Skip to main content

ZAFIN KISHI BY HUSNA_MB

[9/29, 9:10 PM] Ma Asaa4😘: *29/8/2017*

     *8:15pm*

  *"'ZAFIN KISHI'"*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*46*

_Mom, no one can ever_ _take ur place in my heart_
_I love u forever nd ever._ _No matter where i go or_ _whom i meet, You will_ _always be the number_ _One to me_...

    _Momcy Nah, Ur_ _happiness is my cup of_ _tea I'Ill do anything for u_ _May Allah Protect nd_ _guide her_.
    *momcy Nah wannan shafin sadaukarwa ne a gareki Allah ya kareki a duk inda kike* _Ameen_

Ba su Suka dawo gida ba sai 5:30pm.

   ******

Washe gari Aliyu ya dawo, manal tayi farinciki da matukar  murna da Allah ya dawo mata da habibin ta lafiya
Abinci kala kala ta dafa masa na tarbarsa shi kanshi sanda ya rasa ma wanne xaici.
  Manal tayi matukar yiwa Aliyu kyau duk da bawani makeup tayi ba Atamfa tasa tasha daurinta ji yake tamkar ya hafiyeta dan kwana 2 da akayi basa tare kwata kwata baya gane kansa,
   ''Aliyu ya share kusan 1hour saidai baiya fitowar khadija ba abun yayi matukar bashi mamaki ace yayi tafiya amma ko sannu da dawowa bazata masa ba
Bayan ya gama cin abinci anan ne yake tsokanan faty ya taji gidan nasun babu dadi tace dan kwata kwata batyi enjoying zama a gidanshi ba gida kaman wani kurku ga anguwa shiru babu hayaniyan mutane dariya yayi yace to ai haka yafi kinfiso kitajin hayaniya kaman kasuwa murmushi tayi sannan tace wlh yaya bakasan yanda naketa Allah, Allah ka dawo bane gabaki daya na kosa naje naga mamie nah kwana2 nayi missing dinta bari kagama na tashi naje na hada kayana yanxun nan zan tafi manal ne tace babu inda zakije saimunyi _2weeks_ Taaap di tace _two weeks_ a wannan gidan nakun manal ne tace to ai saiki tafi mugani shidqi Aliyu baice komai ba kawai dariyarsu yakeyi

Tashi yayi yace barinje na duba khadija
    "Saika dawo manal tace tare da kashe masa ido

dakin khadija ya nufa Tv ya samu a kunne saiyi yakeyi shi kadanshi babu kowa a falon Handle din kofan dqkin ya murda sai yaji alaman magana shiga yayi kwance ya sameta kan gado tana waya daga kai tayi suka hada ido bari zan kiraki tacewa wadda suke wayan rejecting tayi tana kallonsa
    Sannu da dawowa tace masa Sannu ya Amsq a Cikin takaici, ka dawo lafiya ta kara da cewa
  Ohh dama kin damu na dawo lafiya ne haba khadija tunda na tafi baki taba daukan waya kin kirani kiji ko lafiyana ba nd still nace miki xan dawo bakizo kinmin sannu da dawowa ba shiru tayi batace masa komai ba, magana fa nake miki
  Amsawa tayi da Meye kakeso nace maka toh
  "'Allah ya kyauta yace ya wuce ya barta a gurin...
Aroud 8:30pm faty ne ta matsawa Aliyu akan ya maida ita gida ce mata ta shirya yace mata dama shima yanason yaje ya gaidasu mamie Manal ne tace zata bisa amma fir yako daukanta wai bayanson tana yawan fita ta jirashi yaje ya dawo kawai.

gidansu mamie suka nufah Sunsha tadi sosai da mamie tana tambayansa ina khadija da manal suna gida yace faty ne tace wlh mamie manal tayi tayi yaya yabarta tazo ta gaisheku amma yaki wai bayason yawo dariya mamie tayi sannan tace to ai da gaskiyarshi yaushe ma tazota gwaliyo Aliyu yayiwa faty yamutsa fuska tayi ta tashi tabar wajen wai ita a dole taji haushi...

Bai dawo gida bai sai karfe 10 dan sunsha tadi dasu mamie dakinshi ya nufah toilet ya fada wanka yayi sannan ya dauki kayan bacci ya saka wadrop dinshi ya bude yana neman keys din safe dinshi amma abunda ya bashi mamaki shine yaga kaman an canzawa keys din wajen ajiya dan ba,anan ya ajiye ba dazai tafi yayi mamaki sosai dan yasan manal bazata taba keys dinnan ba kuma bai isa yace khadija bane saboda ba ita ya bari a dakin ba

Keys din ya dauko safe din ya bude domin ya ajiye sauran kudin daya dawo dasu saidai abunda ya bashi mamaki sai yaga kudin kaman an taba shiru yayi baice komai ba jim kadan dq dukkan alamu tunani yakeyi kudin dazai saka ya dauka ya ajiye ya rufe ya maida keys din inda ya dauko
   ''dakin manal ne nufa saidai bai sameta a falo ba daki ya nufa gaban mirrow ya hangeta tana zaune tana shafa mai murmushi yayi yana takawa a hankali harya isa inda take.

