💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
*17&18*
*talented writers fans group wannan shafin naku ne tnx 4d lov n support, kuna kaunar wannan littafin most especially Rabiat Harun , Umme parrot😜, Anty dahare Nuri, n Fatima kina son mijinki😂😂 team ana tare🤝 love u all*😘😘😘😘❤
Hawaye ne suka fito a idanunta gaskiya taji Zafin marin kuma ta tsorata da lamarin Shuraim amma dole ta nuna masa itama jaruma ce🤣lol , ta kauda fuska gefe cikin muryar kuka tace " Allah ze sakamin " tayi kokarin bud'e kofar ta fita amma kash!! Ya kulle kofofin donhaka ta sunkuyar da kai ta fara masa kuka . runtse ido yayi yana jin Zafin ganinta cikin wannan halin amma dole ya koya mata hankali tsawa ya daka mata " ke! Ni abokin wasan Ki ne? Ba tambayar Ki nayi meya hadaki da matata bah? look am talking to u" cikin wani murya me ban tsoro yake magana donhaka ta d'aga kanta tana kallonsa ya tamke fuska tamau ganin babu alamar wasa a tattare dashi ne yasa tace " don Allah prof kayi hakuri ka bud'e min kofa zan koma gun mami na" hararinta yayi sannan yace " kisani cewa ni ba saan Ki bane kuma kada Ki nemi tashin hankali da matata don bana daukan wargi, next tym u shul mind ur business " nan ya bude mata kofa ba tare da yayi magana bah gaba daya taji haushin kalaman sa meyake nufi? Kenan ita ta fara Neman Salina da fada ko me? Tabb..yama gama raina mata wayo , meyake nufi da cewa tayi minding business nata? gaba d'aya taji ta kara tsanarsa nan ta fice cikin motar ko kallon inda gidansa yake batayi ba ta kama hanyar gidan Anty Aysha don bazata iya komawa gidan modibbo bah a cikin wannan halin da take ciki, wayarta yahau ruri Zayyad ne tayi saurin d'agawa " hello my beauty Queen I rily missed u ina kika shiga ne?" Kuka ta fashe masa tamkar yana kallon ta nan hankalin sa ya tashi " ya Allah! Beauty meke faruwa?"
Kuka take babu kakkautawa gaba daya Zayyad ya rikice yace mata " beauty kina ina we need to talk" sai ynxu tace " my hrt yau anci zarafi na an wulakanta ni Shuraim ya mareni" maganar yaso bashi dariya ya kanne yace " waye Shuraim? Me kika masa?" Kuka ta fara yi dakyar yake lallaba ta nan ta zayyana masa komai murmushi Zayyad yayi daga can bangaren lallai Afreen akwai yaranta amma ai tana da laifi don ita ta raina Shuraim dole ya dau mataki. Yayi gyaran murya yace " kin gane beauty na Ki fita harkar wannan Shuraim d'in kada Ki sake raina sa kuma ba ruwanki da matarsa OK" " Amma ai ita ta fara nemana da magana " " but beauty bata kira sunanki ba "
"Shikenan tunda kaima goyon bayansu kake"
"No..no beauty is just.." Diff ta kashe wayar tana share hawaye haka ta cigaba da tafiya babu mutane sosai akan titin estate din nasu a haka ta karasa gida , dama tasan inda suke ajiye key nan ta bude ta shiga babu Kowa kwanciya tayi bisa kujera ta cigaba da kukan ta Zayyad ya kira har ya gaji bata d'aga bah ya tura mata text taki ta karanta . karar mota taji bata damu tasan ko waye ne bah bayan minti 10 Saleem ya shigo tare da sallama yana ganin halin da take ciki ya rude " subhanallah! Queenie meke damun Ki" nan ta kara narkewa ya xauna kusa da ita ya fara rarrashi nan ta labarta masa komai ransa a bace domin Saleem baya son ganin an taba Afreen shi da matarsa an rasa gane waya fi son Afreen a cikinsu , cike da bacin rai yace " wannan ai zalunci ne me kika masa da zai mareki, gaskiya dole na taka masa birki don abin na Neman wuce gona da iri " murna fal zuciyarta ta kara gyara kwanciya ta kashe murya tace " wllhi my yaya kaina na min ciwo zazzabi nake ji" yasa hannu yana taba kan tare da cewa " sorry koh zan sameshi idan aka gama bikin nan OK, kiyi hakuri bazai kara tab'a Ki ba insha Allah " murmushi tayi tare da lumshe ido tace " nagode my yaya kai kadai kake sona " wani kallo ya mata sannan yace " I love u my lil sis shiga d'aki Ki kwanta Ki huta koh" "OK" nan ta tashi ta wuce d'akin bacci a yayinda yabi bayanta da ido yana murmushi tare da girgiza kai Afreen sai a slow.
