Skip to main content

ZAFIN KISHI BY HUSNA_MB

[9/29, 9:18 PM] Ma Asaa4😘: *19/9/2017*

     *3:00pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*61*

*Sakon gaisuwa a gareku_ _my kawalle,_ sadiya mu'azu & baddo na. Na  sadaukar dag page dinnan a gareku Allah  yabar zumunci Ameen*

Upstairs suka haura tare hannunsa yana cikin nata wanka yayi manal ne ta fito masa da kayan dazai saka, yana fitowa ya dauka yasa turare ta dauko ta fesa masa manal ne tace habibi muje muci abinci tun dazu faty ta gama toh yace ya fita ta bishi a baya harsun isa bakin stairs yacewa manal barinje dakin khadija na dubata to manal tace barin jiraka anan to yace tare da nufa kofan dakin khadija handle din kofan ya murda sai kuma yaji a rufe bubbugawa ya hauyi sai kuma yaji shiru kaman babu alaman mutum a dakin, kusa da manal ya dawo yana tambayanta ina khadija taje wlh nima bansani ba manal ta fada tana kallon cikin idonsa shiru yayi baice komai ba kina nufin tun dazu bata gidan nan eh to gsky inaga bata nan dan dazu nazo zan kirata muci abinci naji shiru amma kuma banga time din data fita ba Allah ya sauwaka Aliyu ya fada tare da riki hannun manal su sauko dowstairs.
Aiko abban khadija na dawowa hajiya ta fadamai khadija fa ta dawo gida wai Aliyu ne yace ta dawo shiru yayi baice komai ba sannan yace ta kiramai khadijah
Kwance ta tarar da ita saman gado tana charting kixo abbanki yana nemanki a falo toh tace tare da tashi ta dauki dankwalinta ta daura hijab ta dauka tasaka a falo ta tadda abbanta gaisheshi tayi kanta a sunkuye.

  ''Shiru abban khadija yayi yana kallonta gyaran murya yayi sannan yace khadija na,am ta amsa dashi kanta na kasa
meya hadaki da mijinki dahar yace miki ki dawo gida shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta sannan tace wlh abba babu abunda ya hadani dashi lafiya qlau muke xaune dashi kawai ya shigo ya samen ina zaune a falo yace na tattara kayana na dawo gida shiru abba yayi yana kallonta sannan yace kin tabbata babu abunda ya hadaku daga kai tayi alaman eh Allah ya sauwaka yace tashi ki tafi abunki xan nemeshi shima naji ta bakinshi tashi tayi ta shiga daki.
*Washe gari*

Yaune daddyn bashir yaje gidansu fatee domin sa ranan auren yayan nasun an saka ranan auren bashir da fatee nan da wata 2 yayi daidai dana zahra da sati 2 kenam.

  "'Aliyu ne ya fito daga dakinshi direct kofan dakin khadija ya nufa murda handle din kofan yayi sai kuma yaji still a rufe tsayawa yayi yana kallon kofan a ranshi yana cewa to nikam ina yarinyar nan taje ne yasan dai in anguwa taje yaci ace ta dawo tun jiya koda daddare ma amma har yanxu shiru tsaki yaja yabar kofan dakin downstairs ya sauko wayanshi ya dauko yayi mata text, aiko baifi 2mints ba saiga reply dinta lalle ma yarinyar nan wato ita a dole yaji tayi koh xata gane batada wayo danko babu inda kafana xata taka ya fada yana girgiza kai,
"dago kai yayi sai sukayi ido biyu da manal murmushi tayi tana takowa inda yake a hankali tafiya takeyi cikin kasaita kama hannunta yayi suka xauna akan kujera habibi manal ta kira sunansa na'am yace yana kallon cikin idonta
  ''Nikam har yanxu khadija bata dawo bane murmushin karfin hali yayi sannan yace wai ta tafi gidansu ne subhanallahi manal ta fada tana gwalo ido😳
To ai habibi sai kaje kaji meyasa ta koma gidan shiru yayi sannan yace barta inta gaji ai zata dawo harta bude baki xatayi magana saiya daga mata hannun alama tayi shiru

*After 3days*
Yau kwanan manal hudu kenam a gida Aliyu baije ba Abba yayi niyyan nemanshi sai kuma yace bari ya barshi yasan dole xaixo.
   Abba ne zaune a falo shida hajiya khadija tana daki tana charting dan Yanxu tunda ta dawo batada aikinyi sai chart.

