Skip to main content

ZUMUNCI NA SUNHERA

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na_*Sunhera*_

💦 *Talented writers forum*💦

   *T.W.F*

    *dedicated to Reefat yahya*
  

💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝

𷠽𷠮 *7&8*

        _wannan shafin naki ne my swt hrt sadee smart ke tawa ce love u so much kawallimie_❤😘

Zayyad ne kwance bisa rest chair dake cikin dakinsa knocking akayi ya bada Umarni a shigo , bodyguard nasa ne ya risina cikin girmamawa yace " sir! Angama shirya komai " sai da dan share minti 2 sannan yace " OK u guys shul b redy by 2:00pm zamu wuce " " OK sir! Angama" daga nan mutumin ya fice Zayyad kuwa lumshe idanunsa yayi tare da cewa " my beauty Queen I can't wait to c u..I love u so much " murmushi ya cigaba dayi a yayinda fuskar Afreen ke masa gizo yayi nisa cikin tunani wayarsa tayi kara ya duba yaga number din dad nasa ne tsaki ya Ja sannan ya danna silence ya ajiyeta gefe ya cigaba da tunaninsa.

    💞💞💞

Dariya suke harda kyakyatawa Afreen tace " wallh Anty na kagu muyi Hutu I can't wait to c myself rike da iPhone 7" dariya Anty Aysha ta sake yi sannan tace " dakyau 'yar gidana shiyasa nake sonki wllhi gidan baimin dadi idan baki nan, kedai Ki bada kai kawai muci arzikin Hon" tafa hannu sukayi tace " ai Anty bakiga irin shopping da mutumin nan yamin bah da sai kinyi mamaki, ynxu de zan dauko kudaden Ki tafi dasu " " toh Queenie ke baki bukatarsu a nan ne?" " me zan bukata Anty ina da komai a nan, kedai Ki tafi dasu gida yafi" hostel ta nufa wajen matron nasu taje ta karbo ajiyar kud'ad'en  sannan ta koma visiting ground ta tarar da sauran yan uwansu zagaye da Anty Aysha sai hira suke suna dariya dai-dai nan familyn modibbo suka kunno kai motoci 5 ajere suka shigo harabar makarantar nan mutane suka xuba musu ido.

   Anty Zainab ce wato Maman Afreen tazo da kawayenta cikin motoci 3 tare da sojoji masu Mara mata baya sai kuma su Anty Fatima da uncle Suleiman tare da sauran dangin nasu wato iyayen su Afra, nan suka shimfida darduma  suka baje ga abinci kala-kala suna hira da dariya tare da d'aukar selfie abin de gwanin ban sha'awa . haka suka cigaba da hira Afreen na makale da mami sai xuba shagwaba take ga sauran yayunta ma sunzo ana ta jida ita.  Wata black hummer new model mai shegen kyau ne ya kunno kai gaba daya ya d'auke hankulan jama'a bayan yayi parking ne sarina ta fito rike da d'an ta sunyi bala'in yin kyau Kowa sai kallonsu yake, Afiya tace " ikon Allah yau anti sarina ce tazo mana visiting? Kodai ba wajen mu tazo bah?" Afra tace " toh waya sani Amma de abun akwai mamaki kam" safina taja tsaki tace " ni wllhi haushi take ban don ta fiya girman kai"
  " uhm..ita da mijinta Duk halinsu d'aya" zee ce tayi wannan furucin can suka hango prof Shuraim ya fito ya jingina jikin motar🙀🙀 gaba daya yan mata sun rikice da ganin irin kyaun da Allah ya basa, ga iya daukar wanka sai xuba qamshi yake yayi kyau sosai.

   "Lahh..kinga harda ya Shuraim wllhi wajen mu suka zo " Afra ta fada cike da zumudi domin yayan nasu be taba Xuwa ba sai wannan karon. Tare suka karasa indA yake sai wani shan qamshi yake "yaya sannu da Xuwa" a hankali ya amsa cike da qasaita nan suka gaisa indA suka shaida masa suna tare dasu mama donhaka suka karasa indA sauran familyn suke. Ya gaida iyayen nasa cikin girmamawa  sannan ya xauna a gefe sarina kam a takure take tamkar ba danginta ba tsantsar irin girman kan da take nuna musu idan suka Je gidanta , hira sosai suke amma banda Afreen wacce tayi lamo ajikin maminta tana chat a phn din mami  sai murmushi take ayayinda Shuraim yake satar kallonta domin kuwa a dalilinta ne yasa yazo don yana son kallon kyakkyawar fuskar tata amma yayi mamakin ganinta cikin familynsu shiyasa ya fara shakka aransa anya ba y'ar family bace?  Har mamakin kansa yake da irin yanda ya damu da ita.

