💘 💘 _*'YAR UWATA*_ 💘 💘
_An awesome heartbroken lovetriangle story_ 💔
By ayshalove😘
💦💦💦 *talented writers forum* 💦💦💦
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆
💅🏻 *Dedicated to deejerh lurv* 💅🏻
pg 75
"Ummi! Ummi! Ko juyowa batayi bah..
Seda dausiyya ta dan kara sauri ta riko ta ta baya ta juyo da ita "ummi ya xaki tashi ko mgn baki min ba? Cikin karfin halin zuciya ya ummi tace "xan shiga toilet ne" muryar ta na rawa idanun ta sun cicciko. Tausayin ta ya kama dausiyya itama nan da nan taji idanun ta sun cicciko da kwallah.
Ya ummi juyawa tayi taci gaba da tafiya dausiyya ta kuma riqo hannayen ta "haba ummi ni xaki yiwa karyar zuwa toilet? Abokin kuka fa shi ake fadawa mutuwa! Ummi meysa kike so ki illata kanki ne?
Kukan da take ta riqewa ne ya kwace mata tana fadin "dausiy ya xanyi? Ya xanyi? King baya sona kuma *yar uwata* yakeso uwa daya uba daya balle in kwace shi. Tana gama fadi haka wasu xafafan hawaye suka gangaro mata dausiy ta rungumeta taja ta suka koma bakin pool ta zaunar da ita ya ummi kanta akan kafadar dausiyya tana ta sharbar kukanta seda tayi me isarta.
Itama dausiyya hawayen ne suke zubo mata.
"Ummi ya kamata kiyi wani abu akai fa" "banida abunyi there's no way dausiy babu wata hanya" dausiy gyara xama tayi ta yadda suna fuskantar juna ita da ya ummi.
"Ummi kinada zabi guda biyu a wanan abun! It's either ki hakura ki fitar dashi a ranki ki manta dashi ko kuma kisan yadda xaki king ya xama mallakin ki"
ckn qarfin hali ta goge hawayen da bai daina zuba ba ta dafa dausy
"Dausiy duk ciki babu wanda xe yiwu" ta fada hawaye na cigaba da kwaranya
"Ta yaya xan manta dashi bayan kullum se naji lbrn shi gun kanwata tana kara jaddada min irin kulawar shi da kyawawan halayenshi ta yaya xe fita a raina? its impossible for me...."
"Toh kinga kuwa yaxama dole yaxama mallakin ki tunda baxaki iya cire shi daga ranki bah"
dausy ta katseta
Kara miqewa ya ummi tayi tana kuka tana girgiza kanta
"dausiy baxe yiwu bah naga ya miki its impossible" tana fada ta wuce daki da gudu.
Dausiyya kuwa tsayawa tayi cike da tausayawa "gsky ban taba ganin mutum irin ummi bah she is trying to sacrifice her love I know ko suhailat bata sonshi kmr yadda yaummi tke sonshi mtssw that susu is a selfish girl"
Bangaren su suhaila kuwa tana kashe wayar ta matsa kusa dashi tana fadin me kake yi ne haka king? "ina kokarin designing wasu kaya ne, take a look"
ya nuna mata tace "tooh wanan na maza ne ai! Yauwa meysa baka yin abubuwan mata ne?"
"Eh ai mun fara yin abayas da gowns kinsan kayan matan ne se a hankali akwai dan wahala" Dariya tayi tace nidai ina sha'awar in dan gwada kawo in tayaka, bani inga ko xan iya. Dariya yayi ya miqa mata i-pad din hanun shi sbd da ita yake yawancin zanen products dinshi ba laptop bah.
Haka ya dan nuna mata yadda xatayi cike da shauqin son ta gwada ta karba tana tayi
Shi kuwa kallon ta kawai yake fuskar ta babu ko powder kuma ba karamin kyau tai mishi bah...
Shi kadai yasan me yake tunani akan ta, ta sunkuyar da kanta iya karfinta ta dage ita fa designing jallabiya take... jin yayi shiru yasa ta dago fuskar ta taga yana kallonta murmushi tayi tace "kai ashe dai da wahala amma kalli kaga ai nayi kokari ko ya kalla ya fara dariya
"Wai banyi kokari bane ko me kake min dariya kalli fa kaga wacce ka fara fa na karasa"
"Kinyi kokari susu amma kawo Kiga mu karasa" ya karba yana nuna mata tana ta kalla.
"Toh wacce colour kikeso asa?" A saka red nd black, kai a'a saka blue no wait saka purple kawai murmushi yayi yace "susu kenan" Har ya saka purple tace kaii tayi kyau kuwa amma saka white nd black mugani dariya yayi "susu sarkin ruwan ido" ya saka white nd black sanan tace "woww perfect ita xa a bari tayi kyau sosai"
Time din lecture na yayi fa dama ba wani interval bane me yawa "toh muje na rakaki"
Suka tashi suna ta hira ya raka ta har kusa da class "toh king xan shiga lectures karfa ka kula kowa" ta fada harda kada mishi yatsa alamun gargadi
Dariya yayi toh my queen, take care... ta shiga class.
Comments
Post a Comment