🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖
*AMANAR RAYUWA TA*
_{A very short and interesting story}_
🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖🔖
*© Nov 2017*
*Na*
*_Sadieey Smart_*
*_⚜Talented Writers Forum⚜_*
Dedicated this page to
My Beasties
*Faty Axland&Abeedah Tuatuah*
*06~10*
*T*afe suke a motar duk ta k'agu su isa ita kawae ta ganta *Jos* shine burin ta basu suka isa ba sai wajen after *5pm* a *'yan taya* aka saukesu wani farin ciki ne ya mamaye zuciar *Janaan* take ta saki hamdala kasancewar bb *bus* wajen suka tari *Napep* ya kaisu *Terminus* kafin suka sami bus din da zai k'arisa dasu zuwa *D/k'arfe* dai2 _Jordan eye clinic_ suka sauk'a suka tsallaka titin tare da shigewa cikin wani babban gida da bb kamarshi a layin..........
Cike gidan yake da 'yan uwa nan aka rud'e da murna sbd kowa a family d'in yana kaunar *Janaan* wacce itama tana matuk'ar kaunar 'yan uwanta sedai ko yaya ka ganta cikin sa'anninta ta fita daban,ba wai sbd tafi kowa kyau ba a'a ita dae tamkar *Zara* take cikin taurari komai nata ya banbanta da na kowa tana da wata iriyar nutsuwa bata son hayaniya amman pha idan ka ta'bota bata da hkr ko kad'an bata barin ta kwana take take maida martani.........
Wanka sukayi suka yi sallar la'asar kafin aka kawo musu abinci su *Umma* suka ci amman firr *Janaan* tak'i ci daman ita bb abinda ta tsana kamar shinkafa da aka dameta taci sai ta mik'e ta d'auki _handbag_ d'inta ta nufi 'bangaren *Alhaji Babba* kakan su kenan zaune ta tarar dashi zaune bisa kujera falon yana kallon talabijin a hnkli cikin sand'a ta shiga ta rufe mai idanu ta baya tak'i yin magana.....
Murmushi yy ya dafe hanunta yace
"Amarya ta sai ynx kike tafe bayan mahaifin ki tun safe ya sanar dani zaki zo nayi wanka na shirya gashi har k'amshin nawa ya tafi kar pha kice ina tsami".......
Daria tayi "ni wlhy *Alhaji* ya zanyi maka basaja kuma ka gane ni,gaskia da sake.... Kuma ni na fasa angon dakai tunda bakaje ka d'aukoni ba".....
Zagayowa tayi ta zauna kusa da k'afafunshi tana murmushi dafa kanta yayi yana saka mata albarka sai murmushi suke suna lbr don duk cikin jikokin shi yafi k'aunar ta.....
Sallama akayi wasu samari ne suka shigo sunkai su goma da ka gansu kaga 'yan uwa kowa sai karad'i yake ita kuwa wayarta ta ciro ta fara danne2 sbd *Janaan* is addicted to phone bata iya mintoci bata dannan waya ba haka rayuwarta yake.......
Matasan sai mgn suke da tsohon ita dai tun bayan da ta gaedasu bata k'ara cewa komi ba *Alhaji Babba* ya bud'e baki kenan da niyyar tmbaya sai yaji wani k'amshi a k'ofar d'akin ya murmusa sannan yace
"Bismillah maraba da likita bokan turae"
A hankali yayi sallama ya shigo yana had'e rai a hnkali ya zaune gefen kafar tsohon ya gaedashi da murmushi a fuskarshi ya amsa sannan ya tmby shi
"Takwara ya akai ne waye ya tabo min kai?"
Kwashewa samarin nan sukayi da daria suka had'a baki wajen fad'in "Allah Alhaj yayi new catch ne shine kuma bai san ya zaiyi ya sanar da ita ba mu kuma munki mu taimake sa shine yy fushi yakai kansa"
*Janaan* dake dannan waya ta d'ago suka had'a idanu ya zaro ido ya rufe baki kamar dai yadda yare keyi alamun sunji tsoro ita kuwa ta banka mai harara ta mike ta bude fridge ta dauko _Maltina_ ta fara sha .......
