✈✈✈JIRGIN SO ✈✈
🎯5🎯
💦TALENTED WRITTERS FORUM 💦
©NA RUKAYYAT CE
Da safe bayan na tashi ne da safe gun 8:00 da yake na riga da nayi Sallah dinki dinki dinki asuba.
Ina tashi na shiga toilet na dawo gaban mirror nashafa mai da lip gls ko da ba wani kwalliya nayi ba na yi kyau ni kaina nasan haka. Dan ni mai kyau ce ba wai yaban kai ba.
Na shirya cikin atampa blue mai flower din baki dinkin riga da skirt na yafa dan karamin dankwali sbda ban cika daura dan kwaliba.
Bayan na gama shirya wane na fita dan zuwa gaida ko wa a gidan mu wanda Ya kasance dole ne.
Daga nan side din baba naje.
Ina kwana baba
Lfy lau daughter har kin tashi
Ehh baba na tashi
Toh Alhamdulillah.
Anjima kizo ina son magana dake
Toh nace masa sannan na tashi na tafi side umma (uwargida) shiga nayi na hango ta kan dinning Table ita kadai zuwa nayi na duka nace mata.
Ina wuni umma
Lfy lau Alhamdulillah jiya ance kin fita
Eh umma naje gidan su zainab ne.
Toh da kyau haka akeso kucigaba da zumunci kinji ko
Toh umma tashi nayi na tafi side din anty cike da faduwar gaba dan nasan yarda zata mun in na gaida ta.
Ciki na shiga ban ganta ba har zan juwa naji tace
lfy mikikeso mai idan mujiya?
Babu komi anty ina kwana ?
Da ban kwana ba kya ganni? Tashi nayi chike da takai cin anty kamar ba babba ba kishi har da yar cikin ka Allah kyauta nace a zuciyata.
Na fito a hanya na hadu da yaya alamin zan koma side din Mama dan gaida ta
Ina kwana yaya alamin
Lfy lau yau zaki zo muje shoppin kije kifada ma yen uwan ki.
Toh nace sannan naje na gaida Mama sannan na ci abinci sannan na zauna dan inyi kallo
Gurin karfe goma na tashi na je na chanxa kaya sannan naje side din mu na fada ma su yaya khadija sakon yaya alamin
Cewa sukayi toh
Sannan muka tashi suma duk suka shirya muka je muka kira yaya alamin shiga bus din gidan mukayi dan Ya ishe mu.
Muka nufi shoprite kowa Ya zaba abubuwan dayakeso (wannan yan daya daga cikin abin da ake mana duk month ana kaimu shoppin dan mu zaba abin da muke so)
Bayan mun gaba zaba ne dan ni handbag kawai na dau ka guda 5 sannan muka wuce side din siyan kayan abin ci ma siya akayi sannan muka koma gida
Da Isa gidan naje nayi Sallah din azahar naji phone dina na ringin duba wa nayi naga zainab ce dauka nayi nace
Zee ta handsome
Baki manta dashi ba kenan inji zee
Hmm so Ya garin
Lfy lau wlh kefa
Nima haka mun fa hada party din dawo wan yaya saeed dan haka zan kawo miki invitition anjima ko gobe
Toh Allah kaimu ki gaida umma
Toh zataji ki gaida Mama
Alryt bye sai anjima
Kashe wayan nayi sannan na aje a gefe na tare da fadin ni babu wani party din da zani attoh.
washe gari ma haka ta kasance na bi ko ina na gaida su sai dai yau ban ban cin da aka samu shine yen uwan maman mu sun zo tare da diyar sister ta wato Murja (Murja mate dita ce sannan kuma duk wani abu nawa da ita nike shawara ko da kuwa ace zainab ce best friend dita amma Murja ta kasance kawa ta kuma cousin dita)
Ina zaune a daki gurin karfe goma na safe na ga murja ta shigo dakin.
Ahh su murja saukan yaushe.
Yanzu muka zo ni da Mama. (mamanta take mgana).
Kwana zaku yi kenan
Wlh kuwa na ma zo miki hutu ne Amma Mama gobe zata tafi sai nan da sati biyu ni zan tafi.
Gyara zama nayi nace to shine zaki man irin wannan zuwan na bazata
Kiyi hkr esha surprise na ke son yi miki
Toh naji.
Toh yen zu Ya lbr? Murja ce ta tmbyi aisha.
Hmm murja babu wani lbr sai party din yayan zee wanda za'a hada mai sbd Ya gama karatun sa.
Tsalle tayi tace dan Allah dama kuwa na rabu da zuwa party so wen ne?
Ni ban ma Sani ba amma dai next weekne
Toh Allah kaimu
Ameen ni da ban ma yi niyan zuwa ba amma ganin ki Ya sa zanje tunda na san ki da san party.
Wlh kuwa duk na kosa mu chashe 💃💃
Allah Ya shirya ki Murja wlh ki rage san rawa
Bbu abin da zan rage ki bar ni inyi lokaci na ne yanzu ehen....
©NA RUKAYYAT CE 🖌
Comments
Post a Comment