BOKO 🅰KIDA
💅💅💅
T.W.F 💦
(Hadin kanmu abin alfaharinmu)
Written by
Rukayya Sani Abubakar
(Maman khaleed)
Kacokam wannan shafin sadaukarwa ce gareki ,
U a such a darling friend, I wish to see ur wedding day with ur Deeee
#
ana tare
🤝
Zeelims(Adeela)
005
A nan falon Rahane ta kwana, kuka ta yishi har taji ba dadi, bacci kam duk iy satar sa be iya ya sace ta ba, gani take da zarar ta rufe idanunta zata bace, ga shi ko gafarar innanta da su baffa bata samu ta nema va, abinda ke qara saka ta kuka kenan.
Misalin qarfe tara da yan motsi na safe, ladidi aminiyar haj Rabi ta rangada sallama, sallsmar da se da ta kusa tafiya da numfashin Rahane.
Bayan gaishe2 da suka gabatar aka umarci Rahane data fito su tafi, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki take rakawa riqe da qullin kayabta, ladidi na biye da ita a baya.
Turus taja ta tsaya, ganin wata dalleliyar motar da tunda take a rayuwarta bata taba ganin ko wadda bata kaita ba, kuma ga motar me duhun gilasai ce,
Hawaye suka sake zubo mata, a nata tunanin tun a motar ma ai zasu yanka ta.
Ganin ladidi ta bude gidan baya hankali kwance ta shiga ta zauna, yasa tayi ta maza ta bude qofar a hankali ta fara zura kanta, kamar ace kyat ta zura da gudu,.
Sanyin AC daya bigi fuskarta yasa da hanzari tayi saurin futar da fuskarta waje tana maida numfashi.
A fusace ladidi ta zuro hannu ta fusgota cikin motar ta maida kofa ta rufe tana mita,
"Haba , se batawa mutane lokaci kike"
Rahane dai bata ce komai ba, idanun ta a runtse tana jiran ta inda za'a fara soka mata wuqa.
Manage this plxxxxcc
Comments
Post a Comment