A takaice de program d'in da Afreen bata halarta ba kenan washe garin ma anyi Fulani day bata Je bah haka nan ma walima , sai ranar fansa ne taje gidan modibbo ta gaisa da mami da sauran dangi sannan ta wuce d'akin Nenne can ne babu mutane sosai kwanciyar ta tayi tana buga game din naija ludo a cikin phn nata, Anty Aysha ce ta shigo tare da sallama ta xauna gefen gadon tace " Queenie yade " turo baki tayi ta fara magana cikin shagwaba " ni..ni ba kin share ni bah kinsa biki a gaba sai kika mance dani "
" haba de tawan wane ni ai kinsan ban xauna bane Kowa sai tambaya yake ina kika shiga, na shirya musu karya cewa kina mura ne shiyasa baki zo bah" dariya sukayi Afreen tace " yawwa Anty Hon Ahmed yana son Xuwa yau ya zamuyi dashi?"
Shiru antyn nata tayi na dan wani lokaci sannan tace " toh kuje gida man tunda ba Kowa" ido ta xare " wai..anty kina ganin family duk suna nan idan wani ya ganni fah?, tab wllhi tsoro nake ji" " kaji Ki da shegen tsoro toh waye ze ganku kuna falo ai ba a waje bane" shiru Afreen tai sannan tace " shikenan hakan zaayi " Anty Aysha ta mike bisa gado ta kwanta tace " bara na d'an huta wllhi na gaji " haka suka cigaba da hirarsu.
Hon Ahmed yazo gidan Anty Aysha kamar yanda suka shirya Afreen tayi kyau sosai sai wani murmushi take masa me Jan hankali gaba daya ya mato kanta he was so carried away😂 _chaii...yaudara_ hira sama-sama suke yace " pretty ya maganar gabatarwa" dum gaban ta ya Fadi ta wayance tace " haba my one ai na fad'a maka sai na gama secondary tukunna sannan mu fara xancen gabatarwa ko" " OK Allah ya nuna mana amma ni tsoro nake kada wani ya rigani"
"Haba de..ai ni taka ce kai kadai " haka de Afreen ta cigaba da xuba masa kalamai masu kwantar da hankali _'yan mata a rage yaudara pls_🌝 da yazo tafiya ya ajiye mata rafar kud'i sannan sukayi sallama ya tafi .
An gama taron biki lfy hutun su Afreen ya kare saura kwana biyu su koma skul , yau da yamma ta shirya ta tafi gidan mahaifinta xata karbo kud'in shopping tare da Zee suka tafi.
Katafaren falo ne na gani na fada a can na hango mutumin fari ne dogo kyakkyawa kusa dashi kuwa wani matashin saurayi ne me kama dashi sak! Retired major Aliyu kenan laptop ne suka sa a gaba , Afreen da Zee suka shigo tare da sallama "oyoyo Abba na" Afreen ta karasa inda suke murmushi ne ya bayyana a fuskar rtrd major " 'y'ar gidan Anty Aysha sai yau " zama tayi kusa dashi " ina yini Abba " "lfy ya sweet anty" dariya sukayi gaba daya nan zee ma ta gaishesu cikin girmamawa " ya sadeeq busy -busy " ta fada tana kallon dan uwan nata haka de suka fara hira har mami ta fito nan ta wuce gun mami ta fara xuba shagwaba zee de tana kallon ikon Allah " mami ina teemah ?" "ta Je islamiya sai 6 xata dawo " " hmm..su teemah auta ba, zee tashi mu haura sama " daga nan suka wuce d'akin ta wardrobe ta bud'e ta fara fidda kaya tana ajiyewa bisa gado tace " kinsan ynxu harkan big tym ne potential Ss3 gurls level don change dole a canza taku" dariya zee tayi tace " akwai harkar wanka kenan, irin ba renin nan" " hmm girl..Ki bari kawai ai 'yan Ss3 suna da aiki dani wllhi don zan koma da wannan phn d'ina"
"Wow..da gaske? Ki ce akwai harkar za-za kenan" "yesso..swagger d swaggerious"
"Oh me gosh..yarinya kina gingering dina" nan suka fara haukar tasu sunhera de ta tabe baki gefe tana kallon su, Afreen ta kwaso kananun kaya da night gowns masu Karen kyau sai kuma flat shoes kaloli daban-daban ta shirya kayan cikin wata er karamar akwati sannan suka fice Xuwa falo.