    4:30 su mami suka fara shirin tafiya bayan sun kwashe kayan da aka kawo musu a boot d'in mota nan Afreen ta fara shagwaba dakyar mami ta lallabata sukayi sallama suka tafi, ya rage Anty Aysha da prof Shuraim da matarsa Sarina . Afra na tsokanar Afreen nan ta fara bubbuga kafa tana tura baki Anty Aysha ce take rarrashinta sannan ta koma jikin antyn nata ta kwanta , Shuraim de sai danna phn yake Amma hankalinsa na kan Afreen yana mamakin shagwabarta da kuma miskilanci irin nata domin ko uffan bata ce masa ba tunda yazo. Suna nan xaune d'an gwamna ya danno tare da tawagarsa gaba daya skul d'in ya cika da kukan saireen nan aka juya ana kallo Afreen kam hira suke kasa-kasa da Anty Aysha sai de kaji dariyarsu, bayan minti 20 da zuwan Zayyad nan bodyguards nasa tare da wasu students biyu suka karasa indA su Afreen suke tare da sallama . daya daga cikin daliban tace " Queenie ana son ganinki" cike da gadara tace " waye?". " ehm..d'an gwamna ne"😳😳😳 gaba daya sunyi mamaki ciki kuwa harda Shuraim Amma ya share ya cigaba da danna wayarsa amma ya gama rikicewa, Afreen ta gyara kwanciya tare da cewa

"Kuce masa yazo nan ya sameni" Afra tayi carab! tace " ke lafiyanki kuwa ? Kinsan waye Zayyad? Shifa baya tolerating nonsense wllhi " tsaki Afreen ta Ja tace " toh sai me? In yaga dama yazo nan if not ni babu indA zani"  shiru sukayi suna kallon ikon Allah daga nan bodyguards d'in suka koma wajen Zayyad don isarda sako.

*shin ya xata qaya ne?*

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na_*Sunhera*_

💦 *Talented writers forum*💦

   *T.W.F*

    *dedicated to Reefat yahya*
  

💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝

𷠽𷠮 *9&10*

    *_Ina kuke Fayeez m Usman (Hanyar yaman) pherteenjay ( Feenert d'iyar sarki ce) wannan shafin nakune hakika kuna nishadantar damu Allah kara basira_*😘😘😘

*Naseeba I Uba( Kannan mijina) n Fayeez usman ( Hanyar yaman) ina tayaku murnar kammala buks d'in Ku Allah kara basira kuna wuta 👍🏻👍🏻 a cigaba da sambad'a mana buks masu madish da curry😜😘❤ ana tare🤝*

*My swt potato Haliemerh Ameen bazan daina  sonki bah my love 4u is pure lyk swan water n natural lyk rain water love u so much*😜😘😘❤

Gyara kwanciya Afreen tayi a jikin Anty Aysha suka cigaba da hirarsu kasa- kasa suna dariya cikin rad'a Anty Aysha tace " shegiya Queenie kina wuta fah" murmushi tayi tare da cewa " lokaci na ne Anty Ki barni nayi kawai , ai wllhi sun shiga hannu kenan mai kwacesu sai Allah " dariya suke harda tafawa dai-dai nan suka jiyo sallama wani murya mai d'adin sauraro Wanda ya ratsa zuciyar Afreen ba shiri ta juya don kallon me wannan muryar , yana tsafe cikin shiga ta kaftan fuskar sa d'auke da murmushi ma'abocin kyaun fuska me ingarman jiki . Afra dasu Anty Aysha ne suka amsa Shuraim kam kishi ne ya turnukesa donhaka ya tashi ya koma cikin mota ya xauna , sarina kuwa zaman ya gundureta domin babu wacce ta kulata Zayyad ya xauna bisa dardumar a yayinda jama'a suka zuba musu ido nan ya fara gaishe da Anty Aysha ta amsa cike da fara'a nan su Afra  zee Afiya da sauran 'yan matan suka gaishesa ya amsa sannan ya maida kallonsa gun Afreen yace " beauty ba magana ne"

