Skip to main content

ZAFIN KISHI BY HUSNA_MB

'"ZAFIN KISHI'"

@WRITED BY@*
@husnah mb@*

@EDITED BY@*
@TEEMAH JALO@*

21.

Yau Alhamis anyi walima wa'azi akayi sosai na shiga jiki malam yayiwa amarya nasiha sosai me shiga jiki dan koni kaina sanda jikina yayi sanyi yadda naji malam na zazzagowa Amarya nasiha😃 lol.
A yau friday aka daura auren manal da Aliyu

misalin karfe 1:30 bayan an idar da sallan jumma'a. Mutane ne a tsaitsaye masu fada aji a gwamnati yan kasuwa sannan da manya masu kudi,  Aliyu dai yau baki yaki rufuwa wani farin ciki yakeji cikin ransa wadda zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai tabajin irin wannan bah, bayan ya fito daga masqllaci ne ya dauki waya yayiwa manal text akan an daura aure.
Manal na zaune a dakinta itada su zahra najma da sauran friend's dinta karan wayanta da taji ne yasa tace zahra ta miko mata bude text din tayi ta karanta bugun zuciyarta taji ta karu, wani haushin Aliyu taji ta faraji wanda tunda take bata tabaji ya bata haushi irin na yauba zahra ne take tambayarta akan meya faru saboda taga alama kaman wani abu ya bata mata rai abunka da aminiya duk yanayin da kake ciki indai ta kwarai ce tana ganewa itadai manal shuru tayi batace mata komai bah tana rike da waya a hannunta karban wayan xahra tayi don taga meye batawa manal rai karanta text din da Aliyu yayiwa manal zahra tayi ta kwashe da dariya hadda gudu tace Amarya a gidan Aliyu Allah ya bata zaman lafiya nan su najma suka karba kowa da abunda yake fadi........

Shirin reception su Aliyu sukayi Auwal kuwa sai raba get pass yakeyi na dinner da za,ayi gobe 9 O'clock
Haka aka gama reception dinnan Aliyu ko ruwa ya kasa sha saboda tsabar farinciki.......
Yau ya kama wuni hidima akayi sosai gidansu manal cike yake da taron jama'a 4 o'clock aka fara shirin kai Amarya Manal na xaune a kusada momy sai rusa kuka takeyi kaman wanda ake cire mata rai hakuri momy take bata amma ita kanta hankalinta a tashe yake rarrashinta momy tayi sosai sanda taga ta tsagaita kukan natan sannan tace ta tashi taje ta shirya kar,azo ata jiranta....

Cikin wani hadaddiyar Atamfa me colour red nd white mommy ta bawa manal ta shirya ta dauko wani kato gele ta mika mata yafawa manal tayi tayi kyau sosai kaman wata Sarauniyah..
Mommy da kanta ta kama hannun manal suka tafi falon daddy inda acan xa,a mata fadah ba karamin nasiha daddy ya mata bah da jan hankali akan xaman aure sannan ta kasance me biyayya da hakuri akan xaman aure don hakuri da biyayya shine gishirin rayuwar aure sannan ta kasance me sauke hakkin da Allah ya daura mata na mijinta bakaramin shiga jikinta fadan da dady ya mata ba nan ta rungume momy tana ihu wani hawaye momy taji yana kokarin kubuce mata da kyar akasaka manal a mota saboda tsabar kuka da riko momy da takeyi su kuwa su zahra sun dade a gidan Amarya.... Niko nace Allah bada zaman lafiya yasa ki iya hakuri da zama da khadija.

To jama'a ko wata irin zama za,ayi tsakanin Khadija da Manal a matsayin kishiyoyi ku biyoni dan ganin yaya zata kaya😉

A mota ma dai manal bata hakura da kuka ba hafsa kanwar mamanta sai bata hakuri sukeyi kaman wanda kara zugata ma sukeyi dan babu abunda ya sauya......

Muje zuwa............

