Skip to main content

ZUMUNCI NA SUNHERA

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na_*Sunhera*_

💦 *Talented writers forum*💦

   *T.W.F*

    *dedicated to Reefat yahya*
  

💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝

𷠽𷠮 *25&26*

*masu tambayar dangatakar dake tsakanin Afreen da Anty Aysha Ku duba page 5&6 anan akayi bayani akan tushen modibbo's family tnx love u all*😘

Zee ta fara magana da cewa " yau da safe bayan family sun taru a falon modibbo kamar yanda aka saba a nan ne ya Saleem ya gabatar da bukatarsa na Neman auren Ki " "waat...Neman aurena ? Ya Saleem? Meke damunsa? Ya Allah no wonder Anty Aysha tayi reacting gosh! Wat is wrong wit him..beside he din kia to talk to me first , meyasa zaimin haka?" Zee tace " gaskiya ya kwafsa don yanda kike da Anty Aysha bai dace a ce kun zama kishiyoyi bah"
    "Hey stop it! Ya zaayi na auri ya Saleem u knw I can't, gara ma su daina b'ata lokacin su ni Zayyad zan aura" zee ta gyara zama tace " ai ban gama bah, bayan ya Saleem ya gama maganar sa ya Shuraim yace shi ya dade yana son gabatar da maganar amma gani yayi kina makaranta shiyasa ya dakata. Hayaniya suka fara tsakanin su nan kuwa kakan Salina yace atafau ya Shuraim bazai had'a 'yan uwa a gida d'aya bah haka ma Maman Anty Aysha ta fara surutu kedai anyi baran -baran modibbo de ko uffan bai ce musu bah, bayan an watse ne Salina da Maman ta suka zo sukayi ta surfa bala'i iri-iri babu zagin da basu yiwa mami ba amma babu Wanda ya kulasu daga karshe suka tafi. Toh baby kin dai ji abunda yake faruwa akwai rikici wllhi "  tagumi Afreen tayi sannan tace
  "Ni wannan duk be dameni bah, Zayyad yayi fushi dani ya daina picking call dina" nan ta labartawa zee abunda ya faru Zee tace " gaskiya kina cikin matsala Allah de ya warware matsalolin " "ameen " ta amsa cikin sanyin murya.

Mami ce ta shigo rike da tray ta ajiye a kasa tace " sauko Kuyi kari na tabbata baki ci komai ba" bata son gardama da mami shiyasa ta sauko kasan kafet ta xauna Zee kam tace ta k'oshi nan mami ta xubawa Afreen chips a plate sannan ta had'a mata tea me kauri ta mika mata , a hankali take cin dankalin gaba daya bata jin taste nashi hankalin ta na gun Zayyad batasan ya zatayi ya saurareta bah ga uwa uba Anty Aysha da take fushi da ita. Ya zatayi ta fahimtar da Anty Aysha cewa Saleem bai tab'a furta mata Kalmar so bah? haka de ta cigaba da tunani kad'an taci ta kurba tea tace ya isheta , gado ta koma tayi kwanciyar ta hira sama 2* suke da zee a yayinda mami ta tattara kayan tayi waje dasu.

******
Modibbo ne tare da matansa a falo wato Dada,Diddi, nenne da adda kowacce tayi shiru suna saurarinsa yace " kundai ga abunda ya faru yau da safe donhaka na tara Ku anan ina son jin shawarar Ku" Dada tace " ni a gani na gara abar wannan zancen domin kuwa akwai matsala , idan aka bawa d'aya an hana d'aya babu adalci .sannan maganar na neman jawo matsala cikin dangi ni ina ganin gara su hakura kawai" nenne tace " maganar Ki gaskiya ne ni ina goyon bayan dada"
     Adda tace " gaskiya idan ta auri Saleem baa yiwa Aysha adalci ba idan akayi laakarin cewa a gidan ta xauna, Aysha ta d'auke ta ne tamkar y'ar da ta haifa kunga hakan zai jawo matsala na rashin zaman lfy ina ganin a had'a ta da Shuraim zai fi" Diddi tace " anya xata iya zama da matar Shuraim kuwa? Ke kina gani har malam Bukar bai bada goyon bayan auren bah" gyaran murya modibbo Tukur yayi yace " shikenan Duk naji bayanan Ku tashi kuje zanyi nazari akai " nan suka tashi kowacce ta wuce bangaren ta.
   Da yamma anyi walima amma Afreen bata samu halarta bah tana can tana fama da matsalolin da take ciki, washegarin ma daurin aure akayi sannan aka wuce da amare gidajen su a takaice de Afreen bata sake attending kowane program bah har aka gama bikin. Shuraim ya damu yana son ganinta amma ya rasa wa zai  tambaya Salina kam sai ruwan bala'i take masa a gida baya kulata sabgarsa yake.