Daria ake ta mishi shidae yayi tsuru2 a hnkali ya matso inda take ta juya mishi baya ya kuwa saita dai2 kunnen ta ya kwad'a ihu a figice ta mike ya fice a guje yana daria ta bi bayanshi tana
"Allah ni sai na rama kawae ka tsaya"
Ana ta kallonsu daman kowa ya saba da tsiyarsu ita da *Raheem* a familyn ga wani mugun kaman da sukeyi wanda ko su *Sadeeq* da suke ciki d'aya batai kama dasu ba da ka ganta tamkar tare suka fito duniya dashi......
Suna cikin zagaye gidan ta gaji dai2 wasu kujeru da centre rug a tsakiyar su ta zube a kan kafet d'in wanda nan ne wajen hutawar *Alhj Babba*
Murmushi suka sakar wa juna ya nuna ta itama ta nuna shi suka hada hannu tare da tafawa salon gwanin burgewa.....
Lbr ya tsuge tsakaninsu yake sanar da ita wata 'yar *Uncle Hussain* ya gani mai suna *Jidderh* ita yake so....
Ta murmusa _"Wow I can't wai to see my Oda half's choice_ don nasan zata kasance like no oda"
Suna ta dariarsu *Alhj* suka fito da sauran samarin suka karaso wajen da suke zaune
"Wato daman wayo kamin ka sace min amarya ta ko takwara?"
Yayi daria "ni kaga ma tafia ta zanyi wajen baby nah wannan ai kalar ku ce"
*Ya Sabeer* d'an *Uncle Musa* yace "koma dai miye tare muka sanku don har tunani muke mu had'aku aure don wlhy in ba haka ba duk wad'anda kuka aura in masu kishi ne sedai su mutu don bb mai iya raba ku"
Harara ta galla masa "ni *Allah* ya tsareni me zanyi da wannan surutaccen,sakalin ga shegen zucia in kaishi ina?"
*Ya Hasheem* yace "Hmmm koma dai miye ai halinku d'aya ne wlhy babu ko banbanci sai kuje can kuyi tayi"
*Ya Hilaal* da tun farko bai tanka ba yace "mtsww yo wad'annan in aka had'asu aure ai sedai in da *Ammi* zasu zauna in ba haka ba wlhy sedai musa camera a gdan in muna son nishad'i muke kallon Comedy muna daria".....
Kowa sanda ya dara ta mike "ai kun ganni ne kuke min haka nayi tafia ta"...
Ta fara tafia *Raheem* ya mik'e yana kwad'a mata kira "Oda half tsaya in raka ki man"
Ta mai banza da gudu yabi bayanta ya kama hanunta suka tafi *Alhaji* yace "Allah ya kyauta halin ka takwara".
Suka cigaba da tad'insu
Su *Janaan* 'bangaren *Hajia Mama* suka nufa wacce ta haifi Baban ta,da *Uncle Ahmad* mahaifin *Raheem* a falon suka taras da gungun 'yan mata sai tad'i sukeyi suna shewa tamkar zasu fasa wajen
Direct d'akin baccinta suka nufa hanunsu sark'afe da juna basu ko kula mutan falon ba har ta saka k'afar ta taji wata cikin 'yan matan tace "Allah ya kyauta masu girman kai mutum ba d'an kowa ba"
Wata gefe itama tace "barsu mu zasu gwadawa bariki ko ni da mahaifiya ta take k'anwar senator ban d'agun kai sai wasu jikokin fulanin daji"
Suka d'au daria Hhhhhhhh......
_She can't bear it anymore_ hakan ya sanya ta janye hanunta daga nashi ta koma da baya cikin takunta na isa da tak'ama ta isa garesu...............
*_Janerh💞_*
Comments
Post a Comment