Kudade masu yawa major ya bata haka nan zee ma ta samu rabonta daga nan ta musu sallama suka tafi, wani shopping mall suka nufa me shegen kyau nan suka fara shopping d'in duk abunda zasu bukata wayar ta yayi kara Hon Ahmed ne babu bata lokaci ta d'aga bayan sun gaisa yake tambayarta ina take ? ta shaida masa tana shopping ya kashe wayar ta juya gun zee tace " momma Hon ze zo ynxu a wanki gayu kawai tawan" dariya sukayi harda tafawa sannan suka cigaba da shopping nasu, cikin kankanin lokaci Hon Ahmed yazo ya kirata a waya cewa ta fito waje yana jiranta cikin motarsa ta shiga ta xauna carab! Suka had'a ido da Shuraim yana tsaye kusa da motar waya yake amma hankalin sa na gun Afreen. Cikinta ne ya d'uri ruwa lokacin da ta hangoshi yana xuwan inda suke...
😳🤒🤒🤒🤔🤔
_me ze faru?_
*muje Xuwa*
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
*19&20*
*Anty fauzah wannan shafin naki ne antyn writers muna ji dake sosai-sosai Allah bar mana ke I ❤ u for real ana tare🤝😘😘*
Afreen ta tsorata ainun tun ranar da prof ya mareta ta fara jin tsoronsa haka ma ta tsaneshi ba kad'an bah, cikin takun qasaita ya karasa bangaren Hon ya tsaya tare da sallama nan ya mika masa hannu suka gaisa Ahmed yace " manyan prof Ashe kana gari I tot ka tafi seminar ai"
"No ina nan wllhi wife dina ce bata ji dad'i ba so I have to takkia of her tana bukatar kulawa daga gareni" dariya sukayi Ahmed yace " Shuraim iyayen soyayya har ynxu de kana nan kamar yanda na sanka Mr gentle " murmushi Shuraim yayi yana Satan kallon Afreen cos yayi missing nata sosai. Kawar da kanta gefe tayi tana kallon waje Hon yace " pretty meet my old friend prof Shuraim, tare mukayi karatu a university " juya ido tayi cikin wani salon yanga tace " aww..daz nice" " prof ga matar da zan aura insha Allah " Ahmed ya fada yana kallon Shuraim, murmushi yayi yace " daz gud Allah yasa ba yaudarar ka take yi bah Kasan halin matan ynxu sun fiya kyale-kyale"
Da sauri Afreen ta d'aga kai nan suka hada ido tare suka sakar wa juna harara Ahmed baisan meke faruwa ba yace " ah..haba no na yarda da ita cos she is very special " kada kai Shuraim yayi yace " okay yayi kyau bari na tafi matata tana can cikin mota tana jira na" " OK takkia a gaishe da madam" nan sukayi sallama ya tafi . a cikin zuciyart Afreen kuwa tsaki ta Ja tana jin haushin Shuraim ko meyasa Abu Kadan ya kawo zancen matarsa oho! Toh idan sonta yake ma dole sai Kowa ya sani ne mtsww...batasan cewa tsakin nata ya fito fili ba Ahmed yace " yadai?"
