Skip to main content

Zumunci na sunhera

💦 *Talented writers forum*  💦


*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*

_domin samun littattafan mu shiga....

_To get access to talented novels check_

http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/

💞💞 *Zumunci*💞💞

Na *_Sunhera_*

_dedicated to_ *Reefat yahya*

*41&42*

_u'v captured mah mind mah hrt mah soul no wonder u r d1 am waiting for....evreytym I luk in2 ur eyes I c mah....🤦🏼‍♀ gosh! Love tinz_

    *Golden rules of happiness enunciated my prophet ( s.a.w )*
_1.. Expect less_
_2.. Give more_
_3.. Always smile_
_4....loading....._

'Yan kai amarya sun sauka lafiya suna jiran karasowar amarya amma shiru kake ji nan suka wuce cikin gida aka bar anty maijidda da anty maryam dasu anty Mariya . wasa2* sun share 30 mins suna jira daga karshe anty maryam ta xare waya ta fara neman layin Shuraim, cikin saa kuwa ya d'aga lokacin yana tare da abokansa suna zolayarsa yau ze angwance . cikin girmama wa ya gaisheta cike da fad'a tace " rike gaisuwar ni ka turo mana yarinya mu mikata gidan zamu wuce " cikin rashin fahimta yace " wat? Anty baaje d'aukar ta ba har ynxu? " " kaga banson shashanci ba tare kuka tafi bah?" Shuraim ya fara rudewa " bangane ba anty meke faruwa ?" "Kana nufin ba kai ka shiga mota d'aya da ita bah?" Cikin kidimewa yace " kuna ina ynxu gani nan Xuwa" nan suka kashe wayar anty maryam tace " tohfah! Yau ake yinta, Shuraim baya tare da ita" tsaki anty Mariya ta Ja tare da cewa
" wannan yarinyar akwai taurin kan tsiya, hala guduwa ta sake yi" anty maijidda tace " aa wllhi wannan karon ba guduwa bane gaskiya akwai wata a kasa Allah yasa de a ganota"

Cikin kankanin lokaci Shuraim ya karasa ya fara tambaya nan Anty maijidda ta bayyana yanda sukayi lokacin da aka zo daukar amarya, tashin hankali zufa ne ya fara keto masa yace " wllhi ni banje gidan ba ..innalillah Afreen ina kika shiga? Wa zai aikata min haka?" gaba daya sun razana da jin cewa Shuraim baisan da zaman motar da Afreen ta shiga bah duk hankalinsu ya tashi aka fara neman layinta amma kash! Wayar na hannun Ruky.
    Cikin kankanin lokaci magana ta baza ko'ina nan aka fara nemanta wasa2 sun raba dare suna neman Afreen amma shiru kake ji babu ita babu labarin ta hankalin family gaba daya ya tashi musamman modibbo, Abba, Mami da Shuraim su nasu tashin hankalin daban ne Mami in banda kuka babu abunda take yi modibbo tuni yayi alwala ya fara gabatar da sallar istihara , a takaice de wannan daren ya Zane musu wani iri kowa ka gani jiki yayi sanyi haka aka watse taron biki tare da bazamar neman amarya indA aka yanke shawarar sanar da 'yan sanda idan gari ya waye. Wannan daren Shuraim bai runtsa bah haka ma iyayen Afreen tabbas sun shiga tashin hankali Mara misaltuwa .. _readers wat do u tink?🤔🤔 shin wayayi kidnapping d'in Afreen?? Zayyad ko Saleem ko kuma Saleena ? Ko wani ne daban??_ uhm☹☹ muje Xuwa dai.