   Afreen tana xaune a falon Dada tare da zee wacce ta dawo daga daukar kayan Afreen a can gidan Anty Aysha. cikin kwana biyun ta rame ta xube kamar ba ita bah zee sai fad'a take mata akan ta rage yawan tunani , Shuraim ne yayi sallama ya shigo carab! Suka had'a ido tsaki Afreen ta Ja tare da barin falon d'akin bacci ta shige Shuraim kuwa yabi bayanta . ya kulle kofar d'akin da key sannan ya dawo kusa da ita ya xauna tare da kura mata idanu kawar da kai tayi tace " me kake bukata?"
  "Soyayyar Ki" kai tsaye ya bata amsa " prof don Allah na rokeka ka fita tsabga ta I told u bana son ka wai dole ne?". "Yes my Queen dole Ki soni kuma wataran insha Allah zaki soni " tsaki ta Ja tare da yin kasa-kasa da murya tace " maye kawai" batayi tunani zaiji me ta fad'a ba ga mamakin ta sai taji yace " yau zan nuna miki maytancin kuwa" hannu yasa ya jawota yau ma kissing nata yayi tamkar bazai barta bah, tayi kokarin tura shi amma ta kasa sai da yayi mai isarsa sannan ya sake ta nan ta fashe da kuka tace " Allah ya isa min dan iska kawai " murmushi yayi yace " dan iskan zaki aura insha Allah " yana gama fadin haka ya tashi tare da gyara hularsa ya bud'e d'akin ya fice.
   Kuka ta cigaba da yi ta tuna ranar da ya fara kissing nata wani kunya ne ya kamata ta lumshe ido tana murmushi tare da share hawayen a hankali tace " Allah sarki my Zayyad wani ya rigaka kissing dina, I got my first kiss from d wrong person " kwanciya tayi tana dialing number d'in Zayyad amma is switch off haka ta hakura.
Angama biki lafiya an watse Afreen kuwa ta dan saki ranta ta koma makaranta ynxu sun shiga second semester Zayyad kuwa yana can yana fama da ciwon sonta dakyar iyayensa suka lallaba ya gaya musu cewa wata yake so babu b'ata lokaci gwamna ya shirya yaje gun Abban Afreen akan cewa yazo nemawa d'ansa auren ta , major yace zai sanar dasu halin da ake ciki nan da sati biyu.
    Afreen ta koma gidan modibbo da Xama donhaka mahaifin nata ya aika kiranta bayan ta gama lectures ta wuce gidan. A falo ta same su tare da mami suna tattaunawa zama tayi suka gaisa nan Abba ya fara magana " baby kinsan  Zayyad ?" Dam..gabanta ya fadi a hankali tace " ehh" murmushi Abba yayi yace " tun yaushe kuka fara soyayya " sunkuyar da kai tayi ta kasa magana, mami de sai kallon y'ar tata take "Kina sonsa ne?" Abba ya sake jefa mata tambaya nan ma shiru tayi amma fuskar ta na d'auke da murmushi. " shikenan tashi Ki tafi Allah ya miki albarka" "Ameen " mami ta amsa daga nan Afreen ta haura sama ta barsu.

