💦💦 HAJJA HADIZA💦💦
🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥
💦Talented Writers Forum💦
TWF
Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻
kugiya daya tamkar dubu👌🏼
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
Written & story by Qz
💦6-10
Sauri ta dingayi kamar zata tashi sama, kai karshe dai sai da ta hada da gudu saboda gaskiya ta matsu ta isa gida tayi tozali da abun kaunarta handsome sunan da ta laqa mishi kenan a zuciyarta,koda ta isa gida kai tsaye karamin falon dake zaure ta nufa ko sallama babu tayi shigewarta ciki tana ta dube-dube amma bashi babu alamarsa, maryama ne tace "keh! lafiya zaki shigo bako sallama sai wani zare ido kikeyi kamar kina neman 6arawo"tafada tana hararar ta "yi hakuri" shine kawai abunda Hajja tafada sannan tayi ficewarta zuwa daki tana guna guni "shikenan mutun baya laifine haka kawai zaki min masifa agaban saurayinki wallahi bazata sa6uba ina kyaleki ne don kawai kin girme ni amma wataran zan baki mamaki". tafada tana tamke fuska kamar agabansu, chan kuma kome ta tuna dasauri ta fita tanufi dakin innarsu,da sallama ta shiga "inna nasamu Uma tana aiki amma zata aiko Laure dashi anjima kadan ". batare da uma ta daga kai ta kalle ta ba tace "shikenan jeki ai dama baban nakuma sai bayan isha yake dawowa badamuwa". har zata sake magana sai kuma tafasa ta fita saboda yanayin dataga innar tasu kamar ranta a 6ace yake,sake komawa falon zauren tayi taleka amma duk da haka bayanan, tsaki taja ta koma daki tayi sallah sannan tayi kwanciyarta don gaskiya ko abinci bazata iya ci ba ayanayin datake ciki..
6angaren saleh kuwa yama manta da yata6a ganin wata halitta me kama da ita, sabgar gabansa kawai yakeyi, sai wajen tara darabi yadawo gida har lokacin Sule bai dawo ba, wayarsa ya kunna yafara kallo,karfe goma ya kashe komi yabi lafiyar gado.
Sule kuwa sai sha daya saura yadawo don sai da yabiya gidan yayarsa yaci abinci tukunna don kunyar cin abinci a gidansu maryama yakeyi..
washe gari da safe tun karfe biyar saura tatashi a barci duk da cewa batasamu barcin kirki ba saboda tunanin handsome duk sanda ta rufe ido shitake gani sai wajen daya da rabi barci 6arawo ya dauketa..
tana tashi tagama aikinta da wuri kowa ma mamaki yake a gidan don kuma babu wanda ya kaita son jiki amma yau harta gama aiki batare da inna tayi dogon baki ba lailai akwai magana. bata kula kowa ba har ta kammala tayi wanka ta faki idon maryama ta dau wayarta ta nemi numbern Sule ta kwashe sannan ta ajiye mata wayan ta wuce gidansu Hajja Ghaji kawarta na kut da kut,takoyi saa ta taras da ita tana shirin fita itama "yadai mutumiyar da sassafe haka lafiya dai koh" Hajja Ghaji ta tambaya cike da mamakin ganin kawarta da sanyin safiya.. "ke dai bari zauna muyi maganar". tafada tana janyo kujeran karfe,bayan sun zauna Hajja Hadiza ta zayyana mata komai daga farko har karshe.
mamaki ne yaka ma Ghaji wacce tunda suke bata ta6ajin Hajja Hadiza ta yi mata magana akan wani saurayin da ta damu dashi take sonsa dagaske ba sai dai tayi ta zagin samarin tana cewa su Banki1 Banki2 Gara3 Gara4 Direba5 Direba 6 amma badai tace tana sonsu ba harma tadamu da lafiyarsu da rashinsa,ajiyar zuciya tayi sannan tace "toh kawata ta ina zamu fara kenan yanzu don ni kaina ya kulle da wannan abun alajabin?" fuzgar da iska tayi kafin tace "eh toh na dauko numbern saurayin adda maryama kinga sai mu kira muyi masa bayani koya kikace?" "eh toh banki ta taki ba gwada kira toh mujj inya shiga sai kiban nayi masa magana inbai yiba kuma sai mudau plan B" murmushin jindadi tayi sannan tayi saurin dialing numbern ai kuwa akayu rashin saa wayar akashe take "kash kinji wai switchoff" "sake kira dai may be network ne kinsan network yanzu bai fiya kyau ba inya shiga toh inbai shiga ba inaga dagasken ne akashe take" sake kira Hajja Hadiza tayi amma still akashe, wurgi tayi da wayar taja tsaki,Hajja Ghaji ce ta dauko wayar ta hadu tamika mata sannan tace "inaga ki dan bari zuwa jibi tunda yaudai bazuwa zaiyi ba saidai jibi inkinga basu zo tareba inyaso sai mu dau plan B din,ki daure jibi kamar yau ne komai zai yi nomal muje kirakani gidan anty iyatu chan gangare" ba musu ta mike kamar wanda kwai yafashe a ciki tabi bayanta suka tari mai adaidaita suka kama hanyar gidan yayar Ghaji
😍DEDICATED TO S.U❤
✨QUEEN ZAHRA✨✍
Comments
Post a Comment