Murmushi tayi tare da cewa " no haka kawai naji na tsani wannan abokin naka" " cmon don't mind him in de Shuraim ne haka halinsa yake kiyi hakuri toh" nan ya xare rafar kud'i har bandir 3 yace " ga wannan ayi shopping lafiya ni zan wuce "
Ta wani langabar da kai "haba my one kullum kai Baka gajiya ne, gaskiya dawainiyar tayi yawa Nide ka rage " murmushi ya sakar mata tare da cewa " bana bukatar komai face soyayyar Ki so don't worry yiwa kai ne Allah bada saa sai munyi waya koh" nan ta bud'e kofar motar ta tsaya ya Ja motarsa tana d'aga masa hannu har ya tafi sannan ta sauke numfashi ta juya da niyyar komawa cikin mall d'in kenan taci karo da mutum😳
Shuraim ta gani tsaye a gabanta fuskar nan a murtuke nan ya fisge hannunta cikin mota ya turata sannan ya shiga ya kulle sai huci yake idanunsa sun kada sunyi jaja zir abin ya tsorata Afreen sosai don bata taba ganinsa cikin wannan yanayin bah nan jikinta ya fara rawa ta sunkuyar da kai tana kallon kasa , cikin kakkausar murya yace " wane irin rayuwa kika zabawa kanki? Shin akwai wacce kika taba ganin tana yin haka cikin family? Ko so kike Ki zubar da martaba da darajar modibbo's family? Me kika rasa Afreen ta zaki jefa rayuwarki ckn wannan garari? Meyasa kike son abin duniya haka? Meyasa kika zabi kiyi soyayya da d'a da uba Afreen tell me" ya karasa maganar cikin daka tsawa sai da ta firgita nan hawaye suka malale a kyakkyawar fuskar tata shiru yayi yana kallon ta wani irin kishinta yake ji kuma baya son ganin wannan hawayen nata.
Shiru sukayi a yayinda Afreen ta cigaba da rutsa kuka ya sassauta murya yace " sorry aff..but it hurts me alot idan na ganki tare da wani, ke karamar yarinya ce Ki bari sai kin gama makaranta sannan Ki fara soyayya amma u didn't " jajayen idanunta ta d'aga tana kallonsa cikin sarkewar murya tace " prof meyasa kake son takurawa rayuwata? Me na maka kake son sani a gaba? Nide kayi hakuri koma menene ka yafemin ka fita harka ta ka barni na rayu yanda nake so pls.." Tamkar yace mata yana sonta amma ya kasa furta hakan ya rasa me zai ce mata kawai ya tsinci kansa da cewa
" shikenan kije kiyi rayuwa irin Wanda kike so" daga nan ya bude mata kofa ta goge fuskar sannan ta fice ya had'a kansa da steree ya rasa meke masa dad'i gaskiya yayi nisa cikin kogin son yarinyar baisan ya zaiyi bah ga kuma tana da masoya harma tana sauraronsu shin me makomar soyayyarsa gareta oho!
Afreen kam ta wuce cikin mall can ta hango zee na xaune tana ganinta ta hada rai " haba Afreen ya zaki ajiyeni haka?" "Am sorry momma muje na biya kud'in mu tafi" nan ta biya suka fito rike da ledojin zee ta kalleta tace " lafiya naga kin canza min "
"Momma na rasa meyasa ya Shuraim yake takurawa rayuwata" nan ta kwashe labarin komai ta fada mata , zee tace " kodai sonki yake ne baby" wani kallo Afreen tai mata tace " hmm..kinsan hakan bazai taba faruwa bah" " toh shikenan Allah ya kyauta" suna tsaye a gefen titi sai ga motar Shuraim tazo ta wuce su Afreen tayi mamaki don a tunaninta ya tafi tun dazu toh ina matarsa da yace tana jiransa a mota? Shin meyasa yace tana soyayya da uba da 'da? Wannan tambayoyin sun tsaya mata a rai har suka samo keke suka wuce gida bata daina tunani bah.
**********
Har suka koma skul Afreen bata sake sanya Shuraim a ido bah gashi tana da tambayoyin da take son masa kud'i ta bama wani security ya boye mata akwatin kayan sawar da ta shigo dasu da kuma phn nata sai dare tazo ta karba don ana hanasu Xuwa da waya a skul, haka rayuwa ta cigaba su Afreen an zama seniors sai fisga ake gashi duk group nasu an basu post na prefects Afreen ce *DSP* wato deputy senior prefect ( deputy head girl) ko'ina sunan ta kake ji cikin hostel kuwa wankan da take baa magana ga kuma arniyar phn nata 1 in town gashi Kowa yasan dan gwamna ke son auranta abin de sai shaking ya sanya ta kanta na rawa ga iskanci iri-iri da suke nuna wa 'yan Ss3 kullum sai an tura mata letter ana sonta da momy ko senior pal amma ko kallon lettern bata yi su Afra ne suke karantawa, haka de suka cigaba da karatu kullum sai tayi waya da anty Aysha da kuma masoyan nata musamman Zayyad Wanda gaba daya ya gama sace mata zuciya.