    Abba yace " I tink suna son juna sosai " mami tace " hmm..ni modibbo nake ji ,bansan ya zai karbi zancen bah .cewa zaiyi ni na zuga ta" " kwantar da hankalin Ki komai zaizo da sauki insha Allah "
"toh Allah yasa..amma de da kamar wuya nasan sai an gwabza" haka suka cigaba da tattauna kan maganar Afreen.
    Bayan kwana biyu Abba ya shirya yaje gun modibbo a falo suka xauna bayan sun gaisa yace " ranka ya dad'e dama nazo kan maganar Aisha ne, gwamna yaje waje na yana nemawa d'ansa aurenta" murmushi modibbo yayi yace " toh ita Zainabun bata fad'a maka cewa na mata miji bane?" Shiru Abba yayi modibbo ya cigaba da cewa " wato so take y'ar tata tabi sahun kafarta gun auren bare koh? Toh ka koma ka gaya musu anyi mata miji " Abba de ya rasa bakin magana domin modibbo akwai kwarjini. Ganin Abba baice komai ba yasa modibbo cewa
" zuria ta sun daina auren bare daga kan zainabu ita ma tsananin rabo ne donhaka ni ban amince da wannan auren bah"
   " amma ranka ya dad'e bai kamata babban mutum kamar gwamna a ce ya nemi Abu kuma a hanasa bah, gani nayi yarinyar tana son d'an nasa toh me zai..." "Dakata Aliyu aure ne ba zaayi bah na riga na zaba mata miji ka gane koh" ran Abba ya baci nan ya tashi tsaye yace " Allah ya taimakeka ya'ta ce ni nake da ikon aurar da ita ba wani bah donhaka kuma bazan tauye mata hakki bah dole ta auri Wanda take so, dama ba shawara nazo yi ba nazo sanar da kai ne a matsayin ka na kaka a wajenta na barka lafiya " yana gama magana ya fice cike da bacin rai.
Modibbo ya fara karkada kafafu ransa baki kirin yace " lallai Aliyu wuyan ka yayi k'auri amma zan nuna maka har ynxu kai yaro ne, ba aurar da ita zakayi bah..shikenan xan nuna maka ina da iko akan zuriya ta"

*tohfah akwai chakwakiya muje dai Xuwa*🤔🤔🤔

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na_*Sunhera*_

💦 *Talented writers forum*💦

   *T.W.F*

    *dedicated to Reefat yahya*
  

💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝

𷠽𷠮 *21&22*

*Shout out to dis young lady Faty Azland❤ yau ranar Ki ce hip! hip!! hip!!! Hurray....its ur day happy birthday Mrs lamido wishing u many more fruitful years ahead , may Almighty Allah shower u his blessings kip calm n celebrate❤❤❤❤❤ ..Reefat tace "ana tare🤝🤝*

Yinin ranar Afreen ta yi shi ne cikin damuwa ita kanta ta rasa meyasa taji haushin auren Ahmed bayan ta tabbata Zayyad take so. Xaune suke da amaren suna hirar yanda zasu gudanar da program d'in *sisters n brodas nyt* da zasu yi yau da dare wayar Afreen tayi kara bata duba ko waye ne ba ta katse tare da Jan tsaki Zee tace " wai ni baby lafiyan Ki kuwa? Shikenan don saurayin Ki zaiyi aure sai kibi Ki tada hankalin Ki, gani nayi de kince baki sonsa " dariya afiya tayi tace " chabb..ashe bakisan Queenie da kishin tsiya bah ai na tausayawa mijinta wllhi don zai sha fama" banza tayi dasu ta gyara kwanciyar ta , wayar Afra tayi ringing nan ta d'aga " halo ya Saleem.. Na'am lafiya Alhamdllh, Ameen nagode " sai kuma tayi shiru sannan tace " ehh gata nan muna tare"
    Nan ta mikawa Afreen waya tare da cewa " sweet yayan Ki ne"
     Ta kai hannu ta karba " hello my yaya" tayi shiru na dan wani lokaci sannan tace " Allah yaya ni na k'oshi" ta tura baki cikin shagwaba can kuma tace " toh shikenan a kawomin da hollandia milk me sanyi ..OK tnk u , u too" ta kashe wayar ta ajiye.

