💘 💘 _*'YAR UWATA*_ 💘 💘
_An awesome heartbroken lovetriangle story_ 💔
By ayshalove😘
💦💦💦 *talented writers forum* 💦💦💦
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆
💅🏻 *Dedicated to deejerh lurv* 💅🏻
pg 74
*×*+×*×+*×*+*
King mahbub ne zaune a garden yana waya da salman "haba salman meya samu wayarka kullum bata shiga har nagaji da neman ka"
"Wlh king naje wani daurin aure ne aka sace min wayar shiysa kajini shiru"
"Ayyah Allah kyauta akwai lbr fa I mean lbrn suhaila"
"Mtsw kaga ai ni naga ya maka wlh zan kiraki yayar ta maryam ta bani number ta kawai in kira ta in fada mata tunda kai kullum..."
Dariya mahbub yake ya katse shi yace "guy an barka a baya! An gaya maka da yanzu ce, tun yaushe soyayyar mu tayi nisa da suhaila!
"Ahh haba king are u serious? "Wlh da gaske nake fada maka yanzu haka ma lecture ta shiga nake jiran ta amma nan da en mintuna xatazo!"
Tab kace lbr se mun zauna amma am soo much happy king, yauwa ya batun wanan kayan ne? Kayi designing dinsu kuwa?
"no salman ban samu time bane amma insha Allah kabani 2 days ina gamawa xan maka sending seka gansu " "toh bakomai sena jika a gaida mutuniyar " toh xataji"
Yana kashe wayar yafara designing wasu jallabiya na maza masu kyau...
Suhaila ce take tahowa a hankali ta bayan mahbub rike da wasu flowers data tsunko masu kyau har ta karaso ta bayanshi be sani bah... zuba mishi flowers din tayi ta saman kanshi a nutse a ya daga kanshi ya duba sama se kuma ya juyo baya yana ganinta ta kyalkyale da dariya "ashe dai king din king din gaske ne naga baka tsoro" ta fada tare da juyawa ta gabanshi ta xauna "susu kenan inji tsoro se kace ke" ya lectures din? Susu na u look hungry muje kici abinci ko"
Kai king so kake cikina ya fashe da zamu shiga lectures fa mukaci abinci fa kai dai kace kaine kake jin yunwa"
Dariya yayi noo susu bana jin yunwa ko kadan nasan dai lectures din xata iya sawa kiji yunwa but tunda ba kijin yunwa it's owk"
"Susu na in tmby ki mna" owk tace kawai
"Ni tunda nake dake ban taba jin kince min mahbub ba sedai kice king ko bakisan sunana bane? Murmushi tayi wanda ya kara ma fuskar ta kyau "Ni I prefer na kira ka da king din ne kawai"
"Toh meysa?" "Sbd you are a king"
Cike da walwala a fuskar shi yace "if am a king then u must be da QUEEN" so daga yau kema sunan ki queen. Dariya tayi sosai sbd taji matukar dadi.
Wayar ta ta dauko ta kira ya ummi lokacin kuwa yaummi suna tare da dausiyya. Tunda taga wayar suhaila ya ummi gaban ta ya fadi dan tasan da wuya ba lbrn mahbub xata bata ba kamar yadda ta saba.
"Hello susu na ya kike"
Dausiyya kuwa tunda taji da susu take waya ranta ya baci a ranta tana ta takaicin ace mahbub ita yakeso gata yarinya mara kunya.
"Haba ya ummi wai meysa yanzu kike baya baya dani ne kullum sedai ni in kira ki yanzu kin dena so na ko" ta fada cike da Shagwaba
"Haba susu ki dena fadan haka, ai yanzu kin girma, yanxu fa ke ba yarinya bace susuna kinga kema yanzu xaki koyi iya zama ba tare damu bah ko kin manta fadan da abbah yayi mana lokacin tafiyar ki? Yanzu gashi nan a hankali kina sabawa"
"Toh ya ummi bakomai amma nidai dan Allah kar ki rage so na kinji? "Susu na baxan taba dena sonki bah"
"Yauwa ya ummi ga king ku gaisa" bata jira amsar ta bah ta mika mishi wayar
Wani irin abun ne yayi mata maqoqo a zuciyar ta kamar ta rusa ihu. Haka ta daure
"Hello babbar yaya kina lfy? Lfy lau, da anga xahra xa a ga wata yanzu kudai kullum kuna tare, dafatan kana kular min da er kanwar nan tawa kasan ita daya ce dani" "ai karki damu xan kula miki da ita kamar yadda xaki kula da ita"
Ga dausiyya muna tare ko xaku gaisa "owk ba damuwa bata wayar" ya ummi ta mika mata wayar, cikin fushi dausiyya ta dakatar da ita ni base mun gaisa bah, ya ummi tana mata nuni akan ta karbi wayar mana meye haka a hankali sbd gudun kar yaji mgnr da sukeyi amma taki karba. "Ahh king kaga an kira ta ma a waya" "owk ba damuwa" toh ya ummi nagode sosai a gaisa su umma toh nagode.. "my queen ga wayar" ya Miqa ma suhaila wayar, jin hakan kuwa ba karamin tayar wa ya ummi hankali yayi bah.
"Toh ya ummi bye" bye susu"
Tana kashe wayar ya ummi ta tashi ta nufi cikin gida ranta yana wani irin kuna! Kasancewar suna can garden din cikin gidansu...
Dausiyya ce ta bi bayan ta tana kiran sunan ta
Comments
Post a Comment