*Agurguje*
_1 year later_ su Afreen an gama secondary skul ynxu tana da 18yrs sun fito da sakamako me kyau nan aka sama musu admission a *AUN* ita da Zee da Afiya, su Afra kuwa sun tafi *Mautech* cikin kankanin lokaci aka gama musu komai suka fara Xuwa . Afreen tana karanta bangaren accounting kullum bata da lokaci ynxu sun rage haduwa da Zayyad ma sai jefi-jefi Shuraim kam ya d'auke mata wuta ynxu bata ga fuska ba ma bare ta raina shi don ana matukar girmama shi a makarantar har mamaki abin yake bata ga mata kuwa Duk inda aka had'u sai hirarsa ake daga masu cewa suna son shi sai masu cewa ina ma ya auresu gasunan de itakam tana mamakin irin farin jinin da Allah ya masa ko dan bata tab'a tsayawa ta kare masa kallo ne oho!
Sun gama first semester Zayyad ya nace mata da batun aure tace ya kara hakuri sai ta gama 100 level ana cikin hakan ne modibbo ya had'a family meeting inda akayi baikon su Afra, jameela da kuma maryam duk de cikin jikokin nasa ne wato tuwo na maina nan da nan aka fara shirye-shiryen biki don dukkansu auren so ne dama can suna son junansu shikenan , su Afreen kirjin biki sai safa da marwa ake ana ta zarya tsakanin kasuwa da gun tailor da gidan gyaran jiki kullum tana busy .
Yau suna xaune ana musu lalle Zee tazo tace " baby kizo kiji wata sabuwa inji 'yan caca" ta xare ido "toh...meya faru?" Nan ta jawota gefe tace " Ashe Hon kanin gwamna ne" "waat? Ki rantse innalillah ina kika ji?"
"Hmm ynx a can cikin gida naji ana hira wai aure zeyi next week" "waat? Ahmed dina zeyi aure? Kutuma lallai zaayi bala'i , ni Ahmed zai raina wa hankali ban wayata na kira shegen" dariya zee tayi tace " shegiya y'ar duniya dama sonsa kike ne? Ke ina ruwanki da aurensa tunda dama can Zayyad kike so" "but momma koma menene ai ya dace ya sanar dani koh" "hmm baby akwai rigima wllhi ga kishin tsiya" Afreen se huci take ta fara kiran layin Hon bugu biyu ya katse ya kira cikin bala'i ta fara magana " macuci mayaudari ashe dama haka halin ka yake"
"Calm down pretty let me explain" "explain wat! Hang it to ur self naji labarin auren ka a gari nagode da yaudara" "haba pretty Ki saurareni, wallh ina kaunar Ki har ynxu kawai de naji labarin cewa a dangin Ku baa yin auren bare an gayamin na daina bata lokaci na don ba samunki zanyi bah shiyasa nayi deciding to let u go, ba don na daina sonki ba sai don tsira da mutunci na am getting older shekaru na 46 har ynxu banyi aure ba sai yaushe zanyi.. Kiyi hakuri Ki yafemin wllhi ba yaudarar Ki nayi bah I love u" jikinta yayi sanyi tace " is OK na gane kuma nagode sosai Allah bada zaman lfy " nan ta kashe wayar tana hawaye gaba daya taji ba dad'i wani irin kishi take ji shikenan ta rabu da Ahmed har abada .
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
*23&24*
*Fans kuyi hakuri masu korafin cewa bana posting dayawa u knw is nt easy , up n down busy here n dere so just manage tnx 4ur love n kia ina sonku sosai wannan shafin naku ne masoyan "Zumunci"*❤❤❤❤
Anty Aysha na faman rarrashin Afreen kawai ta ga Salina tsaye akanta a hasale Salina ta fara magana " ke tsohuwar munafuka tashi Ki saurareni da kyau kiji abunda zan gaya miki, mijina ba saan Ki bane gara tun wuri Ki fita harkarsa ko na dau mataki akan Ki " anty Aysha tace " lafiya de Salina meya faru?"