"' hajiya ne tace nifa wlh Alhj yaron nan yabani mamaki ace matarshi bata gida ko biko baizo bah Yaufa kwanan khadija hudu a gidan nan amma bana tsammanin koda a waya ya nemeta shiru yayi sannan yace nifa nafi kyautata zaton akwai abunda yarinyar nan tayiwa Aliyu danko Aliyu yarone me hakuri haka kawai bazaice mata ta dawo gida ba tareda wani abu yashiga tsakaninsu amma barin kirashi yanxu incemai ina nemanshi nasan zaizo kinga sai muji meya hadasu koh ya fada tare da zaro wayanshi a aljihu number Aliyu yahau dialing ringing 1 ya daga
Abba yace" hello Aliyu

Aliyu ne yace na'am ina wuni Abba
''Lfy Qlau' yacen gidan nakan

Aliyu yace" duk lafiyansu qlau

Abba ne yace dama inason ganinka ne shiru Aliyu yayi sannan yace to Insha Allahu zanzo

Abba" ne yace to Allah ya kawoka Ameen Aliyu yace suka katse layin.
 

Muje zuwa

WhatsApp no
0810990994
[9/29, 9:18 PM] Ma Asaa4😘: *24/9/2017*
*6:00pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*62*

_Wannan page din na sadaukar dashi ne a gareki Allah ya kareki duk inda kike Ameen_ *pherteenjeey*
 
_Na gode sosai da kulawarki a gareni Allah yabar zumunci ya kuma kara basira_ Ameen.

5 o'clock Aliyu ya tashi taga office, gidansu khadija ya nufa direct.

  ''A falo ya tarar da Abba da hajiya suna zaune tsugunawa yayi ya gaishesu abba ne ya amsa da fara'arsa hajiya kuwa murtuke fuska tayi tana harararsa.

Abba ne ya umurci hajiya da taje ta kiramai khadija tashi tayi ta nufi daki zaune ta sameta tana waya da dukkan alamu da kawarta take waya hajiya ne tace kizo abbanki yana nemanki katse wayan tayi tare da daukan hijab ta saka falo ta fito kanta a sunkuye kaman mutumiyar arziki

A kasa ta zauna bata lura ma da suwaye a falon bah dago kai tayi gani Aliyu da tayi a xaune gabanta taji ya fadi sai kuma ta matse tayi kaman batama ganshi ba
  ''Abba ne ya fara tambayan Aliyu meya hadaka da matarka da kace mata ta dawo gida shiru Aliyu yayi a ranshi yana cewa lalle wuyan khadija yayi kwari watoma yarinyar nan sharri tazo tayi masa agun iyayenta shirun da abba yaga yayi ne yasa yace Aliyu tambayanka fa nakeyi dago kai yayi suka hada ido da Abba

Sunkuyar da kai ya karayi sannan yace Abba babu abunda ya hadani da khadija nidai kawai na dawo daga office na samu bata nan nayi zaton ma kota geta anguwa ne sai kuma har washe gari bata dawo ba nayi mata text sai tacemin ai tana gida ni kuma banyi xaton wani abu bane shiyasa ma banzoni bah shiru abba yayi yana kallonsu duk kansu ranshi a bace yacewa khadija kinji abunda yace shiru tayi ta kasa cewa komai tunda abba yaga khadija tayi shiru yasan itace batada gaskiya.