  Afiya tamkar jira take su gama wayar ta fara magana " kai Queenie y'ar gata , Anty Aysha da ya Saleem de na rasa waya fi sonki wllhi amma gaskiya suna shagwaba Ki sosai gara a dan rage" zee tace " wallh wani lokaci ni kuma gani nake tamkar ya Saleem na son Queenie " dariya sukayi gaba daya Afreen tace " ai kema kinsan babu haka tsakanina dashi kawai shakuwa ce"  haka suka cigaba da hirar cikin kankanin lokaci akayi sallama wani yaro ya shigo da ledoji yace an aikesa gun Afreen daga nan ya ajiye ya tafi.
   Bud'e ledojin sukayi kaji ne gasassu sai pizza da meat pie sai da hollandia milk guda 3 , ihu su Afra suke suna cewa " sai y'ar gatar yaya Saleem " babu bata lokaci suka hau ci.

   K'ayataccen hall ne Wanda yasha decoration abin de baa cewa komai  an ware filin zaman amaren daban haka nan ma kawayen amarya da abokan ango .
      _9:00pm_ hall d'in ya cika makil da jama'a maza da mata abin mamaki shine babu yara a cikin hall d'in wato de an tsara komai , Duk inda ka duba familyn modibbo ne Fulani kyawawa farare suka fi yawa akwai bakaken ma de . *9:40* amaren suka shigo Afra tana sanye da pink material ,jameela kuma blue sai maryam kuma maroon n silver gaba daya sunyi kyau sai d'aukarsu hotuna ake har suka karasa wurin zaman su sannan kawaye suka shigo . Afreen na hango cikin shiga ta doguwar riga red n silver material sannan ta xuba gashin kanta a kafad'a tayi balain yin kyau kamar a saceta a gudu, cikin kankanin lokaci aka fara gudanar da program yawanci familyn su sai abokan arxiki Duk abokan angwayen hankalin su na gun Afreen wacce batasan suna yi bah.

    Shuraim ne da Saleem suna xaune cikin mota a waje Saleem yace " pls prof mu shiga ciki, family duk an taru banda mu" Shuraim yace " Kasan ni banson raini ka ga kuma Duk kannen mu ne a ciki shiyasa bana son shiga, mayb ma akwai students dina a cikin friends nasu"
   " haba man! Su mustafa da shuaib da su Ahmed , Suleiman Duk fa suna ciki.muje don Allah " " sorry Saleem I can't " tsaki saleem ya Ja tare da cewa " toh da meya kawo ka?"
"Uhm..Salina ce ta dage  wai dole sai na jirata If nt da na tafi gida" Saleem ya fice cikin jin haushi ya wuce Xuwa cikin hall d'in, Shuraim ya buga tagumi yana son ganin Afreen yasan tayi kwalliya tayi kyau amma bazai iya shiga bah.

A can cikin hall kuwa zaayi indian dance ne Kowa ya dage lallai Afreen ce zatayi tunda dama ta iya dole ta tashi ita da Mijin Afra mai suna sudais tare zasuyi rawar, wakar da tafi so aka sanya musu wato wakar *latlagee* cikin kwarewa ta fara da farko tana jin kunya daga baya kuma ta ajiye kunya gefe ganin cewa duk family ne , sudais ma ba dama rawa yake tamkar shi yayi wakar haba wa ai mutane sunyi caa! A Kansu ana musu ruwan kud'i. Anty Aysha da mijinta sun shiga tare suna tsokanar Afreen ga abokan angon duk sunyo kanta, Shuraim dake cikin mota da ya ji wakar nan ya tuna ranar da ya fara ganin Afreen a can FGGC yola nam zuciyar shi ta fara harb'awa ya tabbata rawa take nan yaji kishi ya turnukesa dole ya shiga ya ganawa idanunsa .
Su Afreen ana can ana rawa jama'a sai xuba mata kud'i suke  Shuraim ya tsaya gefe yana kallon ta ana cikin haka ne Dj ya canza waka Xuwa wakar *salaama yaa* na veer nan yan maza da matan familyn suka tashi dama duk sun iya miming wakar , layi sukayi na maza daban mata daban harda Anty Aysha da mijinta sun shiga nan aka fara rawa gwanin shaawa anayi ana canza partner yayi dai-dai akan Afreen da Saleem. Murmushi Afreen take masa a yayinda shi kuma ya kura mata ido babu ko kiftawa har tsigar jikinta ya tashi nan ta sunkuyar da kanta kasa Saleem yasa hannu ya d'aga habarta suka kurawa juna ido har sunyi nisa babu Wanda ya kula dasu, kamar a mafarki aka fisge hannun Afreen aka kutsa cikin mutane da ita Saleem ya shiga dube-dube amma babu alamar su .

