💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
_bear wit me fans bana editing just ignore d typing error pls love youu.._
*3&4*
Afreen❤ ta tashi cike da farin cki domin saura 'yan kwanaki Kadan ne ranar visiting nasu dole ta nemi waya ta buga musu a gida ta lissafa musu abunda zasu kawo mata.
" Afree queenie watzup kinga shegiya Deborah ta kira house koh? tashi muje dallah" tsaki afreen ta Ja sannan tace " bar shegiya taji dashi ai duk wata tsiyar yazo karshe don next term don ubanta dole a bamu mulki shegiya mayya, ynxu Ki duba irin ranar da ake zabgawa amma su babu ruwansu 'yan iska" kwanciya Afreen ta koma tayi bisa bonk tayi lamo tamkar Mara lafiya, Rashida bunk mate nata kuma classmate nata ta tsaya a tsorace tana cewa " haba Queenie kinsan halin Deborah fah bata da imani" " jeki kawai tunda kinga zaki iya don ni wllhi aikin jakancin ya isheni daga yau na daina " fita Rashida tayi cike da fargaba indA ta tarar da sauran juniors kowacce tayi kneeling sai hada gumi suke . wata bakar arniya ta fito mai siffan namiji da alama itace Deborah nan ta fara bayani cikin harshen turanci tana cewa gidan nasu wato pink house yayi datti su tashi su share ynxu -ynxu kuma ta basu minti 10 su share kowane lungu da sako sannan su wanke bayi sai su dawo su cigaba da punishment har Xuwa karfe 3 . daliban sun tashi cike da fargaba ga kuma azabar rana sai zaginta suke cikin zuci...hmmm wannan kenan rayuwar boarding skul
💞💞💞
p👐rof Shuraim ne kwance a falonsa na shakatawa idanunsa a rufe amma gaba daya ba bacci yake bah illa tunanin fuskar wannan kyakkyawar yarinya da ya gani a FGGC yola tabbas akwai indA yasan fuskar Amma Sam ya kasa tunawa kuma ya kasa daina ganin fuskar tata "I think am in love wit u, pls ina zan sake ganin Ki my pretty" carab! Kalaman suka fada kunnen Salina wacce take shigowa Dum..zuciyarta ya buga wato daman soyayya ce ta maida prof haka? Ya daina cin abincin kirki ya daina walwala da sauran abubuwa dama akan mace ne? Wannan wacece? A ina take? Hawaye ne ke fitowa a idanunta domin tasan Shuraim mutum ne da ba ruwansa da shiga harkar mutane musanman mata toh ina ya ga wannan yarinyar?
Sheshekar kukan da take ne ya jawo hankalin Shuraim ya tashi xaune " Salina? Meya faru I min meyasa kike kuka?"
Zama tayi dirshan ta fara rutsa kuka " haba prof Kasan ina tsananin sonka bana fatan ganinka da kowacce mace a duniya amma wane laifi na maka har kake neman jefani halaka" " halaka? How but Salina me na miki" cikin muryar kuka tace " gashi nayi sake har ka fada son wata " murmushi yayi sannan yace " ina kika ji wannan tatsuniyar kuma?" Wani kallo ta jefa masa tace " daman nasan zaka fake ai , toh wllhi bazan lamince ba bazan taba zama da kishiya bah sabida babu abinda ka rasa a gidan nan" tana kawo nan a zancen ta fice . murmushi Shuraim yayi yana kallonta kamar kidahuma haka ya kwanta ya cigaba da tunaninsa.
Hon Ahmad jauro yana kwance a gidansa gaba daya muryar wannan yarinyar yake son ji donhaka dole yau yaje makarantar tasu , wanka yayi ya shirya tare da deban kudade masu yawa ya kira bodyguards nasa ya shaida musu indA ya nufa daga nan suka dau hanyar Xuwa fggc dake can bayan gari.