  Fada yayi musu sosai mai shiga jiki musanman ma khadija dan yafi yimata fada sosai dan yadda ya fahimci abun itace batada gaskiya sannan ya umarci Aliyu daya dauki matarsa sutafi gida.
dago kai tayi suka hada ido da Aliyu galla mata harra yayi ta dauke kanta da sauri tashi tayi ta shiga daki hajiya ne ta tashi ta bita a baya sai kumbure kumbure takeyi akwatinta ta dauko kayan data saka ta dauka ta jera aciki rafan dubu dubu guda 2 ta dauka ta baya hajiya aiko nan hajiya ta fara murmushi dan duk xaman da tayi da khadija na kwana 4 batayi tsammanin tana ajiye da kudi masu yawa kaman haka ba karban kudin tayi tare da saka mata albarka da addu'oi
Akwatinta ta dauka tayiwa abba sallama a mota ta tarda aliyu yana zaune fuskansa a murtuke kaman bai taba dariya ba.
gaban motan ta bude ta shiga ko kallonta baiyi ba ya fizgi motan da karfi babu wanda yayiwa wani magana acikinsu har suka isa gida a parking space yayi parking motan budewa tayi ta fita a falo ta tarda faty da manal suna zaune ko

gaban motan ta bude ta shiga ko kallonta baiyi ba ya fizgi motan da karfi babu wanda yayiwa wani magana acikinsu har suka isa gida a parking space yayi parking motan budewa tayi ta fita a falo ta tarda faty da manal suna zaune ko kallan inda suke batayi ba ta haura upstairs faty ne ta kalli manal suka kwashe da dariya Aliyu ne ya shigo tambayansu ya hauyi su kuma dariyan meye sukeyi babu suka fada a tare upstairs ya haura dakinshi ya nufa direct faty ne tacewa manal maza tashi kibi mijinki dan da duk kan alamu yadda na ganshi yau ranshi a bace ne tashi tayi tare da dariya dakin Aliyu ta shiga zaune ta tardashi kan gado ya zabga uban tagumi ganin manal da yayi ne yasa yake kokarin daidaita fuskanshi ya kalkalo murmushi karya yayi amma dakaga yadda yayi murmushi kasan baije zuci bah kusa dashi taje ta zauna tana tambayansa meya sameshi babu yace batason takura masa kawai saita barshi bata sake tambayanshi bah salon data saba amfani dashi tayi domin ta kwantarwa mijin natan hankali aiko nan da nan ya manta da bacin ran da yake ciki suka lula duniyar masoya....

_Washe gari_
Khadija ce ta fito fuskanta dauke da fara'a yadda kikasan ba ita ba manal dai har mamaki takeyi yadda taga yau daya khadija ta canza tayasu girki tayi tare sukayi girkin safe da manal na rana ma haka,

Ta bangaren faty kuma sai preparing tarban bashir takeyi kaman kullum wanka tayi ta saka kaya masu kyau amma ko kadan batayi wani kwalliya mai yawa a fuskanta ba bayan sun gama lunch abinci data dafa masa taje ta jerasu a dakin karban baki...

Muje zuwa....

WhatsApp no
08109990994
[9/29, 9:18 PM] Ma Asaa4😘: *27/9/2017*

     *6:00pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*63*

*Masoyan zafin kishi ina mai baku hakuri na rashin jina da bakuyi ba kwana biyu wlh wani dan uzurina ya hanani typing na gode sosai da support Allah bar zumunci, Ameen*
Bayan ta gama jerawa dakin manal ta koma ta zauna a falo tana kallo baahir ya kirata ya shaida mata ya iso, tana zumudi ta dauki gele ta yafa ta nufi wurinshi yana tsaye jikin motanshi looking more handsome, murmushi ta sakar masa sannan ta kaishi dakin saukan baki yaci abincin sama sama dai dan baici da yawa ba bayan ya gama cin abinci ya kalleta fuskanshi dauke da murmushi hira sukasha sosai around 9
Ta Rakashi har bakin mota ya shiga sannan ta koma cikin gida fuskanta dauke da murmushi.