   Wani shegen murmushi me sace zuci ta masa sannan tace " ina yini" " no bazan amsa ba tunda sai da na roqa" " eyya sorry naga kuna gaisawa da sauran ne shiyasa " murmushi yayi sannan ya Ja dogon numfashi yace " well is OK! Ya kike ya karatu"
  " Alhamdllh ya gida" " toh nidai bani da gida ynxu maybe nan gaba, ba tare da b'ata lokaci bah sunana Zayyad idan bazaki damu ba ina son ganin Ki in private koda minti 10 ne pls" juya ido tai cikin tsigar Jan hankali tace " ka nemi izini gun my swt Anty "
   dariya sukayi gaba daya a yayinda su Afra suka koma gefe suna yin kus-kus da alama de gulmar Zayyad suke, Anty Aysha tace " na baka dama amma kada ta dade " " godiya nake swt Anty" nan ya tashi tsaye suka jera suna tafiya gwanin birgewa sun dace kwarai da gaske jama'a sai kallonsu suke ana ta gulma wasu ko suna mamaki a yayinda 'yan mata ke kishi.
     Cikin mota suka xauna Afreen tana satar kallonsa gaskiya Zayyad akwai class ya gama burgeta tun ynxu ya juya kenan suka had'a ido murmushi suka sakarwa juna Zayyad yace " Afreen ko?" " ya akayi Kasan sunan?" " ya zama dole nasani shiyasa nayi bincike na gano" murmushi ta sake yi a karo na biyu sannan tace " well lokacin da Anty na ta Baka na tafiya " "OK ..kamar yanda na fad'a sunana Zayyad mahaifina shine gwamnar wannan jaha , gaskiya bazan boye miki ba tun ranar da na fara ganin Ki na kamu da sonki kuma ina da burin auren Ki idan Allah ya kaddara n pls bana son yaudara Ki fad'a min gaskiya idan kina da wani don naji familyn Ku yawanci auren dangi ake muku"
  Numfashi ta sauke sannan tace " nagode Zayyad but a gaskiya ni ban fara soyayya bah don ynxu ina Ss2 kuma sai na gama skul kafin na fara zancen aure a gida so?"
   " so? Kin amince dani kenan " " well..Nide ba ynxu ba sai na gama makaranta " ya marairaice yace " haba beauty yaushe zan jira har Ki gama makaranta , wllhi nima ban taba soyayya ba a kanki zan fara I rily love u Afreen don Allah Ki amince " shiru sukayi sun kurawa juna ido zuciyar Afreen sai bugawa take ta shiga cikin wani baqon yanayi donhaka ta d'auke kanta tana kallon window tace " shikenan zanyi tunani akai"
    " don Allah beauty Ki taimaka min bazan jure rashin Ki ba u r my first love " murmushn jin dadi tayi tare da cewa " OK ni zan tafi "
" tun ynxu? Pls ki dan tsaya ban gaji da kallon beautiful face naki bah" " but Anty na tana jirana kuma kaga tym ya kusa " " olryt nagode da lokacin da kika ban sai next visit insha Allah zan zo , so Ki kula da kanki n I love u " murmushi tayi sannan ta bude motar ta fita , sun sake jerawa suna hira ya rakata  har  wajen zamansu nan yayi sallama da Anty Aysha da sauran yan matan yana d'aga mata hannu ya juya ya tafi.

  Bodyguards ne suka fara jero mata kaya har abin ya fara basu tsoro daga karshe suka mika mata envelope sannan suka tafi, su Afra sun hau shewa sarina kam ta zama y'ar kallo Anty Aysha ta Ja Afreen gefe tace " Ki saurareni da kyau Queenie, kinyi babban kamu wllhi kada kiyi sake ya kubce miki wannan mijin aure ne yasin ya had'u donhaka Ki maida hankali Ki bawa 'yan bakin cki kunya " " trust me Anty zan baki mamaki ni nasan yanda zan tafiyar dashi" " daz my girl shiyasa nake son Ki" dariya sukayi Afra ce ta katsesu ta hanyar cewa " Afreen ya Shuraim na kiran Ki" tsaki ta Ja tare da cewa " uwar me zan masa ynxu zaki jamin raini gun wannan uwar kishi ta fara wani banzan tunani akaina" " haba Queenie ai itama taga zahiri tasan kin fi karfin mijinta " Anty Aysha ce tayi wannan furucin daga nan Afreen ta wuce inda yayi parking motar sa tare da sallama ta bud'e ta shiga.

