tashigayi ita kanta manal sanda ta tsargu da irin kallon da iklima take mata duk da babu wanda ya kula kowa a cikinsu
   "dakin khadija tayi direct zaune ta sameta a

falo tayi uban tagumi ganin kawar tatan ne yasa ta tashi da sauri ta kamota daki suka shige
bakin gado suka xauna suna facing din juna iklima ne ta fara tambayan khadija kawata meyake damunki ne kam kiga yadda kikayi baki kika rame ita kuma yanxu muka hadu da ita bakiga yadda ta zama bane tayi kiba tayi wani fresh har wasu mazaune ta ajiye meyake damunki ne wai haka nunfashi khadija taja tare da cewa ba dole tayi kiba ta kwacemin miji kawat wlh yanxu haka maganan da nake miki rabona da Aliyu ya kusanceni tun ana aurensa saura sati1 ido iklima ta zaro tabbas maganan khadija ya ruda mata kwakwalwa kasa cewa komai tayi tana kallon kawartatan Shiru ne ya ratsa wajen na kusan minti2 iklima ne tace kinsan me kike fada kuwa khadija saikace ba mace ba ina makaman yakin kinaso kicemin duk basa aiki kenam koh meye Auren Aliyu da

wannan matsiyaciyar kishiyar takin fa kusan wata 6 fa kenam amma kicemin a duk wata bakwai din nan baku hada shimfida da Aliyu ba me kika tsaya yi baki dauki mataki ba har lokaci yana son kure miki ni wlh kalon dana mata ma kaman wata me cike ai mun hadu da ita yanxu ina kokarin shigowa..


Muje zuwa....☺


*WhatsApp no*
08109990994

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...