*** whatsapp no***
08109990994
[9/29, 9:00 PM] Ma Asaa4😘: 3/8/2017

9:40am

'" ZAFIN KISHI'"

@WRITED BY@*
@husnah mb@*

@EDITED BY@*
@TEEMAH JALO@*

22.

gidansu Aliyu aka kai manal zata kwana 1 sai gobe asabar a kaita gidanta su zahra da najma da sauran friend's nata na skull sune wanda zasu taya amarya kwana Sai bayan an dan watse ne manal ta samu ta sake a cikin frnd's dinta inda su zahra suke tsokananta Alah yasa nanda 9 mouth su dawo suna najma ne tace ai ba abu me wahala bane kuma gashi kunga yanzu hakama period takeyi kinga ai da ta gama sai a abun nan....... 😂😜 kwashewa da dariya sukayi suka tafa ita dai shiru kawai ta musu dan batada abun fada(nidai cewa nayi to Aliyu me rawar kafa ai sai kwalamarka ta koma.. lol)kusan kwana sukayi suna tadi....
Misalin 10 o'clock na safe Hafsa kanwar momy ce tazo ta dauki manal ta kaita gun mamie inda ta dankawa mamie Amanar Manal Nasiha mamie tayiwa manal sosai sannan tayi musu addu'a sosai akan Allah basu zaman lafiya da zuri,a dayyibah....

****                    ****
Ta bangaren khadija kuma tana nan anata ribibin biki da ita yadda kasan batada wata damuwa dan ko inka kalleta inba kasani bama baxaka ce ita za,a kawowa kishiyar bah uhmmm nidai cewa nayi na ciki na ciki duk yadda akayi akawai abunda khadija take shiryawa...

Ku biyoni danjin yaya zata kaya.....

******      *******
Daki ta shiga ta zauna wayanta da tayi flugging a chatger ta dauko number hajiyarta tayi dialing sun shafe yakai 2 hour suna magana da hajiya wanda nidai banji me suka ce ba amma nasan tabbas koma meyene akan Aliyu ake maganan wayar ta mayar bayan ta gama sannan ta koma aka cigaba da hidima da ita.......
Misalin karfe 7:00am kowa ya watse nan akabar daga Amarya sai kawayenta 2 zahra da Najma su zasu rakata gidanta,

Auwal ne yazo ya dauki Amarya da kawayenta gidanta da yake g.r.a aka kaita kiran sallah akayo zahra da najma suka tashi sukaje suka dauro alwala suka fito bayan sun idar da sqllah najma ne ta fada bathroom ta hadawa manal ruwan wanka wanda yaji hadin turaruka najma ne tace to Amarya na hada miki ruwa fa ya kamata ki tashi kije kiyi wanka tashi tayi ta fada bathroom xahra tanajin alaman manal ta fara wanka tayi sauri taja hannun najma tace tashi mu tafi middin ta fito ta iskemu wlh kinsan da kuka zamu rabu suna maganan ne a hankali yadda baxata jisu bah fita sukayi a hankali da yake akwai wanda Aliyu ya ajiye akan insun gama abunda zasuyi ya maidasu gida......
Aliyu ne zaune a dakin Auwal yana kallo Shigowa Auwal yayi yana haba ango tun dazu ankaima amarya kazo nan zaune kana kallo na tabbata by now ai su zahra sun tafi ya kamata ka shirya muje mu rakaka sayan bakin Amarya dariya Aliyu yayi sannan yace ku rakani ina ka ganni nan ni kadaina xan tafi xanje na sayi bakin Amaryata ni kadai dariya auwal yakeyi har yana kokarin faduwa kasah yatsina fuska Aliyu yayi sannan ya juyo yace saida safe tsayawa gurin me saida kaza yayi ya sai kulli 2 ya jefa a gaban mota ya wuce, horn yayi sannan gate man din gidan ya fito ya bude masa parking space yaje yayi parking din mota...

''Manal kuwa bayan fitowarta a wanka gani tayi bataga su zahra ba jin gidan shiru ya tabbatar mata tafiya sukayi wani hawaye taji yana kokarin kubuce mata akwatin da aka taho mata dashi ta bude sleeping dress ta dauko wadda bata wuce iya guiwa ba ta saka bakin mirrow taje ta shafa mai da fowder kadai sannan ta fada kan gado...
"Bayan yayi parking mota dakin khadija ya shiga saidai abunda ya bashi mamaki ganinta normal babu alamar damuwa a tattare da ita ledan naman ya mika mata guda 1 sannan ya mata saida safe y wuce abunsa...

Muje zuwa.........😉

*** whatsapp no***
08109990994
[9/29, 9:01 PM] Ma Asaa4😘: 6/7/2017
   

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...