💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
*29&30*
*jinjina gareku masoyan kwarai Allah bar zumunci ya kara had'a kawunan mu talented writers musamman.....*
*Reefat yahya*
*Haliemerh Ameen*
*Islah tasi'u ya'u*
*Maryam Lawal*
*Rukayya dubbani*
*pherteenjay*
*Husna MB*
*Aysha Umar*
*Hajarat M Bash*
*Fayeez Usman*
*Sadee Smart*
*Roshni Anty*
*Suhailat Ishaq*
*Maman Khalid*
*Zahra MS*
*Ya'r aljannah*
*Ummin Innah*😘😘😘😘🤝❤❤❤❤ *_ana tare ai_*
Afreen ta sunkuyar da kai tana kallon kasa uncle Mohammed ne ya daka mata tsawa dama shi yana da zafi don family duka ana tsoronsa yace " ke kinga saan Ki a nan ne ana miki magana kika yi shiru" cikin rawar murya tace " bab..babu ko d'aya " uncle Mohammed yace " uban wa kike so? Toh karya kike auren zumunci ya zama dole matukar kina cikin wannan dangin" murmushi modibbo yayi tare da cewa " ka bita a hankali y'ar gata ce" tsaki uncle yayi yana danka mata uwar harara gaba daya haushinta yake ji yanda ta wargaza Zumunci ta tada hankulan jama'a cikin family. Modibbo yace " kin biyewa iyayen naki kema dan gwamna kike so koh? toh bari na baki sako ii Isar musu , gobe bayan sallan jumaa xaa daura aurenki idan uban naki yaga dama yazo idan yaga dama kar yazo ga Mohammed nan shine waliyin Ki tashi Ki tafi Allah muku albarka " gaba d'aya sun juya suna kallonsa mamaki ne bayyane a fuskokin su toh waye angon??🤔 modibbo yace su tashi su tafi da Shuraim , Saleem da Afreen wato ya rage sai iyayen nasu.
Dakyar Afreen ke tafiya wani jiri ne ya dibata saura kad'an ta fadi Shuraim yayi saurin tare ta ta fad'a jikinsa cike da kishi Saleem yace " Baka da hankali ne? Matar tawa zaka runguma" " matarka ko matata kaji wata maganar banza" ganin sun fara haukar tasu ne yasa Afreen fisge jikinta tana dafe bango har ta karasa cikin gida, d'akin Dada ta wuce babu kowa a falon nan ta xube bisa kafet ta fara rusa kuka tamkar ranta zai fita. Wannan wace irin rayuwa ce? Shekaran jiya ta gama exam gobe xaa daura mata aure , auren ma ba da Wanda take so bah Saleem ne ko Shuraim oho! Kuka ta cigaba da yi tare Dada ta shigo da Shuraim. A kidime ta karasa kusa da ita " yau me zan gani y'ar nan mutuwa akayi ko me?" Dada tayi magana cikin rudanin ganin kukan da Afreen take " wayyo Dada zasu kasheni gobe xaa daura min auren dole" gyara zama Dada tayi tare da washe baki " toh..toh da Shuraim d'in xaa daura kenan, Alhamdllh kai masha Allah abu yayi kyau" Shuraim yace " modibbo fa bai gaya mana da waye xaa daura bah kedai Ki tayani da adua Allah yasa dani zaayi" gaba d'aya haushinsu take ji tamkar ta rufesu da duka , cikin fushi ta tashi ta koma bedroom tabar su nan falo Shuraim ya kashewa dada ido nan ya tashi yabi bayanta .