A hanya suka tsaya wajen Atiku shopping mall suka mata shopping mai shegen yawa da tsada sannan suka wuce. Afreen na class ta samu kira daga ofishin principal cike da tsoro ta amsa kiran ga mamakinta principal bata nan sai dai wani mutum xaune ga kuma securities zagaye da ofishin ta risina har kasa ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska " Aysha Aliyu xauna man" ya nuna mata kujera ta xauna . fuskarsa d'auke da murmushi yace " sunana Hon Ahmed jauro am d Hon commissioner of education n d younger brother to d Governor of dis state, gaskiya ban taba yin aure bah kuma tunda na fara ganin ki naji kin kwanta min a rai so wat do u tink" rufe ido tayi da tafin hannu cike da kunya a can kasar zuciyarta kuwa murna take sabida Afreen akwai son hutu😂😂 dariya Hon yayi yace " am waiting Aysha " gyar zama tayi tana kallon kasa tace
" toh naji kuma nagode Amma de ban fara soyayya sai na gama makaranta don iyaye na bazasu amince bah donhaka kayi hakuri sai na gama insha Allah " murmushin jin dadi yayi yace " nasan da hakan ba komai zan iya jira fatana dai kisoni kar wani ya rigani shiyasa na kasa hakuri nazo da kaina" nan ya ajiye mata sabbin kudade 500 notes yace " ga wannan 50k ne kiyi managed sai kinzo Hutu koh" godiya tayi sannan ta dauka daga nan sukayi sallama ya cikata da kayan provision dakyar ta karba tana wani nokewa sannan ta koma class.
'Yan ajinsu sai mmkin yawan ledojin suke ga kuma yar jaka me kyaun gaske Afreen de tace musu babanta ne yazo kowacce ta Ja bakinta tayi shiru , bayan sun taso ne ta labartawa Rashida komai ihu tayi suka tafa tace " shegiya Queenie abin nema ya samu sai ke 'yar gidan antyluv" " ai bari kawai yarinya Allah kaimu visiting antyluv tazo ta koyamin wasu dabarun Jan hankali walle sai mun tsiyaye rabonmu ba kwamishina bah haa..." dariya suka sake yi daga nan suka debi kayansu Xuwa hostel kudaden kuma ta kai ajiyansu wajen matron.
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na_*Sunhera*_
💦 *Talented writers forum*💦
*T.W.F*
*dedicated to Reefat yahya*
💦talented writers had'in kanmu shine abin alfaharinmu🤝
*5&6*
Afreen ta shirya fita night prep akan hanya ta hadu da 'yan uwanta Arwa , Afiya da zee suna tafe suna hira " Afree Queenie ya akayi" " hmm bari kawai 'yan mata ya shirin visiting ne kunyi magana da mutanen gida ne?"
Arwa tace " dole suzo fah ..mutum 7 wasa ne? Wllhi gara suzo cos am broke " dariya sauran sikayi Afreen tace mata " ba dole kiyi broke bah shegiya kina playing mom n dota stuff adole ke big girl koh" " kyaleta Queenie iskanci take ji , dat reminds me naji ss1 girls sai toasting naki suke kina rejecting koh" afiya ce tayi wannan furucin . dariya Afreen tayi tace " bani da lokacinsu " haka suka cigaba da hira daga karshe kowacce ta wuce ajinta dayake Afreen da zee class daya suke don haka suka wuce tare.
💞💞💞
*Modibbo's estate* aka rubuta da manyan harufa wato estate d'in familyn modibbo Tukur kenan Wanda Duk fadin jahar Adamawa ansan da zaman familyn , family ne mai girman gaske Wanda babu bare a cikin estate d'in Duk dangin juna ne kowane gida ka shiga yan uwane. Modibbo Tukur hamshakin mai kudine tun zamanin baya yana da shanaye babu adadi sannan yana noma Duk da cewa ynxu ya tsufa Amma yana nan da karfinsa, matansa 4 hajiya Aishatu tana da yara 9 sai hajiya Hafsatu tana da 6 sai hajiya Asabe mai 'ya'ya 7 sannan hajiya Rakiya itace amarya yaranta 5.
'Ya'yan hajiya Aishatu wacce ake kiran adda sune Mohammed ..Abubakar..Usman..Umar..Aliyu..Zainab.. Amina.. Ahmad.. Sai auta Salisu , hajiya Hafsatu wato ( Nenne ) tana da safiya ..Fauziya..Sani.. Hauwa..Adamu..sai Fatima.