   Can bayan hall d'in suka tsaya sai sauke numfashi take gaba d'aya ta tsorata don batasan waye ne bah domin akwai dan duhu a wannan bangaren cikin muryar tsoro tace " don Allah waye kai me na maka ?" Murmushi Shuraim yayi a hankali ya jawota jikinsa ya rungume ta gam zuciyar Afreen sai bugawa take nan ta fara hawaye tace " don Allah kayi hakuri karka cutar dani" cikin muryar rada yace " babu abunda zan miki kawai ina kishin ganin wani namiji kusa dake ne shiyasa na kawoki nan, but trust me bazan cutar dake bah"
  Shiru tai tana son tuna ina tasan wannan muryar amma ta kasa tunawa , wata mota ce ta haska su da fitilar ta Afreen ta lumshe ido batason hasken a razane wacce take cikin motar ta kare musu kallo sannan ta kashe fitilar ta fito a guje ta wuce cikin hall d'in don bata yarda da abinda idanunta suka gane mata ba.
   Shuraim ya rike hannun Afreen suka bar wajen wani lungu suka shiga ita de bata yarda dashi bah sai adua take cikin xuci yayi kasa-kasa da murya yace "  pls Ki min alkawarin cewa bazaki sake yin rawa ba idan kika koma ciki" shiru tayi tanason gane wanene " kinyi shiru pls talk to me" banza tayi dashi sai kuma yace " shikenan tunda naga kinfi son zama dani a nan let's sit" da sauri tace " don Allah waye kai ya sunan ka?" Murmushi mai sauti yayi dama yasan bata gane shi bane da xata fara masa tsiwa  , waya ya cire ya haska fuskarsa yace " hop ynxu kin gane ni" cike da mmki tace " wat? Shuraim dama Kaine? Shii..I can't bliv dis"
   Ya kai hannu zai riketa tayi saurin buge hannayen tare da cewa " dama rashin sani ne yasa na kyale ka rungumeni but not again " cikin Zafin nama ya jawota nan ya had'a bakinsa da nata ya fara kissing nata passionately gaba d'aya jikinta ya mutu is her first tym. Sun share minti 3 cikin wannan yanayin sannan ya saketa yace " idan kika sake min tsiwa wannan shine abunda zan miki "
Kuka ta fara yi Reefat tace wai ..daga baya kenan😝😝  ya sake jawota a jiki yana rarrashi " am sorry my Queen na dad'e ina fama da ciwon sonki I can't hide it anymore I love u Afreen, I truely love u and I want to marry u" a firgice ta d'aga kanta tana kallonsa duk da cewa cikin duhu suke nan ta kwace jikinta tace

"I hate u ya Shuraim, bana sonka bana kaunar ka kuma bazan tab'a sonka ba " tana gama fadin haka ta ruga a guje tana share hawaye yabi bayanta amma inaa!..tayi nisa,  cikin hall d'in ta shiga can bangaren family ta nufa ya hangota kusa da Anty Aysha ta kwanta a jikinta tana kuka. Murmushi yayi yana tuna kiss da ya mata Salina ce ta jawo hannunsa sai huci take sukayi waje nan ta fara bala'i
" wace shegiya ce aka ganku tare? Tun yaushe ka fara cin amanata prof, iyye ga fadamin wace yarinya ce ?"
   " ke meyake damun Ki?" "Kai zan tambaya.. Shuraim da aurenka zaka Je ka rungumi wata Mace, ka min adalci kenan" " listen Salina.. " "listen to wat wallh sai naci ubanta ba Afreen ba, xata gane kurenta" ido Shuraim ya xare "me kike nufi?"
  " koma menene wallh sai na illata ta" fuu..ta wuce cikin hall "Salina! Salina!" Amma ko waigowa batayi bah

Ko me xata aikata cikin hall oho🤔🤔

*muje Xuwa*

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...