💦💦 HAJJA HADIZA💦💦
🔥🔥🔥🔥🔥
A true life story with ultimate fire roaming in circles
🔥🔥🔥🔥🔥
💦Talented Writers Forum💦
TWF
Hadin kanmu abun alfaharin mu🤝🏻
kugiya daya tamkar dubu👌🏼
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
Written & story by Qz
💦11-15
ahaka tayi kwana biyun nan adaddafe kamar wata wacce tayi shekara ba lafiya har ta zube ta zama so silent kamar ba ita ba kullun sai tunani shi ne ya zame mata aikin yi.
Yau ya kama jumma kuma aranar sukayi zasu hadu da kawarta suyiwa saurayin yayartasu magana akan ya taimaka da lambar wayar abokinsa,tun safe take ta fara'a kamar anyi mata albishir da gidan aljanna,tana gama aiki saiga Hajja Ghaji ta iso cikin afterdress tayi roiling gyalenta sai zuba kamshi takeyi,ita kuma Hajja Hadiza ba abunda takeyi sai kallonta sai kace zasu biki amma dai tayi kyau sosai abunta "kai kawata irin wanna kwalliya ai sai ki kwacen saurayi". tafada cikin tsigar zolaya,hannunta ta kama suka shige daki "kinga yanzu ko nagama ayyuka na, yanzu dai bari inje inyi wanka domin ankusa fara sallar jumma kuma ana idarwa yake zuwa". tana magana tana daura towel "shikenan ban littafi in karanta kafin kifito" mik'a mata littafin tayi sannan tayi ficewarta zuwa bandaki.
"Nikam wallahi zan wuce in barka, haba kullun in zakaje gun budurwa sai ka 6ata lokaci gunyin gayu, yau dai gaskiya bazan raka kaba iyakata masallaci zan dawo intafi ziyara gidan yan uwa da abokan arziki". inji Saleh wanda ke cika yana batsewa shi a lailai Sule ya 6ata masa rai sosai sosai..
Fitowa yayi yana gyara hullarsa ya zuba turare sai kanshi ke tashi kamar shagon humra kilama wanka yayi da ruwan turare waya sani ne "yi hakuri aboki afwan bazan sake ba muje koh". ya fada yana rufe kofa sannan ya dau sallayarsu suka wuce masallaci "ai kai kullun haka kake cewa yanzu duk inda mukabi sai an kallo mu saboda irin wannan uban wankan turaren da kayi ai dai ko mace sai haka,ni kamar ma hadda hoda kashafa koh?" shidai Sule bai tanka masa ba har suka isa masallaci yanata banbami karshe dai yayi shuru don kansa..
Hajja hadiza kuwa anyi wanka anyi kwalliya kamar wata amarya duk don zuwan abokin saurayin yayarta da bai san da zamanta ba,nata turarenkam haryafi na Sule kamar ta kwana cikin ruwan turare "kawata naji kamar har an idar da sallah koh". ta tambayi Ghaji wacce ke faman katanta littafi me suna DARASIN RAYUWA "eh tooh inaga dan niba sauraron sallar nikeba amma mai yiyuwa sun idar ai tunda kinji shuru kam". tafada tama cigaba da karanta littafinta.
adda maryama ce ta shiga itadai abun nasu na bata mamaki "kodai biki zasu kokuma bako zasuyi oho Allah masani" tafada acikin ranta kafin ta dau sallaya tayi sallah ta kimtsa kanta domin tarban masoyinta..
A 6angaren Sule kuwa yayi duk yanda zaiyi Sale yarakoshi yace sam shifa zumunci zai yi yau,akwai guraran da ya kwana biyu bai ziyarce su ba,ba yanda zaiyi haka sukayi sallama kowa ya dau hanyarsa.
bai tsaya ko inaba sai kofar gidansu maryama,yana sauka a napep ya buga wayarta domin sanar mata isowarsa,su kuwa yan nema duk sun zuba kunne domin sauraron zuwan bakon nasu,koda sukaga tadau waya tanacewa "sannu da zuwa ganinan fitowa" duk sai suka cika da farinciki harma suka rigata fita, koda isarsu suka tarar da Sule shikadai gaisheshi sukayi atare kafin Hajja Hadiza tace "Mijin addarmu yau bakazo da dan rakiya bane?"
murmushi yayi ganin cewa yau bata yimar shekiyancin data sababa kafin yace "eh toh da dai tare zamuzo amma kasancewar yanada wani uzuri shiyasa bamu taho tare ba, amma bayanda banyi dashi ba yaki zuwa". kallon juna sukayi kafin hajja Ghaji tace "toh yayanmu zamu iya samun numbansa mu sai mukirashi kila asamu yazo!"
duk da cewa Sule bai kawo komai aransa ba amma kuma yayi mamakin damuwarsu kan Sale sai dai kuma kawai ya basu numbern yakuma yi watsi da zancen nasu..
Maryama dake bakin kofa takejin duk abunda sukayi taja dan karamin tsaki"dama wai akan wanda bai sanda zaman subane sukayi wanka haka lailai sun ja wakansu aiki". ta fada aranta, "nikam inkungama sai ku min izini inshigo da masoyina koh?" tafada tana musu wani irin kallo wanda yasa ba shiri suka koma cikin gida "yi hakuri habibi,wadannan yaran ba hankaline dasu ba any way mushiga ciki koh".
tafada tana yimishi murmushinta me kya'yatarwa
😍DEDICATED TO S.U❤
✨QUEEN ZAHRA✨✍
Comments
Post a Comment