Hajiya Asabe wacce ake kira da ( Diddi ) tana da Abdulrahman..Abdulmalik..Suleiman..Sa'adatu.. Hadiza..Asma'u..sai Harira. Amarya Rakiya ( dada ) tana da yara 5 sune Maryam..Hajara..Sadika..Auwal da Hasiya. Wannan sune 'ya'yan modibbo Tukur wato idan an hada su 27 kenan. Modibbo Tukur su 8 ne agun iyayensu maza4 mata4 kuma kowanne daga cikinsu yana da yara sama da ishirin donhaka ne suka gina estate har ya zama tamkar unguwa guda sun hada ya'y'an nasu auren zumunci kuma suna zaman lafiya babu bare a cikin dangin nasu.
Al'adan dangin ne idan yara sun girma sai a hadasu aure ko suna so ko basu so ba sai anyi shawara da Kowa bah, Zainab kacal ta fita daban a cikin dangin wato ya'r Adda uwargidan m Tukur babu yanda ba ayi ba kafin ayi auren nata mahaifinta yayi fushi sosai lokacin da akayi auren indA ta auri wani major Wanda a halin ynxu yayi retire. Zainab itace uwa agun Afreen indA ta haifi yara 5 tare da retired major Aliyu kojoli yaranta maza 3 mata 2 suna nan zama a cikin Jimeta a unguwar dougirei wannan shine takaitaccen tarihin familyn .
Modibbo Tukur farin tsoho Dan kimanin shekaru 82 a duniya yana xaune bisa darduma a cikin falonsa mai girman gaske ya'yansa na risine agabansa yace " yaune ranar ziyarar yaran nan wa zaije ?" Suleiman yace " dama mun gama magana Auwal tare da sani zasu Je da su Fatima " "toh..toh shikenan a gaishesu anjima ka shiga dakina ka duba kud'i a kai musu"
" Baba ai angama shirya komai " " ehh ..nasani amma Duk da haka de" "toh shikenan Allah kara girma" "Ameen" sauran suka amsa daga nan suka watse, a falon Adda suka hadu tana tare dasu Diddi da sauran kishiyoyin nata Fatima tace " wllhi modibbo ya shagwaba yaran nan , wai a ce dole kowane visiting day sai anje musu .mufa lokacin da muke makaranta bahaka aka mana bah" Nenne tace " toh sai kije Ki fada masa ai, mutum da jikokinsa keda kika tsaya boko ai sai kiyi tayi" dariya suke mata taja bakinta tayi shiru. Auwal ne yace " ai babu y'ar gata irin Afreen, Anty Zainab xata Je ga Anty Aysha ga kuma nan gidan "
" uhmm..Afreen da Aysha sai Allah " Diddi ce tayi wannan furucin. Dada tace " gaskiya Aysha na kaunar Afreen tamkar ta karbe mata numfashi " tsaki Suleiman ya Ja tare da cewa " wace kauna? tana de batata da shagwaba da nuna mata son kud'i" gaba daya suka fashe da dariya haka suka cigaba da hirarsu har Xuwa wani Dan lokaci.
💞 *FGGC YOLA*💞
Yau asabar ranar visiting na daliban makarantar FGGC kowacce fuskarta d'auke da murmushi don zasuga 'yan uwa da abokai anyi ado sai raba ido ake, can naga wasu 'yan mata su 7 xaune sunyi kama sosai daga nesa na gano Afreen tayi kyau ba karya hira suke da dariya Afreen ta tashi tsaye tace " ni zan wuce mosque idan sunzo Ku kirani" Afiya tace " sannu ajebo kice de kin gaji da zama zakije Ki kwanta Ki jira Anty Aysha koh" murmushi tayi sannan zee tace " yau samarin bazasu zo bane dota?" Dariya suke Afreen tace " kai momma ina jin kunyar Ki fah " haka suka cigaba da raha Daga nan Afreen ta wuce Xuwa masallaci.
Comments
Post a Comment