"Ki tambayi wannan karuwar wallh mijina yafi karfin Ki matsiyaciya kawai mai bin maza" aikuwa cikin Zafin nama Afreen ta tashi ta d'auke ta da mari tare da nunata da yatsa " Ki kiyaye kada Ki sake cemin karuwa kuma wllhi Ki fita tsabgata ko kiyi nadama ,ke har wani Mijin gareki da zaki tsaya tada jijiyoyin wuya?" Kukan kura Salina tayi ta shake rigar Afreen aikuwa kokawa ta tashi dakyar aka banbare Salina jikin Afreen sai maida numfashi suke, abin de har ya fara jawo hankulan jama'a ganin haka Anty Aysha tayi waje da Afreen Shuraim kuwa ya karasa gun matarsa ya fisge hannunta sukayi waje sai bala'i take surfa mata.
Cikin mota ya jefata tare da wanka mata mari " ke wace irin dabba ce? a cikin bainar jama'a zakije Ki tada xaune tsaye? So kike Ki b'ata sunan danginmu ya zama topic of discussion a gari? Wai meke damunki ne Salina "
Cikin muryar kuka tace " shine zaka mareni sabida wannan yarinyar? Wllhi bazan yarda bah a cuceni a hanani daukan mataki, wllhi sai na hallaka wannan shegiyar ni babu wata shegiya da xata shigo min gida. Idan kana mafarkin aurenta ne gara ka farfado don wllhi bazai tab'a faruwa ba" murmushi Shuraim yayi kai Salina akwai kishi , daga nan ya Ja motar ya wuce gida da ita.
Afreen kuwa tambayar duniya Anty Aysha ta mata akan meya hadasu da Salina atafau tace ita bata San komai ba daga nan Saleem yazo ya d'auke su suka wuce gida tun baa gama program bah.
**********
Mai girma gwamna ne tare da Zayyad suna tattaunawa akan batun auren Hon Ahmed suna cikin magana Ahmed ya shigo zama yayi kusa da yayan nasa , murmushi gwamna yayi tare da cewa " ango ka sha qamshi" tsaki ya Ja yace " yaya kafi Kowa sanin auren nan zanyi shi ne badon ina so bah " "nasani but kayi hakuri Ahmed tunda an Baka yarinyar nan pls karka kunyata mu just accept it, nasan kafi son y'ar gidan rtd major Aliyu but kayi hakuri mayb wannan shine alherin ka" da sauri Zayyad ya d'aga kai yana kallon mahaifin nasa . Ahmed yace " wllhi yaya ina kaunar yarinyar, jiya ta kirani cike da bacin rai wllhi I felt guilty " yayan nasa ya rike shi a kafada yace " b strong bro komai daga Allah ne kayi hakuri "
Zayyad yace " dad u min dama uncle wata yake so daban?" "Yes son! Uncle naka yana soyayya ne da wata y'ar gidan rtd major sai kuma wani abokina ya bashi y'arsa ya aura" wani irin zafi da radadi Zayyad yake ji cikin zuciyarsa yana son tabbatar da zargin da yake . cikin in-ina yace " rtd major Aliyu Wanda yake dougirei? " "yes Kasan shi ne?" "Um..ehh nasan d'ansa abokina ne" daga nan Zayyad ya mike zumbur yace " dad bari na dan kwanta Xuwa anjima zamu cigaba da tsare-tsaren" kai tsaye d'akinsa ya wuce idanunsa a rufe kishi ne ya baibayeshi wani irin haushin Afreen yake ji tabbas itace domin su biyu ne kadai mata a gidan major kuma itace babba, wayarsa ya d'auko bugu d'aya tayi picking daga can bangaren tace " hello my hrt!"
"To hell wit ur heart Ashe dama yaudarata kike? Ki rasa cin amanar da zaki min sai na soyayya da kanin mahaifina? Me na miki Afreen" karo na farko da ya fara kiran sunanta kai tsaye tun lokacin da suka fara soyayya.
"Kayi hakuri let me explain, wllhi bansan..." "Shut up my friend.. har kina da wani explanation da zaki min? dama ai mata duk halinku d'aya" yana magana cikin tsawa da d'aga murya , Afreen ta fara hawaye cikin muryar kuka tace " am sorry pls ka saurareni kaji ..." "U knw wat Afreen, I hate u na tsaneki" duff ya kashe wayar idanunsa sun rikida sun zama Ja kwanciya yayi a gado ya rasa meke masa dad'i a duniya.