Ya share minti 2 sannan yace " me tsakanin Ki da wannan Dan iskan?" a dakile ta d'aga ido tana kallonsa sannan tace " me tsakanin ka dani da zaka tasani a gaba ka jefamin irin wannan tambayar?" Cike da mamaki Shuraim ya kura mata ido, murguda baki tayi ta kawar da fuska gefe batayi aune bah taji ya cafke bakin ya matse da karfi taji zafi sosai nan hawaye suka fara gangarowa " ni zaki murgudawa baki? Ni sa'an Ki ne ehh? wato ke fitsararriya koh toh wllhi mun fara kenan " nan ya cika ta tare da Jan tsaki da karfi ta bud'e motar tana hawaye ta jefa masa kallon tsana tace " Allah ya isa mugu kawai azzalumi Allah ze saka min" nan ta ruga a guje ta wuce gun Anty Aysha ta fad'a jikinta tare da fashewa da kuka.
Sarina wacce hankalin ta bai kwanta ba sai xare ido take a yayinda zuciyarta ke dukan uku-uku wani balain kishin Afreen take ji, dakyar Anty Aysha ta rarrasheta sannan ta zayyana musu komai zee tace " kema de da naki iskancin don bakisan halinsa bane shiyasa "
Afra tace " hmm..prof kenan kad'an ma kika gani don baki xauna dashi bane" tsut sukayi don ganin prof na Xuwa kowacce ta Ja bakinta tayi shiru, ya tsaya kusa dasu fuska a murtuke yace " kai kuje booth Ku kwaso kaya ni zan wuce, Anty Aysha sai anjima" can ciki Anty Aysha ta amsa don an tabo y'ar gata sarina ta tashi tabi bayansa ba tare da ta musu sallama bah.

Su Afiya sun kwaso kaya tare da yi masa godiya ko uffan be ce musu bah daga nan ya Ja motar sa yayi gaba, bayan 30 mins Anty Aysha ta musu sallama ta tafi kamar kar su rabu nan suka fara kwashe kayansu Xuwa hostel Duk da cewa su 7 ne amma sai da suka nemi wasu daliban su taimaka musu don kayakin sunyi yawa.
*'yan gata kenan modibbo s family*👍🏻

__muje Xuwa__

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na_*Sunhera*_

💦 *Talented writers forum*💦

   *T.W.F*

    *dedicated to Reefat yahya*
  

💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝

𷠽𷠮 *11&12*

*Dr ummiey zee Abakson my kawalliya romon biri😂😂 but not monkey pox woo..ina son Ki sosai wannan shafin naki ne ke da me🤰🏻🤰🏻🤰🏻 mum Ablah ( islah tee) 1love*😘😘👍🏻❤❤

Bayan visiting Afreen ta fara fuskantar matsaloli daga gun seniors don suna kishin jin cewa Zayyad na neman ta domin wasu daga ciki sunkai Kansu ma ba'a kulasu bah donhaka suka sata a gaba sai tura mata wanki suke da punishments iri-iri don ma de Fauziya da Jamila 2 daga cikin 'yan uwan nasu suna Ss3 ne shiyasa ake d'an raga mata, haka rayuwar ta cigaba da tafiya bayan wata biyu suka fara jarabawar first term a hankali Afreen ta fara soyayya da Zayyad domin yana kiran ta a wayan wani malaminsu kullum sai sunyi waya . haka ta maida hankali gun jarabawarta har suka gama bayan sati daya da kammala jarabawa aka basu hutun sati 3 murna gun dalibai baa cewa komai mami da kanta tazo daukar Afreen domin gidan mahaifinta zasu wuce kafin ta koma gidan Anty Aysha.

💞💞💞💞

Prof Shuraim na xaune a ofishinsa dake *American university of Nigeria yola* yayi nisa cikin tunani kenan wayarsa yahau ruri ..firgigit ya juya kallo d'aya yayi wa wayar ya d'auke kai Salina ce ke kiransa tsaki ya Ja sannan ya d'aga " ina jin Ki" daga can bangaren tace " Baban Khalid ka manta Baka Je ka d'auko Khalid a makaranta bah " tsaki ya Ja sannan yace " sorry wllhi na manta abubuwa sun min yawa meyasa baki Je bah? OK Ki tura driver yaje ynxu pls"
   "OK  miss u " nan ya kashe  wayar, numfashi ya sauke yana lumshe ido fuskar Afreen kawai yake son gani amma yana da aiki a gaba domin baisan ta ina ze fara furta mata Kalmar so bah. shiru yayi ya fara nazarin hanyar da zai bi don ganin ya cimma burinsa don gaskiya ya fad'a tarkon sonta ba kad'an bah.