*******

Al-amarin Afreen kuwa kwanan xaune tayi don ko baccin ya gagareta gaba daya a tsorace take har garin Allah ya waye gashi babu damar fita tanason tayi sallah amma babu hali haka ta cigaba da Xama har gari ya waye sosai nan wani murjejen kato ya bude ya shigo yana waya yana cewa " ehh oga tana nan ..toh shikenan ba komai , ehh..zamu kula ..toh shikenan " ya kashe wayar ya juya yana kallonta cikin rawar murya tace " don Allah ka barni nayi salla " wani mugun tsawa ya daka mata yace " ke! Ni abokin wasan Ki ne ko an gaya miki wasa mukeyi a nan?" " kay...kayi hakuri don Allah wllhi salla zan..." Bata karasa ba ya d'auke ta da mari cikin muryar kuka tace " Allah ya isa azzalumi kafuri Wanda baisan Allah bah, ka guji haduwar ka da ubangiji " murtuke fuska yayi yace " ni zaki gayawa magana ? wato kin fini tsoron Allah koh? Yau xan koya miki yanda ake girmama mutane shegiya Mara tarbiya kawai" gadan-gadan yayo kanta tayi saurin takure a bango tare da kulle ido tana nanata innalillah a cikin zuciya , wayarsa ce tayi kara yayi saurin d'aga wa cike da girmamwa yace " ehh oga..ehh..ehh wai salla zatayi , OK toh shikenan ynxu xaa kawo .OK..OK nagode oga "
     Tsaki ya Ja tare da watsa mata harara yace " shegiya kin ci sa'a da wllhi yau sai kin dandani gudarki jaka kawai" " Nide ba jaka bace " tayi saurin bashi amsa yayi galala yana kallonta yace " wato ke me taurin kai koh..zanyi maganin Ki duk da cewa oga ya hana a tab'a lafiyarki amma wllhi sai na koya miki hankali, tashi kizo kiyi alwala na baki minti uku " yana gama magana ya bude kofa harara ta galla masa sannan tayi saurin bin bayansa .

Bayan tayi salla tana xaune ta rafka uban tagumi tana tunanin gida Allah sarki ko a wane hali suke oho! hawaye na bin kuncinta tayi nisa cikin tunani taji alamr bud'e kofa , wata nyamura ce ta ajiye mata plate da pure water d'aya ta juya ta fice ba tare da ta kalli bangaren Afreen ba. tabi plate d'in da ido tabbas yunwa take ji dole ta ci abincin nan ta bud'e plantain ne soyayye da dan kwai a sama nan ta hau ci hannu baka hannu kwarya cikin kankanin lokaci ta cinye tas! gaskiya bata k'oshi bah haka ta kora da ruwa me dan sanyi , hamdala tayi ta koma gefe ta rakube ta cigaba da tunanin da take.

💞💞💞💞

Wasa2* Afreen ta share 2 weeks iyayenta sunyi Neman har sun gaji 'yan sanda ma suna cikin nasu binciken amma babu nasara har ynxu, modibbo yayi istihara a cikin mafarki Allah ya nuna masa Wanda ya aikata abin shiru yayi babu Wanda ya bawa labarin don gudun tashin hankula.
      Afreen ta rame kamar ba ita bah ga rashin wanka tunda tazo ko sau d'aya basu barta tayi wanka ba. Kamar kullum yau ma tana nan rakube salati takeyi idanunta na fidda kwalla, mai kawo mata abinci ne ta kawo ta ajiye har yau bata taba yiwa Afreen magana bah kuma ita Afreen ta sha yi mata magana amma bata amsawa ko kurma ce oho! Cikin muryar kuka Afreen tace " baiwar Allah pls Ki taimaka Ki fiddani nan wajen, kiji tausayi na don Allah. Ynxu idan y'ar Ki cikin wannan halin shin haka zaki kyaleta bayan kina da damar taimaka mata" cak! Matar ta tsaya ta juya cikin sanda ta dawo kusa da Afreen da alama de maganar ya shigeta , alamar bud'e kofa suka ji yasa matar tayi saurin karasa bakin kofar da niyyar fita.

Wannan murjeejn katon ne ya shigo duba lafiyar Afreen daga nan yabi ta da kallon raini matar ta fice haka nan shima ya tafi bayan ya kulle kofar.

******* *Modibbo Estate*
Rikici sosai ake inda malam Bukar kanin modibbo kuma kakan Salina yace a raba estate d'in a bashi rabonsa  har abada babu shi babu zuriar modibbo Tukur, ba modibbo kadai ba kowa yayi mamakin wannan lamarin abin bai tsaya a nan ba sai da yasa ya'yansa da suke auren ya'yan modibbo Tukur kaf sun rubutawa matansu takardun saki😳 kowacce ta koma gidan ubanta. Yaran modibbo mata 5 aka saka sai kuma jikoki 15 ciki kuwa harda amaren da basufi watanni kad'an a gidajen su bah.
     Hankalin family ya tashi ran uncle Mohammed yayi baki kirin donhaka ya Tara meeting a falon modibbo yace lallai sai dai su ma su dau mataki, modibbo yayi murmushi mai ciwo yace " haba d'ana idan anyi haka ai abin ya Xama jahilci, yaku ya'ya Nah na horeku da hakuri domin hakuri yana d'aya daga cikin halayen manzo ( s.a.w ) donhaka kuyi hakuri nasan anci muku zarafi amma Allah ne ya kaddara insha Allah babu komai, mahakurci shine mawadaci donhaka kuyi hakuri kuma ban yafe muku da yanke zumunta bah ko bayan raina ne Ku cigaba da *Zumunci* da Bukar tamkar mahaifi yake agareku"