Muje zuwa........😉

08109990994
[9/29, 9:10 PM] Ma Asaa4😘: *5/8/2017*
   
   *8:30pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*

*48*

_sorry fans of zafin kishi am very sorry for d late of posting. Wlh abubuwa ne sukamin yawa kuma ga bikin syster na ah gabana, please am sorry bear with me, Love You all._

dakin khadija ya nufa direct sanda ya isa bakin kofa harya taba handle din kofan zai murda sai kuma wata zuciyar tacemai mai zai kaika dakinta ai ita yakamata tabika tunda tasan sharadin da kayi kwanaki wata zuciyar kuma tace mai ya shiga inyaso yaga meya hanata zuwa shiru yayi after 2mints kawai saiya murda handle din kofan a hankali kanshi ya saka baiganta a falo ba karewa dakin kallo yashiga yi tv ne keta faman aiki shi kadai har bakin tv ya isa ya kashe tare da jan wani tsaki
   kofan dakin ya tura zaune ya hangota kan gata tana dannaw waya d dukkan alamu chart takeyi shiru yayi yana tallonta baice mata komai ba dago kai tayi suka hada kai sai kuma ta kauda kanta kiran sunanta yayi
   ''Khadija!!! Khadija har sau 2 still bata amsa ba a ransa yace nikam meye yarinyar nan takeji dashi ne har ya juya zai tafi kuma sai yayi tunani shine babba koma meyene shiya kamata yayi hakuri a matsayinsa na wanda yake sama da ita still kara kiran sunanta yayi amsawa tayi kaman bazata amsa bah

"Meya hanaki zuwa dakina kuma bayan kinsan yau kwananki ne kamata yayi ace tun 8:30 kin gama duk abunda kikeyi inma wani abun kikeyi sai kuma naga ma chart dinki kikeyi ko kin manta ne yau Toun dinki ne shiru tayi tana kallonsa sannan tace
  Oh ai ni nama manta wlh shys wani zafi yaji a ransa but saiya matse bai nuna mata komai ba yayi kyau yace mata tare dayi mata saida safe Amsawa tayi tana masa kallo ½ jan kofan yayi da karfo tare da cewa tafi nono fari can miki dadin gida biyu kenam maganin gobara dama banda me farantamin ne xai damen

dakinshi yayi direct shiga yayi da mamaki sai baiga manal ba a tunaninshi ko toilet ta shiga sai baiga alamn akwai mutum a bandaki ba kayan jikinsa ya rage toilet ya fada ya sakarwa kansa shower da towel ya fito daure a jikinsa da daya kuma yana goge kansa Wadrop ya bude kayan bacci ya dauka ya saka towel din ya dauka ya shanya cikin bandaki bakin mirrow ya nufah turare ya dauka ya fesa harxai kwanta sai yaji kuma ba bacci yakeji ba ga kuma zaman kadaici tsaki yaja sannan ya nufi bakin kofa dakin manal yaje ya murda sai yaji a rufe komawa yayi ya dauko wayansa yahau dialing number dinta harya xama misscalls batayi responding ba kara dialing yayi jaraf saita dauka a ranta tana mamaki har yanxu bai kwanta ba to yama akayi ya kirata ina khadija kenam maganashi ne ya katse mata tunanin da takeyi

Hello_ yace
hello habibi lafiya kuwa ka kiran by now lafiya yace maza kizo ki budemin kofa to tace tare da katse wayan...
Budewa tazo tayi samun waje tayi ta zauna tana jiran shigowansa after3mints sai gashi ya shigo kusa da ita yaje ya zauna.cike da tashin hankali tahau tambaynsa ko lafiya

menene habibi ya kawoka at this tym ina khadija duk ta jera masa tambayan a lokaci daya

Rungumanta yayi ba tare da ya amsa mata tambayanta ko daya a ciki bah batayi kokarin katseshi ba sunyi kusan 5mints a haka

Cikin sanyi jiki tace ina Khadija?

Tana dakinta yace
murmushi tayi tace to meya faru bata da lafiya ne lfynta Qlau yace ta bude baki xatayi magana ya dakatar da ita tare da cewa let's go ya nuna mata hanyan fita waje kallon jikinta tayi taga bazata iya fita har waje da wannan yar figigiyar rigar baccin jikin natan bah sai tace to habibi ina zamuje bai amsa mata ba ya riko hanunta tare da tasar da ita...