Rub da ciki tayi ta cigaba da kuka a hankali ya xauna kusa da ita tare da jawota jikinsa nokewa tayi da karfin tsiya ya jawota ya rungumeta gam! Yana jin karar bugun zuciyarta nan ya fara mata magana cikin wani salo " kiyi hakuri my Queen Ki daina kuka pls kina d'aga min hankali cos bazan jure ganin hawayen Ki pls" banza tayi ta cigaba da kuka a yayinda ta lafe bisa kirjinsa .wani irin shaukin sonta ne ke fisgar Shuraim ina ma a ce sunyi aure murmushi yayi cikin xuciyarsa yana adua Allah yasa gobe ayi dashi, idan Saleem ne kuma fah? Nan ya kara kankameta gabansa na faduwa yana tsoron rasa ta baisan lokacin da hawaye suka xubo masa ba , Afreen tayi mamakin ganin hawaye a idanunsa nan ta sagaita kukan da take a hankali ta d'aga kanta tana kallon sa yace " Ki tayani da adua bana son na rasa Ki Afreen, xuciyata xata iya bugawa wllhi ina sonki son da ban tab'a yiwa kowane mahaluki ba a duniya. Pls Ki taimaka wa rayuwata " Zayyad ne ya fado mata a rai wane irin hali zai shiga? Allah sarki tausayinsa ne ya kama ta nan ta shiga xubda hawaye. Idan Saleem ne ya aureta shin wane irin Xama zasuyi? Ya xata fuskanci Anty Aysha? Wayyo rayuwa haka ta cigaba da kuka Shuraim ya kasa rarrashinta domin shi ynxu hankalinsa a tashe yake , sun share 30 mins cikin wannan hali a hankali ta xame jikinta da nasa wayarta ta d'auka tayi hanyar fita yayi saurin bin bayanta. Tafiya take amma bata da karfi ko kad'an a farfajiyar gidan ta samesu suna hira wato su Dada, Diddi da sauransu "sannun Ku " kawai tace ta wuce suna tausaya mata don Dada ta basu labarin daurin auren da zaayi gobe, Shuraim ya fito ya musu sallama a kofar gidan ya sameta jingine jikin gate yace " zo muje na sauke Ki"
Babu gardama ta bi bayansa don bata da option ya bud'e mata gidan gaba ta shiga sannan ya Ja motar suka tafi.
Mami na d'aki Afreen ta shigo da gudu ta fad'a jikinta " lafiya my baby meya faru? " " mami Ki taimakeni gobe zasu daura min aure" a razane mami ta tashi xaune tace " waat! Gobe? Innalillah " nan ta rungumi Afreen suka fara kuka "shikenan abunda nake gudu ya faru, ynxu Afreen ya zaki fara zama da Aysha a matsayin kishiya?" Da sauri ta d'aga jajayen idanunta tana kallon mami dakyar tace " mami u min ya Saleem zan aura?"
"Tabbas Saleem ne Mijin Ki don naji labarin gun ya Usman wai tunda shi ya fara cewa yana sonki dole Shuraim ya hakura" hannu tasa a kai "wayyo ni Afreen na mutu rayuwata tazo karshe" toshe mata baki mami tayi suka cigaba da kuka. sadiq ne ya shigo d'akin ganin halinda suke ciki yaje ya kira Abba a can bangarensa a rikice Abba ya xauna kusa dasu " lafiya Zee meke faruwa? " cikin muryar kuka Afreen tace " Abba sun rabani da Zayyad gobe zasu daura min aure da ya Saleem "
" wat? Gobe? Wannan wane irin gadara ne? Kai da d'anka amma a dinga nuna maka iko , gaskiya bazan lamince ba" xumbur ya tashi tsaye yace " bari naje a warware wannan matsala don gaskiya ban amince da wannan auren bah" ya fice daga cikin d'akin cike da bacin rai .sadiq ne ya xauna yana basu baki tare da kwantar musu da hankali har aka kira sallar magrib sannan ya fita mami ta lallaba Afreen sannan suka tashi don gabatar da salla .
Abba ya jira modibbo ya dawo daga masallaci sannan suka gaisa yace " naji sako gun Aisha amma ranka ya dad'e gaskiya ni bazan yiwa ya'ta auren dole bah donhaka a warware wannan maganar ,tana da wani Wanda take so " murmushi modibbo yayi yace" sai dai Ku kuyi hakuri don na riga na gama komai har na gayyaci mutane, donhaka Ku taya ta da adua Allah basu zaman lfy " idanun Abba sun rikida cikin sarkewar murya tace " amma ai ko addini bai ce haka ba"
"Nasani malam Aliyu, koma menene aure ne babu fashi" xumbur Abba ya mike yace " shikenan a daura amma yarinya babu inda xata " daga nan yayi ficewarsa dariya modibbo yake yana cewa " Duk Ku gama shirmenku aure ne anyi angama babu mai hanawa sai Allahn da ya kaddara" hmmmm.
Comments
Post a Comment