*Mohammad Shuraim* kenan gidan Alhaji Usman modibbo Tukur mahaifinsa da mamin Afreen uwa d'aya uba day'a suke , shine 'dan fari a gun Alhj Usman Wanda ya kasance hamshakin d'an siyasa kuma dan kasuwa. Matarsa d'aya hajiya Hafsat yaran su biyar Shuraim ne babba sai sadiq, Fatima, Afiya da Afra suna nan xaune cikin modibbo estate. Shuraim ya gama karatunsa na degree da masters a fannin Chemistry sannan yayi PhD d'in sa a kasar Germany bayan ya dawo ne aka aura masa Salina wacce ta kasance Jika ga kanin modibbo , suna nan cikin family estate d'in modibbo Duk da cewa Shuraim baya so amma dole ya amince akayi auren suna zaman lfy sun haifi d'an su d'aya me suna Khalid. Salina irin matan nan ne masu kishin tsiya tana balain son mijinta kuma tana da girman kai hatta yan uwanta bata kulasu sake!ta dauko halin uwarta hajiya Batulu wannan kenan.

Kwana biyu Afreen tayi a gidan mahaifinta daga nan ta wuce gidan Anty Aysha.
*wacece Anty Aysha*?? 'Ya ce a gun yayar mami ta wajen Uba wato y'ar anty Safiya ( y'ar wajen Nenne) sannan mijinta Saleem 'da ne a gun Alhj Abdulrahman (d'an Diddi ..a duba page 5&6 don gane nasabarsu) wato dai auren dangin ne su 'yan uwan juna ne, shekara biyar da aurensu amma Allah bai basu haihuwa bah shiyasa Afreen ta dawo gidan da zama tana debewa Anty Aysha kewa.
    A falo ta iske antyn nata xaune ta kurawa TV ido da alama film d'in ya d'auke hankalin ta " salamu alaikum my swt anty" Afreen tai sallama cike da farin cki suka rungume juna , anty Aysha tace " Queenie na ta dawo wayyo dad'i " murmushi suka sakarwa juna nan suka zube Kasan kafet " ina yaya Saleem yau weekend ina yaje?"
"Uhmm kinsan inda zaije ai, kin manta kowane weekend suna gun baba tsoho ( modibbo Tukur) " " au..ashe hakane wllhi na sha'afa" " ya gida ya Mami ?" " lfy kalau tace a gaida Ki"
   "Nagode ya labarin mutanen Ki?" Afreen ta gyara zama tace " yawwa anty wllhi ina ganin kamar Zayyad zan aura don gayen ya iya soyayya " dariya Anty Aysha tayi tare da cewa " keda kike Ss2 har kin fara zancen aure? Kinsan Abba ai Nide ba ruwana kar a ce ni na zuga Ki"   " dallah manta dasu ni Ki ban shawara Zayyad ko Hon Ahmad? "
  " uhmm..ko Dr Shuraim bah" xare ido Afreen tai tace " wannan mugun me zanyi dashi?" " toh albishir! Jiya yazo gidan nan wai yana Neman dear Nah kuma be taba Xuwa bah, ni nasan ke yake son gani"

"Kai Anty ai baice yana son ganina bah" "amma ai ya tambayi inda kike, kuma idan ba sonki yake ba meyasa ya nuna damuwarsa lokacin da Zayyad yaje wajen Ki?" Shiru Afreen tai sannan tace " uhmm can ta matse masa ni ina ruwana" dariya Anty Aysha take sannan tace " uhmm akwai aiki a gaba"
"Anty Ki bar wannan zancen ina waya na ?" "Yana cikin wardrobe"  , d'aki Afreen ta wuce ta dakko phn nata cikin kankanin lokaci ta kunna Zayyad ne ya fado mata a rai take tayi dialing numbar sa sannan ta haye gado ta kwanta .

  Bugu biyu yayi picking " hello swt hrt Afreen ce" daga can bangaren yace " wow my beauty nayi kewarki sosai wllhi, naji kun samu hutu but na jira call naki shiru"
       " ehh..wllhi naje gidan iyayena ne ynxu kuma ina gidan swt anty" " OK yaushe zamu had'u cos I missd u" " OK me zai hana kazo anjima da yamma " " wow gaskiya naji dadin Ki saurareni"
"OK tnx ka kular min da kanka " " u too ( ke ma ) " tare suka ajiye wayar Afreen ta gyara kwanciya tana faman murmusawa ita kadai .

*muje Xuwa*

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...