A falo ta tarar da khadija da manal sai hira sukeyi harda dariya abun yayi matukar bata mamaki sosai a ranta take tunani anya kuwa khadija batada wata muguwar manufa akan manal tundaga dawowarta taga ta canza ta maida manal tamkar wata kawarta ita dai bata kulasu ba upstaits ta haura dakin manal ta barsu zaune a wajen

"Zama tayi a falo tana kallo around 9:30 manal ta shigo zama tayi kusada faty tana tambayanta yaya surkin nasu kelkyalewa da dariya faty tayi sannan tace qlau yake kaman yadda kike murmushi manal tayi tare da cewa to marar kunya
  Faty ne tace maman baby dama inason muyi wata magana dake murmushi manal tayi sannan tace meye kike sauri kema kwana nawane faty ne tace dama yadda naga yanda kukeyi da khadija ne abun yana matukar bani mamaki gsky sosai naga yadda take shiga jikinki kaman ba ita ba bakya tunani wani abu ta shirya miki kinsan fa ance duk wanda ya kika da farko koda daga baya yazo yace yana sonka tofa ni a tunani na wani abu ya shirya maka shiru manal tayi sannan tace nima nayi tunanin da kikayi wlh amma sai daga baya nake ganin kaman sharrin shaidan ne kawai ta gane abunda takeyi bata kyautawa ne gyara to nidai koma meyene bazan hanaku hulda ba amma kisan irin zaman da zakiyi da ita Murmushi manal tayi sannan tace. To shikenam karki damu,
ta tashi ta nufi bedroom wanka tayi sannan ta kwanta.

_The next day_
Aliyu ne ya fito daga dakinshi downstairs ya nufa cikin kitchen yakejin hayaniya da duk kan alamu wannan muryan khadija da manal ne har zai shiga sai kuma ya tsaya yanajin abunda suke fada.  
  ''duk da yanda yake cike da fishin khadija amma saiya tsinci kansa cikin jin ta burgeshi yau yadda take ririta manal kaman ba khadija ba gani yayi duk ta canza murmushi dauke akan fuskanshi ya shiga khadija ne ta fara gaisheshi ya amsa yana murmushi sannan manal ma ta gaisheshi amsawa yayi yana tsokanansu yau kuma girki ake yimana ne da sassafen nan murmushi khadija tayi sannan tace eyii mana ai nabita tun dazu akan taje ta kwanta karta wahalar mana da baby mu amma taki dariya Aliyu yayi sannan yace ai da duk kan alamu wannan baby me rigima ne dan duk ya mada ita rigimemmiya dariya manal tayi sannan tace eh din nidai bazan barta tayi aiki ita kadai ba
Aliyu ne yace to nikam bana fita saina dawo Allah ya kikaye hanya manal tace
Khadija ne ta karbi jakan da yake hannunsa suna tafiya suna hira yadda kikasan basu ba shima kanshi Aliyu khadija tayi matukar bashi mamaki har parking space ta rakashi ya tafi ita kuma ta dawo ciki.
Yau Aliyu yini yayi kas cikin farin ciki da annashuwa abunda ya dade yana Addu'a akan Allah ya hada masa kan matansa yau Allah ya karbi addu'arsa,

*Washe gari*

Zaune Aliyu yake a dakin khadija yanacin abinci
Abunda bai saba gani ba gunta yau har da kanta ta zaunar dashi tana bashi abinci a baki harya koshi kwashe kwanukan tayi gaba daya takai kitchen dawowa tayi kusa dashi ta xauna tana kallon shi cikin kissa irinta mata

''_YaYa aliyu ta kira sunanshi dago kai yayi suka hada ido ta sakar masa murmushi

_dan Allah inaso naje gidan iklima ta fada tana langwame fuska

Da mamaki ya kalleta a iya xamanshi da ita bata taba masa irin abunda ta masa yau ba...



Muje zuwa☺


WhatsApp no
08109990994

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...