0/30,1:50PM]***
11/7/2017.
10:30PM
'''ZAFIN KISHI''
@WRITED BY@*
@husnah mb@*
@EDITED BY@*
@TEEMAH JALO@*
01.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
Cikin wani yanayi ta tsinci kanta aciki jin abunda ya fada shiru tayi jim kadan sannan tace masa yanxu inkamin haka kamin Adalci kenam, wani nunfashi yaja sannan yace ni banga abun rashin Adalci acikin wannan maganan bah Khadija. Da nace zan kara aure bafa ce miki nayi xamu rabu dake ba dahar xaki daga hankalinki ki kwantar da hankalinki karki dauki abunda nayi niyyan yi a matsayin rashin yin adalci kuma bawai dan bana sonki bane yasa zan kara aure xanyi hakanne kawai dan ubangiji Allah ne ya umurcemu da muyi hakan dago kai tayi ta dubi inda yake tanamai kallon kare dangi To kasani ka hura wutar da baxaka taba iya kashewa ba 'a gidannan, baice mata kala ba yabi bayanta ya wuce.
bai tsaya ko inaba sai inda ake Ajiye motoci matse key din dake hannunsa yayi sannan ya shige motan fincikan motan yayi dakaga yadda yaja mota kasan ransa a bace yake bai tsaya ko inaba sai office xama yayi kan chair dake cikin office din sannan ya dauko wayan dake Aljihunsa number bala ya dannawa kira kaxo ka sameni a office bai jira amsan daxai bashi ba kawai ya katse cikn minti 2 zuwa 3 sai yaji an murda kofah dagowa yayi don ganin wayene bala ne ya shigo jiki a sanyaye yace gani Alhj yauwa dama inaso na sanar dakai ne duk wanda yaxo nemana kace masa yau baxan samu ganin mutane ba su dawo gobe domin banajin dadi To Alhj! nan ya wuce abunsa
ZAFIN KISHI
02
Haka ya yini a office cikin rashin jin dadin abunda khadija ta masa khadija wata irin matane Shikam dai gsky baiyi dacen mata ta gari ba kwata kwata bata ragawa kowa dagashi har yan uwansa babu wanda ta bari ni kaina nasan khadija batada kirki ko kadan amma na rasa meyasa na kasa daukan mataki akan abunda takemin dagani har iyayena amma insha Allahu karshe abun yaxo tunda Allah ya hadani da mace ta gari jin ringim din da wayansa yakeyi ne ya tsundumo dashi cikin duniyar tunanin daya shiga zarota yayi a Aljihu dan ganin waye ke kiransa MANAL ya gani nan ya sake wata yar karamar murmushi wadda take kara fito da kyaunsa dagawa yayi sannan ya manna wayan a kunnensa, shiru yayi domin jin abunda zatace wata sanyayyen murya yaji ance Assalamu Alaiku ya amsa da Wa'alaiku mussalam lfy kuwah bby yinin yau banga kiranka ba shiru yayi kadan sannan yace wlh Manal banajin dadine Subhanallah Ayya wlh bansani ba ai dama tunda naga baka nemeni ba nasan dole akwai wani abu To yanxu dai ya jikin da sauki to Allah ya kara sauki Ameen nan ta katse wayar daga kai yayi don kallon agogo karfe 5:30 ya gani nan ya tashi ya dauki jakarsa jiki babu kwari ya nufi parking space bude gaban motan yayi ya jefah yar jakar dake hannunsa xagayawa yayi ta baya ya shige gaban motan yadda ya fincoki motan daka gani kasan ba lafiya bah bai tsaya ko inaba sai gida inda ya packing motan a packing spac dake gefen gidan ya nufi side dinsa motsin da khadija ta jiyone yasa ta fito ganin Aliyu ne yasa ta danna uban tsaki ta shige ciki bayanta yabi baice mata kala ba ya shige dakinsa ajiye jakar dake hannunsa yayi ya fada bandaki alwala ya daura ya fito darduman dake gefen gadonsa ya dauko shimfidawa yayi, domin yin sallan magrib.
Comments
Post a Comment