uncle Mohammed yace
" amma Allah ya kara maka girma Baka ga irin abubuwan da yake mana bah? Shifa yace baya son alaka damu shi ya yanke Zumuncin dake tsakanin mu da zuriarsa shin dole sai munyi zumunci dashi ne zamu shiga aljanna? Haba gaskiya ni bazan iya bah"
murmushi modibbo yayi yace " d'ana Kaine babba amma Sam Baka da hakuri, shin ka manta cewa manzon Allah ( s.a.w) yayi mana hani da abubuwa dayawa? Ko Kasan yanke Zumunci yana d'aya daga ciki? Bayan yanke zumunci akwai girman kai, karya, daukar hoto , annamimanci, yawan tsinuwa, Hassada, yin aiki domin mutane, kafirta musulmi, Alfasha, Nuna kiyayya ga masoyin Allah, Rauni a salla, Barin ambaton Allah, Kauracewa musulmi babu dalili,  Zaluntar makwabci, da dai sauransu. donhaka kuyi hakuri Ku mika lamuranku ga Allah sannan Ku nisanci wadannan abubuwan da na lissafa Allah muku albarka " "Ameen suka amsa cikin sanyin murya tabbas Addinin islama bata bar komai bah Allah ka bamu kyakkyawan karshe Ameen.

*Ja muje*

Comments

Popular posts from this blog

ANCUCI HIJJABI BY FAYEEEEEEX M USMAN

ANCUCI🤦🏼‍♀HIJJABI _*TRUE*    *LIFE*   *STORY*_ ✏ _Writen by_ *fayeeeeex m usman* 💦💦 *Talented writers forum*  💦💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga.... _To get access to talented novels check_ http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/ 💚💙❤✨             💃🏼💃🏼💃🏼✨ 🍭🍡🥂✨ 💙💚❤ *zuri'a d'aya soyayyama guda d'ay~a karda kutam bay~a rabu da* _jun~abana mun~e wannanba❤y'an uwan jun~a soyayy_ *a had'uwar jin~i soyayyar zuciya ba ayimata magani💙wannan pg d'in nakune ku kad'ai my* _lovely family bani da kamarku har abada kuneni inbaku ni bakomai bace soyayyata agareku d'orarriyace tarihina daku_ *dauwamammeni bazaku ta6a i...

NADAMAR SOYAYYA

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM note dat wannan labarin ya faru ne da gaske ba kirkirarsa nayi ba , Allah yasa muyi aiki da darusan dake ciki musamman 'yan matan yanxu kuma wannan shine labari na farko da na rubuta based on true life story Allah ya bani ikon gamawa lafiya ameen* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Baiwar Allah*: _Salam sister Reefat ya kike ya fama da jama'a_ *Reefat* _lafiya Alhamdllh sis ya kike_ *Baiwar Allah* _lafiya sai godiya, don Allah tarihin rayuwata nake son na baki Ki rubuta_ *Reefat* _OK ba damuwa Allah yasa mu dace_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai amma don Allah Ki boye sunana da sunan garin mu , ina son labarina ya zamto darasi ga sauran al'umma_ *Reefat* _ba komai insha Allah, Allah ya shige mana gaba_ *Baiwar Allah* _ameen nagode sosai da karamci_ *Kada...

Nadamar soyayya

💞 *Nadamar Soyayya*💞 ( a true life story) 🖊by *_Reefat Yahya_*💞 💦 *Talented writers forum*  💦 *had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu* _domin samun littattafan mu shiga...👇🏻👇🏻👇🏻 _To get access to talented novels check_👇🏻👇🏻👇🏻 http://talentedwrittersnovel.blogspot.com _dedicated to *Zaleefah S Nalado*_my kwalliyas😘😘 *5&6* Da gudu khairat ta shiga dakin har sai da tasa ummi ta tsorata tayi tunanin ko wani abun ne ya faru.. "Khairat lafiya kike gudu haka?" Ummi tace cike da fargaba. "Bakomai wallahi ummi sai alkhairi" khairat ta ba ummi amsa cikin fara'a. "Toh alhamdulillahi wlh har hankalina ya tashi na dauka wani abun ne ya faru kike irin wannan gudun haka kuma wai kha...