Daga can bangaren Afreen kuwa kwala ihu tayi tayi jifa da wayan bisa gado nan tayi rub da ciki ta fara rusa kuka tamkar wacce aka aikowa sakon mutuwa, tana cikin wannan halin taji saukar wasu tagwayen mari sai da taga taurari tamkar a mafarki ta juya Anty Aysha ta gani tsaye a kanta sai huci take tamkar wani mayunwacin zaki " shegiya munafuka Ashe gaskiyan Salina da tace kina bin maza, abunda zaki saka min dashi kenan Afreen " (yau babu Queenie😝😂😂 kishi kumallo) Afreen ta tashi dakyar tana rike da inda aka mareta fuskar ta hawaye cabe-cabe cikin wata murya me ban tausayi tace " me na miki Anty Aysha yau kece kika mareni? Allah yasa de mafarki nake"
" ke ni ko kasheki zanyi akan mijina , kuma Ki tattara ynxu kibar min gida na shegiya munafuka Ashe munafuntata kuke kuna cin amanata. Toh wllhi karya kike babu ke babu Saleem har abada tashi Ki bar min gida " ta karasa maganar cikin Zafin rai. Waya da gyale kawai Afreen ta d'auka bata nemi Karin bayani ba don ta gane kan zaren donhaka ta wuce Anty Aysha ta bi bayanta da uwar harara .
Tafiya take cikin estate d'in nasu tana share hawaye lokaci Xuwa lokaci wai meke shirin faruwa da rayuwarta ne?? Wayar Zayyad ta kira ya danna mata busy ta sake kira ya danna busy a karo na ukun ne ya kashe wayar gaba daya kuka ta cigaba da yi tana tuna kalaman Anty Aysha toh meya faru? haka ta karasa gidan modibbo har ta manta da zancen wani biki ma , duk inda ta wuce kallonta ake har ta fara jin wani iri bangaren Dada ta wuce mami ta gani tare da Dada da kuma uncle Usman. A gefe ta risina ta gaishesu sannan ta wuce uwar daka ta fad'a gado ta cigaba da kukan ta, bayan mintuna 10 sai ga mami ta shigo ta xauna gefenta tace " tashi Ki share hawayn magana zamuyi "
Babu gardama ta tashi xaune tana share fuskar da gyalenta " yaushe kuka fara soyayya da Saleem? "
Xare ido tayi tana mamakin wannan tambayar Mami tace " magana nake miki kika min shiru " a hankali tace " Nide bamu tab'a soyayya bah, mami ya Saleem Mijin Anty Aysha ne ya zaayi na.." Hannu mami ta d'aga mata nan tayi shiru mamin ta cigaba da magana " Shuraim kuma fah?" Gabanta ne ya bada wani sauti dam! Tayi saurin girgiza kai tace " aah 'aah ni bana soyayya da Kowa" shiru mami tayi na wani dan lokaci sannan ta tashi ta fita.
"Innalillahi..wai meke faruwa ne?" Wayarta ta d'auka ta kira Zee "hello momma don Allah Ki sameni d'akin Dada" ta katse kiran ta gyara zama ta nemi hawayen ta rasa, cikin dakika 10 zee ta shigo tare da sallama ko Xama batayi ba ta fara magana " ai ko baki kirani dole zan nemeki baby, gaba d'aya kin hargitsa family kina Neman warware *Zumunci* " ido Afreen ta xare tace " bangane ba meke faruwa? Ni bansan komai ba kawai Anty Aysha ba sai ta tsinkamin marin da yasa na kusan Xuwa lahira bah"
Dariya zee tayi tace " ai dole kuwa wllhi nasan xata ji ba dad'i " cikin fuskar damuwa Afreen tace " don Allah momma Ki gayamin meya faru?"
" ke komai ma ya faru, har uwar Salina fa tazo nan da safe kuma abin haushin ma harda kakansu yana goyon bayan maganar. Kedai anyi baram-baram"
"Don Allah Ki min dalla2* ni ban gane kome bah, meya kawo Maman Salina?" " gyara zama Ki sha labari" nan kuwa Afreen ta baza kunne...
Comments
Post a Comment