💦💦 HAJJA HADIZA💦💦
🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥
💦Talented Writers Forum💦
TWF
Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻
kugiya daya tamkar dubu👌🏼
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
Written & story by Qz
💦16-20
Bangaren saleh kuwa koda ya koma gida yafita bai dawo ba sai wajen yamma,wayarsa kuma a gidaya barta saboda yasamu chaji
Koda suka koma cikin gidan haka sukayita kiransa har suka gaji kowa ta wanke fuska duk suncika da haushi
"Toh kawata in kuma shima wajen budurwars yaje fa yakenan?" tafada tare da tsurawa Hadiza ido
"Haba Ghaji dan Allah karki 6atan rai mana,mai makon ki kwantarmin da hankali kuma ke kike kokarin dagamin gaskiya banaso kuma banji dadin hakanba".
tafada tana 6ata rai
"Yi hakuri kinji bazan sake ba amma in akwai taya zamu magance lamarin kikega? amma dan Allah ki kwantar da hankalinki ta abokin yaya Sule" tayi maganar cikin tsigar wasa don sanyaya ran kawar ta ta
"Hmmm Ghaji kenan ai kibari zan iya yin komai indai har akan handsome ne domin kuwa sonshi yayi nisa a zuciyata tayanda bana majinkira, gangar jikina shi suke muradi, ruhina kuma saida shi zai samu nutsuwa, kedai kitayani addua amma ina me tabbatar miki da cewa bazan bar kowata mace ta sameshi ba inhar nima bazan same shiba,yamma nayi tashi in rakaki gida" tafada tare da mikewa tsaye
Ghaji kuwa kallon ta takeyi tana nazarinta "watofa da iya gaskiyarta take magana zata iyayin komai lailaikam dole ta tayata da addua wannan wani irin sone?" ta fadi a ranta tare da mikewa tsaye ta dau gyalenta suka fita waje tayi wa inna saida safe kafin suka dau hanyar fita daga gidan kowa da abunda take tsakawa aranta game da wannan lamarin,nama kamar Ghaji datake hango irin matsalolin da ze auku domin akwai chakwakiya a wannan abu..
Sule kuwa sai wajen laasar ya tafi koda ya koma bai wuce gida ba ya tsaya a majalisa don adama dashi, sai wajen magariba ya shiga cikin gida alokacin shima Sake bai dade da dawowa ba, tare suka jera suka fita sallah a masallacin kofar gidansu..
Koda suka dawo gida Sale bai bi takan wayarsa ba sai bayanda sukayi sallar ishai sukaci abinci sannan ya dau wayar don hawa facebook,yana budewa yaga 30miscal 25 nawata sabuwar number biyu na Sule daya na Aisha sabuwar kawarsa ta social media sauran biyun kuma na wata kanwarsa,bai bi takan sauran ba ya fara kiran sabuwar numbern don miscal din sunyi yawa Allah dai yasa lafiya,koda yakira sau biyu ba'a dauka ba se bai sake kira ba, ya kira kanwarsa sukasha hira sannan yakira kawarsa Aisha itama suka dan labarta kafin ya sake dialing sabuwar numbern nan, kira daya aka dauko sai baiyi magana ba jin muryar mace "hello! hello!!" shine abunda take ta fadi,shidai a iya sauraronta da yayi yakasa gane muryar nata kawai sai ya kashe, yana kashewa takira har kamar bazai dauka ba sai kuma ya dauko "hello kana jina kuwa? "eh ina jinki, wake magana dan Allah kuma daga ina" sautin murmushinta yafara ji kafin tace "Hajja Hadiza ce kanwar budurwar abokinka yaya Sule ta unguwar ....". "okay nagane ya kike yasu maryama? "lafiya kalau ya aiki ai nayi ta kira dazu danaji shuru nace kila kanagun antinmu!" "eh chan naje" yafada a takaice don har ya fara gajiya da surutunta "okay shikenan dama nakira mugaisa ne kayi saving numbern dan Allah" tafada kamar zatayi kuka jin cewa yanada budurwa "toh zanyi ki gaida maryama saida safe" bai jira amsarta ba ya kashe wayarsa gaba daya,yayi wulli da wayar sannan ya kwanta..
Itama a nata 6angaren wulli tayi da wayarta duk sa cewa bata kashe ba tayi kwanciyarta tana mai bakin cikin cewa yanada budurwa kila kog tafita kyau ko kuma ita tafi budurwar kyau, kai bazama tafita ba ai itama kyakyawace komade meye bari zuwa gobe zata je gun Ghaji susan abunyi don kuwa babu mahalukin da ya isa ya mallaki Sale itakuma bata mallaka ba kai karya ne bazai sa6u ba wai chacha a idi
😍DEDICATED TO S.U❤
✨QUEEN ZAHRA✨✍
Comments
Post a Comment