Muje zuwa.....😉

*Whatsapp no*
08109990994
[9/29, 9:11 PM] Ma Asaa4😘: *7/9/2017*

    *5:30pm*

*ZAFIN KISHI*

*WRITED BY*
*husnah mb*

*EDITED BY*
*TEEMAH JALO*
*49.*

hannunta a cikin nasa har suka isa dakinsa a falo ta zauna tana jiran mexaice kallonshi tayi kaman xatayi magana sai kuma tayi shiru kaman baxatayi magana ba kawai saita daure ta tambayeshi ina khadija
 
  "Nan ya kwashe labari yadda sukayi da ita ya bata shiru tayi tana kallonsa after5minuts saita mike ina xakije yake tambayanta dakina tace
  dakinki kuma my Queen ke dinma bazaki tayani kwana bane shiru tayi kaman baxata bashi amsa ba sai tace habibi ai bai kamata na kwana a dakinkq ban tunda ba kwana na bane yanzu intazo fah kaga ai bamu kyauta ba ai tunda bacema tayi bazata zo ba saika jira zuwa anjima kagani... nunfashi yaja sqnnan yace wify khadijq ba zuwq zatayi ba hasalima shirin kwanciya naga tayi abunta bata damu dani b meyasa ke bazaki debemin kewa ba ta kuntatamin kema so kike ki gujeni duk da kalamnsa sun ratsata but bazata iya kwana a dakinsq ba sabida tasan intayi haka bata kyauta ba in ita akayiwa baxataji dadi ba to meyasa ita zatayiwa wata harta juya xata tafi sai kuma ta juyo hannunsa ta riko tare da cewa habibi bazan iya kwana a dakinka ba saboda ba kwana na bane amma in bakason kwana kai kadai nw kazo muje mu kwana a dakina kalman data fadane yasashi murmushi kofar dakin nasqn ya jawo tana tafe yana binta a bay kaman rakumi da Akala...
''Hira sukayi sosai cikin soyayya da jin dadi sune basu kyaunta ba har sai karfe 12 na dare ita dai manal tun bata iya biye masa rashin bacci da wuri harta saba dqn shi Aliyu dama al'adansq ne rashin bacci da wuri dan wani lokacin saiya kai karfe 2 na dare idonsa biyu.

Washe gari da safe khadija ne zaune a falon downstairs tana kallon mbc bollywood taci kwalliya da duk kan Alamu ma anguwa zataje Aliyu ne ya sauko zaune ya tarar da ita koda ya ganta a zaune kauda kansa yayi dan har yanxu yanajin haushin abunda ta masa jiya da daddare duk da kuwa Queen dinsa ta faranta masa rai
gaishesa tayi amsawa yayi ba tare da ya kalleta ba dama inaso na fita anguwa ne tun dazu nake jiranka baka sauko ba a dawo lafiya yace bai tsaya tambayanta ma ina xataje ba ko ita tayi matukar mamaki ace duk halin Aliyu na hana fita yau tana tambayansa ya barta baima tsaya tambayanta ina zataje ba itako dadin hakan taji hakan xai bata daman zuwa duk inda takeso
  Tashi tayi ta nufi dakinta harta dauki gele sai ta mayar ta dauk hijab hadda nikab tayi tafiyarta.

Kitchen Aliyu ya nufa breakfast ya musu a try ya hada ya haura upstairs a falo ya ajiye ya sauka ya dauko flask din daki ya shiga kwance ya hangota saman gado murmushi tayi mai bakin gadon yaxo ya xauna yana tambayanta yaya jikin dai da sauki tace tana kokarin tashi jikinta ya taba yaji har yanxu da sauran zazzafin dan jikin akwai zafi hannunta ya rike tare da cewa tashi kiyi breakfast sainaje na kira doctr yazo ya dubaki koh yamutsa fuska tayi a,a nikam habibi banasha magani ba plz habibi ka bari zuwa gobe inban ware ba saika kirashi wlh banason Allura kuma nasan inyazo saiyamin allura ta karisa maganan tana hawaye jawota yayi yana jijjigata dan har cikin ransa yakeji kukan Queen din nashi bayason abunda xai tabata kona seconds.
    "Saida yace mata ya fasa kiran doctr sannan tayi shiru abunda ya fadane yasa tayi murmushi dagata yayi cak har falo yazo ya ajiyeta a hankali ya hau bata abinci kaman wata yarinya saida ta daina karba sannan yaci shima
   Rashin dadin da manal batajine yasa yaki fita office Abdul ya kira ya sanar dashi akan baxai samu fitowa ba dan haka yayi duk wani abunda ya dace
Ba khadijq ta dawo gida ba sai 5:30 na yamma ji gidan da tayi shiru ne yasa tayi tunani ko manal dinma bata nan ne fitowa tayi xata sauka sukaci karo da Aliyu a bakin stairs harkin dawo ne ya tambayeta na dawo tace sannu to yayi wucewarsa abunsa dakinta ta kowa wani kullin abu ta dauko a cikin jakanta ta nufi dakin Aliyu...


*Muje zuwa.....☺*

*Whatsapp no*
08109990994

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...